9

28 2 0
                                    

HAWA DA GANGARA

*Daga Kundin ✍️📚✍️*
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman

*page 9*

"Yasir ga Ummina"

Nayi zumbur na mike nace

"Mama dama kece babar Yusrah?"

"Me kake nufi da haka?"

"Mama ba ki ganeni ba ko?"

"Ban ganeka ba!"

"Nine fa Yasir yayan Yasira wadanda suka zauna a hannunki a lokacin da muna yara....... "

Sai ta taho da gudu ta rikeni ta salati da sallallami.

"Yasir! Yasir!! Yasir!!! dama kuna raye, ina ita kuma Yasirar take?"

"Tana gida mama"

Kawai sai ta fashe da kuka tana neman afuwa.

"Yasir ka yafe min, nasan na cutar daku kai da 'yar'uwarka Yasira na wahalarku na, na azabtar daku, don Allah ku yafe min wallahi......"

"Don Allah mama kiyi shiru in dai mune mun yafe miki"

Yusrah tana kallonmu zuciyarta tana mata sake sake, fuskarta dauke da alamun tambaya.

"Yasir dama kasan mamana?"

Kawai sai hawaye suka zubo min na kalli Bushrah nayi shiru. Sai Bushrah ta kwashe labarin duk abinda ya faru ta fada mata tana gama fada mata sai ta sake fashewa da kuka.

Nace "Mama don Allah kiyi hakuri kiyi shiru abinda ya faru ya riga ya faru, sai dai a kiyaye gaba"

Yusrah tace "Yanzu mama da irin wannan rayuwa kika yi da marayun Allah? a gaskiya kinyi kuskure ba ki kyauta ba! banji dadin wannan al'amari ba!"

Nace "Don Allah ku bar wannan maganar bata da amfanin komai, a yi wata maganar mana."

Nan dai muka yi shiru na dan wani lokaci sai na daga kaina sama sai na sake yin karo da hotunan Sabir da Mugir.

"Wannan Mugir ne da Abba ko?"

" Eh sune "

"Basa nan dukkansu ko?"

"Kai! Kai!! Kai!!! ai sun dade da rasuwa sakamakon hadarin mota da ya ritsa dasu a hanyarsu ta dawowa gida daga wurin aikinsu!"

"Allahu akbar! Allah yaji kansu! Allah ya gafarta musu!"

"Amin summa Amin"

Muka yi shiru na dan wani lokaci sannan sai muka cigaba da hirarrakin mu, har lokacin cin abinci yayi muka je muka ci abinci muka yi sallah, sannan muka dawo muka cigaba da hira. Ban baro gidan nan ba sai bayan karfe goma sha daya da rabi, da zan wuce mama tace don Allah in daure in kawo mata Yasira ta ganta.

Bayan na fito daga cikin gidan sai na duba wayata don naga karfe nawa, kawai sai na missed calls har guda ashirin da hudu,don a silent take, dana duba sai naga Yasira 12 missed calls, Mas'ud ma haka.

A raina nace 'To yau zan sha tuhuma da tambaya'

Ai kuwa ina zuwa gida na tarar da Yasira da Mas'ud sunyi jigum jigum, ai kuwa suna ganina sai dukkansu suka tashi suka yo kaina suna cewa ina na shiga me ya faru da wayata suka kikkira ni amma ban dauka ba, sai kawai na sanar musu cewa ina wani meeting ne mai muhimmanci shi yasa kuma ga wayata tana silent, haka dai suka bar maganar amma a zuciyarsu ba lallai bane sun yarda.

HAWA DA GANGARAWhere stories live. Discover now