Chapter 2

20.5K 1.5K 61
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*
@fatymasardauna

*CHAPTER 2*

Agaban wani tankamemen gate yayi parking motarsa, fitowa yayi daga cikin motar ya nufi ƴar ƙaraman ƙofar dake jikin gate ɗin, ahankali yatura ƙofar yashiga, Manu mai gadi naganinsa ya kwaso aguje cike da girmamawa yace.
"Ranka ya daɗe barka da zuwa, Ango, Ango kasha ƙamshi...."

Kallon da yayiwa Manu mai gadine yasa yaja bakinsa yayi shiru, batare daya ƙarasa maganar dayakeyi ba.

Direct wani dogon gini dake tsakiyan compound ɗin gidan yanufa.

Wata ƴar dattijuwar mata ce ke zaune acikin katafaren falon, kayane zube agabanta tare da wasu manyan akwatuna masu kyau da tsada.
Da sallama ɗauke abakinsa yashigo cikin falon, amsa masa sallaman matar tayi fuskarta babu yabo ba fallasa. Baidamu da yanayin yanda yaga fuskarta ba, don yasan dalilin daya sanya tayi kicin kicin da fuska damace batason bashi, kuma amma duk da haka baijin zaiƙi furta abundake cikin ranshi.

"Barka da gida Ummu"
Sooraj yafaɗi haka bayan yayiwa kansa mazauni akan lallausan carpet ɗin da ya mamaye ƙasan falon.

"Yauwa sannu" Ummu tafaɗa tana mai ƙoƙarin tattare kayan dake gabanta. Shirune yashiga tsakaninsu, dama shi haka yake idan yayi magana saiyaja wasu mintuna baisake cewa wani abu ba, bakuma don baida abun cewa ba, a'a haka ya sabarwa kansa. Ummu kuwa afakaice ta ɗan saci kallonsa, yanda taga fuskarsa ya tabbatar mata da cewa akwai magana abakinsa, itakuwa bazata so taji komai daga bakinsa ba. Miƙewa tayi daga zaunen da take, wayarta taɗauka kana ta nufi hanyar da zai sadata da ɗakinta.

Ganin da yayi cewa idan yabari tatafi yarasa damansa ne, yasanyashi gyara zama haɗe da cewa. "Ummu dama inaso...."

"Banason kacemin komai, ya isa haka, munriga da mungaji da halinka SOORAJ, wallahi kaji na rantsema awannan karon kasaki matar da muka aura ma, ranka saiyayi mummunan ɓaci, zakuma kaga fushinmu irin wanda baka taɓa gani ba!" Ummu takatseshi ta hanyar faɗan haka cikin ɓacin rai.

Jajayen idanunsa yaɗago ya watsawa Ummun, itakuwa ko waiwayosa batayiba ta wuce ɗakinta.

Wani irin tsannin baƙinciki ne yasake kawo masa ziyara, babban abun takaicin shine yanda akaƙi basa dama, jiyayi kansa na sarawa kamar zai rabe gida biyu, tashi yayi ya fice daga cikin falon, ko iya kallon gabansa bayayi haka yakoma motarsa, kafa kansa yayi ajikin steering motar, yana fidda numfashi mai zafi, "Wannan wace irin rayuwace yakeyi? sai yaushene zai samu sauƙi daga raɗaɗin da yakeji?" tambayar dayaketa yiwa kansa kenan acikin zuciyarsa. Ya kusan mintuna 10 a wajen, kafun ya iya tada motarsa yabar unguwartasu gaba ɗaya, kaitsaye gidansa ya nufa.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now