8

31 3 0
                                    

                HAWA DA GANGARA

*Daga Kundin ✍️📚✍️*
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman
 

                         *page 8*

           HADUWATA DA YUSRAH

     Wata rana ina yawo akan babur dina sai hanya hanya ta biyo dani ta wani titi, sai nayi kacibis da wata yarinya budurwa tana jiran mota da gani ma ta gaji da jira har ta fara kosawa, shekarunta ba zasu wuce na Yasira ba, fara ce tas mai siririn hanci, tana da kananan idanu da baki madaidaici, siririya ce doguwa gata Allah ya hore mata gashi har gadon bayanta.

  Ina karasawa kusa da ita nayi magana.

      "Sannu"
      
      "Yauwa sannu"

      "Makaranta za ki ne?"

      "Wallahi makaranta zani gashi na kusa makara kuma har yanzu ban samu mota ba"

       "To hawo na rage miki hanya mana"

       "A'a wallahi na gode"

       "Ah ki hawo hanyar zanyi ne shi yasa kika ji nace miki ki hawo"

     Ta hau muka tafi muna tafiya muna hira nan da nan kuwa na kaita ta sauka.

       "Na gode"

       "Yauwa, am! don Allah yaya sunanki?"

        "Sunana Yusrah"

        "Yusrah kamar karfe nawa kuke tashi daga makaranta?"

        "Misalin karfe biyar wataran har zuwa biyar da rabi"

        "To ki bari zan zo in dauke ki in mayar dake gida don inga gidanku"

        "To shikenan, am! kai baka gaya min sunanka ba"

        "Ni sunana Yasir"

        "To Yasir sai ka zo"

        "Sai an jima"

        "To sai ka dawo"

        Ina ta kallonta har ta shige aji, sannan na tada babur dina nayi gaba. Karfe hudu da rabi a bakin makarantar tayi min ina nan tsaye har biyar ta cika har da karin minti goma sha takwas sannan sai gata tana ganina ta sakar min wani Ingattacciyar murmushi.

      "Afuwa! na tsayar da kai ko?"

      "A'a ni baki tsayar dani ba, ban ma dade zuwa ba"

      Nayi mata izini data hau mu tafi, ta hau muka kama hanya muka tafi, muna tafiya muna hira kai da ka ganmu kace mun yi irin shekara da shekarun nan a tare, na kaita har kofar gida ta sauka.

     "Yasir na gode, Allah ya kara zumunci"

     "Nima na gode da kika yi sauri amincewa dani"

      Tayi murmushi wadannan kyakkyawan hakoran nata suka bayyana haskensu ya bugi kirjina ya ratsa ta cikin zuciyata.

     "Yusrah ni zan tafi"

    "To Yasir sai yaushe kenan?"

    "Gobe ma zan zo in kaiki makaranta in Allah ya yarda"

    "To sai goben kenan?"

    "Eh! sai gobe, ki gaida kowa da kowa na gidanku"

    "To. Kaima ka gaida duk mutanen gidanku"

    "Zasu ji"

      Muka yi sallama na tafi gida, sai da nayi kwana goma ina kai Yusrah makaranta in kuma an tashi na koma na dauko ta, a ranar da nayi kwana goma sai nace mata zanyi tafiya amma sati daya zan kawai zanyi na dawo, ta nuna min rashin jin dadinta amma sai na nuna mata tafiyar tana da muhimmanci a gareni, tayi min addu'ar Allah ya dawo dani lafiya, Allah kuma ya tsare hanya.

HAWA DA GANGARAWhere stories live. Discover now