Chapter 30

11.9K 1.3K 155
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

           *SOORAJ!!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

             *WATTPAD*
       @fatymasardauna

*Chapter 30*

Haka ta daure ta cuccusa abincin wa cikinta zuciyarta cike da tarin tunani, tana kammalawa tayi sallan magriba, bayan tayi sallan isha ne tabi lafiyan gado, da yake agajiye takejin kanta take bacci ɓarawo ya ɗauketa.

_SOORAJ_

Yana gama sipping black coffee tea ɗinsa, ya aje cup ɗin tare da miƙewa tsaye ya fice daga cikin kitchine ɗin,  direct ɗakinsa ya wuce, toilet yafara shiga yayi wanka sannan ya ɗauro alwala,  wata blue t-shirt ya sanya kana ya wuce masallaci. 
Bashi yadawo gidan ba sai ten pm dai dai,  wanka ya sakeyi sannan yafito ɗaure da towel a weast ɗinshi,       ɗan ƙaramin towel ya ɗauka agaban dressing mirror ya shiga goge kansa,  duk da cewa bai shafa turare ba amma gaba ɗaya ƙamshin sabulun da yayi wanka dashi ya cika ɗakin,   wani body lotion wanda baya kama jiki sosai ya shafa ajikinsa,  turarensa me sanyin ƙamshi  ya ɗauka tare da fesawa,  cumb ya ɗauka ya  taje kwantacciyar sajen dake kan fuskarsa,  ɗan kallon kansa yayi amadubi lokaci guda kuma ya kawar da kansa gefe, pink lips ɗinsa ya ɗan ciza, wani tunanine yazo ransa hakan yasanyashi sakin murmushin daya bayyana zallan Kyawunsa, shi kansa baisan da yayi murmushin ba,  direct gaban drawer ɗinsa ya nufa tare da zaro kayan dazai sa, riga da wando  na black jeans ya sanya ajikinsa wanda sukayi matuƙar yi masa kyau,   White kambas masu kyau yasanya aƙafafunsa, tare da ɗaura hulan white facing cap akansa, sosae da sosae yayi kyau harma baka iya tantance kammaninsa saboda yanda hulan ta ɓoye fuskarsa,  wayoyinsa ya ɗauka tare da ɗaukan car key ɗinsa,  yana fita daga cikin ɗakin ya murzawa ƙofar key tare da tura key din cikin aljihun wandonsa,   koda ya fito ko ina dake cikin gidan ya ɗauki shiru, direct parking space ya nufa,  mota ƙiran kia  yashiga tare dayi mata key,   koda ya iso bakin gate taradda Maigadi yayi yana ta zuba gyangyaɗi,  wani silent horn ya danna, take maigadi yatashi a zabure, cikin daburcewa ya wangale masa gate ɗin,   ba ɓata lokaci Sooraj ya cilla hancin motar sa waje,    kasancewar dare ne hakan yasa babu wani hayaniya sosai akan tituna, tuƙi yake cike da nutsuwa yayinda ya saƙala earpiece akunnensa. 
Duk da sanyin AC'n dake tashi acikin motar hakan bai hanasa sauƙe glass ɗin window ba, wani irin ni'imtaccen sanyine ke ratsa jikinsa wanda har ma yafi na AC daɗi. 
    
TRANSCOP HILTON.

Wangale masa makeken gate ɗin akayi, asukwane ya tura hancin motarsa cikin ƙawataccen compound ɗin hotel ɗin,   ababban parking space ɗin hotel ɗin yayi parking motarsa.  

Ahankali ya zuro da ƙafafunsa waje, cikin takunsa me ɗauke da nutsuwa haka ya nufi cikin hotel ɗin, direct babban ɗakin da zasu gudanar dawani important meeting ya nufa,  gaba ɗaya kowa da kowa sun hallara shi kaɗai kawai ake jira, kasancewar shine jagoran meeting ɗin shiyasa basu fara ba dole saida suka jira yazo,  aƙalla sun ɗauki sama da 1 hour suna tattauna maganganu wanda gaba ɗaya su yasu suke abunsu,  Sooraj kam maganarsa bata wuce "Eh"  ko "A'a"    Ko kaɗan basu wani damuba domin dama acikinsu babu wanda baisan halinsa ba, 11:30 pm daidai suka kammala meeting ɗin, kowa ya kama gabansa,  koda ya baro Transcop Hilton baikoma gidansu ba, direct gidansa ya wuce kasancewar gobe zai koma bakin aikinsa na Bank.

Washegari.

Kamar koda yaushe 7:15 daidai take kammala shirinta na zuwa makaranta, yauma hakance ta kasance domin tuni ta shirya kanta cikin uniform ɗinta,  school bag ɗinta ta ɗauka agurguje tafice daga cikin ɗakin,  bata tarar da kowa acikin falonba gashi har 7:30 takusa sam kuma bataso tamakara,   buɗe ƙofar falon tayi ta fice,  Kamalu driver ta iske tsaye yana jiranta, tana shiga cikin motar yaja suka tafi.
***
Tun 7 daidai yagama shirya kansa cikin wani tsadadden maroon colour suit and white long sleeve shirt, sosai yayi kyau acikin suit ɗin, wani dark maroon toms  ƙiran company'n Italy yasanya aƙafafunsa,  sosai kwalliyan nasa ya sake ƙawata. Agogon rolex ne ɗaure a tsintsiyar hanunsa, gaba ɗaya gashin kansa sai shining yake yana ɗauke ido, saboda sosai yasha gyara,   kamar wanda akawa ɓarin turare ajiki haka yake tashin ƙamshi,  sabuwar   black car ɗinsa mercedes benz yashiga,  direct bank ɗinsu ya nufa,   tun fitowarsa daga cikin mota mutane keta kawo masa gaisuwa, sama sama yake amsasu yana wucewa,   koda yakai office ɗinsa ya samu komai nead, dama kowa yasan bayason ƙazanta shiyasa always ake tsabtace masa office ɗinsa, sosai yatarar da aiki na jiransa saboda haka tunda yaje bai wani huta ba aiki kawai yaketayi a computer.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now