10

27 2 0
                                    

              HAWA DA GANGARA

*Daga Kundin ✍️📚✍️*
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman

                        

                          *page 10*

         Yasir ya sunkuyar da kai kasa yana hawaye ya ka sa ce mata komai.

         Yusrah tana masa wani irin kallo tace "Wannan ya tabbatar min da cewa Ummi ta rasu, shikenan na zama marainiya gaba daya ba uwa ba uba! amma ai ina da kai ko?" ta fada tana kallon Yasir idonta fal da hawaye.

         Yasir ya gyada mata kai idonsa na zubar da hawaye ya kasa furta uffan, gaba daya tausayinta yake yana hango yadda rayuwarta zata kasance, a ransa yace 'Insha Allahu ba zan kiyi rayuwar maraici irin wadda muka yi ba'

       Yasira ta zauna a kusa da ita a daya barin ta dafata, Yusrah ta kalli Yasira sannan ta Yasir, tace "Wannan ita ce Yasira?"

       Yasir ya gyada mata kai a karo na biyu ba tare da yace komai ba.

       Sai Yusrah ta rungume Yasira, tana cewa "Yanzu ke kadai ce 'yar'uwata ta jini domin kuwa tare aka fara shayar damu kafin kaddara ta rabamu"

        Mas'ud da Dr. Ra'is da Dr. Karim da wadannan nurses din kawai kallonsu suke zuciya cike da tausayawa.

          Yusrah ta saki Yasira ta kalli Yasir, tace "Yaya ka kaini naga Ummina nayi mata sallama kafin a kaita a binne"

          Nan fa aka fara kallon kallo a tsakanin mutanen da suke cikin dakin.

         Yusrah ta kula da duk yadda mutanen dake dakin suka yi don haka sai ta sake kallon Yasir, tace "Yaya an kuma samun akasi kenan ko?"

        Yasir yana kallonta cikin yanayin tausayawa yace "Idan baza ki manta ba bayan mun kawo umma asibiti an turamu mu siyo magani a lokacin da zamu tsallaka titi mota ta kadeki, tun daga wancan lokacin ba ki san inda kanki yake ba sai yau da kika farka, daga ranar zuwa yau kimanin wata shida kenan, umma kuma lokacin da aka shigar dake emergency ita kuma a lokacin aka fito da ita ta rigamu gidan gaskiya"

        Sai Yusrah ta sake fashewa da kuka, Yasira ta rungumeta tana rarrashinta.

         Yasir yace "Sai dai idan kina bukatar ziyartar kabarinta sai in kaiki makabarta da zarar an sallamemu"

         Nan Dr. Ra'is ya bukaci dukkansu su fita don ya duba lafiyarta ya gani ko da wata matsalar, an aunata sosai anyi mata gwaje gwaje duk sakamako ya nuna ba wata matsala, nan take ya rubuta musu sallama aka sallamesu suka tafi basu je gida ba sai da suka fara zuwa makabartar da aka binne Bushrah suka yi mata addu'a ita da sauran mamatan musulmai na duk fadin duniya, sannan suka wuce gida. Yusrah tayi matukar farin ciki da yadda Yasir da Yasira suke yi mata, suna matukar kaunarta itama tana kaunarsu babu wanda zai ba uwa daya uba daya suke ba sai wanda ya sani, sun rakata gidansu ta da suke haya ta debo kayan ta wanda take so, wanda bata so kuma ta hada da na Bushrah ta rabawa mabukata, sannan suka dawo suka yi zamansu cikin aminci da yarda.

       A yanzu Yasira da Yusrah tare suke tafiya makaranta, don Yasir ya maidasu makaranta daya suna karatu tare tunda dama duk likitanci suke karanta, rayuwa tana musu dadi duk abinda suke so shi Yasir yake musu yana nuna musu matukar kauna.

       Wata rana da hantsi Yasir da Yasira da Yusrah suna zaune a falo suna hira cikin annushuwa da kwanciyar hankali, kawai sai suka ji ana kwankwasa kofa, Yasir yana daga zaune yayi izini da a shigo, ana turo kofar wa zasu gani? Shukrah ce da Rayyan kana ganinsu kasan suna cikin tashin hankali da damuwa sun rame sunyi baki, suna shiga Shukrah ta fada jikin Yasira tana kuka mai tsuma zuciyar mai jinsa, shima Rayyan kukan yake, Yasir da kyar ya rarrashesu suka yi shiru sannan ya sasu suka yi wanka suka ci abinci suka huta sannan suka zauna gaba dayansu Yasir, Yasira, Yusrah, Shukrah da Rayyan.

HAWA DA GANGARAWhere stories live. Discover now