15 END

49 3 0
                                    

              HAWA DA GANGARA

*Daga Kundin ✍️📚✍️
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman

                         *page 15*

      Dama su a al'adar kasarsu miji sadaki kawai zai bayar a daura musu aure da matarsa, sai a kawota daga ita sai kayanta na sawa, sauran duk wani kayan amfanin gida kuma wannan duk hakkin miji ne, kama daga kayan sawa a cikin gida na alatu irin kayan daki, har zuwa kayan aikin cikin gida na yau da kullum duk hakkin miji ne.

     Bayan sun dawo gida daga tafiyarsu Dubai suna zaune tare dasu Zayyan da Rayyan suna dudduba kayan da suka siyo.

       Yasira ta kalli Yusrah da Shukrah, tace "Wai ku amare idan an daura muku aure a rana daya a lokaci daya, wace zata fara tarewa?"

      Yasir ya kalli Yasira da sauri yace "Ni kaina na dade ina so nayi musu wannan tambaya"

      Shukrah tayi farat tace "Yusrah ce zata fara tarewa, in yaso ni bayan mako daya sai nima na tare, kunga ita ta zama uwar gida ni kuma amarya, saboda dama itace budurwar yaya ta farko ita ya fara cewa yana so"

         Yusrah tayi farat itama tace "Kun ga aikin hankali ko? gaskiya nayi matukar dacen abokiyar zama, babu abinda zan wa Allah sai godiya tare da fatan zaman lafiya har karshen rayuwarmu"

       Gaba dayansu su amsa da cewa "Amin summa Amin"

        Yusrah tana kalli Yasira tace "Kema kiyi addu'ar Allah ya baki abokiyar zama kamar tawa......!"

       Yasira ta katseta da hantara tace "Ke dahalla can! wa ya gaya miki ni tare da kishiya zan zauna?"

       Yusrah tace "Ba wai yanzu nake nufi ba, nan gaba idan mijinki zai yi miki ita.......!"

        Yasira ta sake katseta da cewa "Ko nan gaba ma ba yi min zai yi ba! don bana so!"

         Shukrah cikin matukar mamaki tace "Tooo!"

         Yasir yace "Ashe dai masu kin kishiyar suna da yawa!"

     Sai duk su kyakkyawan da dariya.

     A tare suka je wajen gyaran jiki da kitso da kunshi aka yi musu suka fito fes, duk wanda ya kallesu sai ya sake kallonsu, don tsabar kyau da suka yi abin sha'awa abin birgewa. A haka aka shiga hidimar biki ka'in da na'in, bayan gabatar da abubuwan al'adu irinsu wankan turare da karatuttukan Alkur'ani da aka yi a ranar farko, washegari kuma aka gabatar da walima a wani katon Hall inda dukkanin angwaye da amare suka hallara akan floor, aka yi wannan walima aka ci aka sha, sannan MC ya tashi ya fara jawabi.

     MC "Biki bidiri birede, abu namu maganin a kwabemu, dakan daka shikar daka tankaden bakin gado, kuma  tuwona maina. Taro yai taro jama'a sun taru baki sun zo daga ko'ina 'yan'uwa da abokan arziki, ranar da muke ta jira gata tazo, shagalin biki yana tafiya komai daidai kowa ka gani yana cikin farin ciki, ga angwaye nan su da amare guda uku kai kace 'yan uku ne da aka haifesu a tare, yau fa wannan babbar rana a gareku, shigar amare babu mai irinta duk wurin nan, kamshin turarenku ban taba jin irinsa ba, kwalliyar amare ta ruda duk wadanda suke wajen nan, kowa fatansa dama shine, to muyi shagali amma kada mu shagala, fatanmu angwaye da amare ku zauna mutu ka raba takalmin kaza"

     MC ya cigaba da jawabi "A yanzu zamu gabatar muku da shahararriyar mawakiyarmu ta wannan kasa inda zata kara bamu nishadi duk cikin murnar wannan shararren biki na 'yan'uwan juna, yanzu dai bari mu gabatar muku da mawakiya Sabyan"

     Nan jama'ar dake wajen suka kaure da shewa da tafi, nan take Sabyan ta fito ta fara wakokinta masu dadi har angwaye da amarensu suka zo suka yi mata liki, haka aka yi wannan  walima cikin farin ciki da annushuwa kuma aka tashi lafiya kowa ya koma gida.

HAWA DA GANGARAWhere stories live. Discover now