5

27 3 0
                                    

               HAWA DA GANGARA

*Daga Kundin ✍️📚✍️*
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman

                        

                          *page 5*

RAYUWARMU A GIDAN ABDUSSATTAR

   Abbanmu Abdussattar yayi kudi sosai ya zama hamshakin attajiri na kwantance a gari, an sauya mana gida babba na alfarma kuma katafare, don dakina daban ni kadai kuma komai na bukata an samin a ciki har da laptop computer da bangaren karatu daban da desk da tarin littattafan karatu a kantoci, ga wardrobe cike kayayyaki, da bangaren takalma, da bangaren kallo cike da plasma tv, a gaban mirror kuwa mayuka ne kala kala irinsu cream da lotion, man gyaran gashi dana tafin kafa, ga dakin ya painting sa ma na daban ne daki yasha recess da wallbracket ga Chandelier a tsakiya daga sama, ga ac gefe kuma ga wani hadadden toilet mai kyau da tsari ga waterheater da shower da baho dai sauran tarkacen bandaki irinsu mirror da shampoo da  toothpaste da  soaps da sauransu, a takaice da Abba ya maidani handsome guy.

   Bayan gama makarantar secondary school gaba sai Abba ya turani kasar waje na cigaba da karatu a can, da zan tafi ya bani shawara akan abinda zan karanta yace na karanci architecture ko kuma technology.

   Na tsinci kaina a kasar waje cikin turawa da sauran mutanen wasu kasashen mabanbanta, wasu su bige da soyayya, wasu shaye shaye, wasu bin matan banza, wasu yawace yawace, ni sai na yiwa kaina karatun ta nutsu na tsaya nayi karatu tukuru Abba ya hanani zuwa gida hutu kwata kwata sai dai shi inya bushi lokaci ya kanje da kansa ya ziyarceni, don haka ban koma gida ba sai da nayi degree na  masters guda biyu, daya akan technology daya kuma akan architecture.

   Bayan na koma gida iyayenmu sunyi matukar farin ciki da murna zuciyarsu cike da alfahari dani. Na tarar da kannena shida gaba daya sun girma, Zayyad da Dayyab sun zama cikakkun mutane samari 'yan hutu ajeboters, Yasira da Shukrah sun zama cikakkun 'yam mata kyawunsu ya kara bayyana, haka su ma Zayyan da Rayyan sun zama matasa kowanne kana ganinsa kaga botty.

  Naji dadi sosai, sai dai naci karo da abubuwa guda biyu, daya na farin ciki daya na bakin ciki, abun farin ciki dana samu shine arzikin Abba ya ya kara bunkasa don a yanzu ya gina kamfaninsa na kansa mai suna Abdussattar and sons Construction & Technologies company. Abun bakin cikin kuma shine lalacewar Zayyad da Dayyab gaba daya tarbiyyarsu ta baci basu da wani aiki kullum sai yawace yawace basa dawowa gida sai karfe biyu ko ukun dare. Zayyad ya lalace da neman matan banza kamar bunsuru, shi kuma Dayyab ya lalace da shaye shaye kamar dan qabusu.

    A washe garin dawowa ta daga kasar waje Abbanmu Abdussattar yake sanar dani wannan a lokacin da naje sashinsa muna tattaunawa.

   Na kalleshi nace "To Abba kai me kayi a kai? wane mataki ka dauka akai?"

   Yace "Na kirasu nayi musu fada nayi musu nasiha amma duk a banza, basa jin maganata bare ta mahaifiyarsu!"

   Nace "Abinda kayi yayi kadan Abba, me yasa baka daukesu aiki a kamfaninka ba?"

   Yace "To gaba daya ma wane karatu suka yi da har zasu iya samun gurbin aiki a kamfanina!"

   Nace "Duk da haka da ace lokacin da suka gama karatu an daukesu aiki a matsayinsu na 'ya'yan mai kamfanin, a ganina da haka bata faru ba domin duk wadannan abubuwa da suke aikatawa laifuffuka ne irin na marasa aikin yi"
 
    Yace "Idan da haka ne me yasa basu nemi aiki a wani kamfanin ba lokacin da naki daukarsu a kamfanina?"

HAWA DA GANGARAWhere stories live. Discover now