Chapter 28

11.4K 1.1K 89
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ !!!*

*Written By*
phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

*Wattpad*
@fatymasardauna

#romance

*Chapter 28*

Inda yake zaune wani secret wajene me kyau da burgewa, wajen tamkar garden haka yake domin anƙawatasa da korayen furanni masu sanyin ƙamshi.
Zaune yake akan wata haɗaɗɗiyar chair wanda aka ƙawata tsakiyanta da wani haɗaɗɗen table me kyau, drinks ne kala kala ke jere asaman table ɗin, gefe dashi Mas'oud ne ke sipping coconut juice, yayinda Sooraj ke aikin latsa wayarsa, azahirin gaskia idan kaga yanda gaba ɗaya attention dinsa ke kan wayan zakayi tunanin wani abu me amfani yake aiwatarwa, saɓanin haka kuwa kwata kwata hankalinsa ba ga wayar yake ba, idanunsa ne kawai ke kan wayan amma gaba ɗaya tunaninsa yayi nisa izuwa wani ɓangare na daban, duk abun dayake Mas'oud na kula dashi, ɗan aje cup ɗin coconut juice ɗin yayi tare da duban Sooraj...

"Bazaka taɓa daina sakanka adamuwa ba matuƙar bazaka fito ka faɗa mana damuwarka ba, haka kuma bazaka warke daga ciwon dake damun zuciyarka ba matuƙar ba zaka amayar da abun dake cikinta ba, har yaushene zakana ɓoye matsalanka RAJ? taya kake tunanin zaka samu sassauci da kuma nutsuwar zuciya bayan bakanemi hakan ba? shin ni bankai na zama abokin da zaisan matsalarka bane RAJ? tun muna ƙanana muke abota me yasa har yanzu bankai jigon dayakai sanin sirrinka ba?" Duka waƴannan tambayoyin Mas'oud yayiwa Sooraj alokaci ɗaya fuskarsa ɗauke da damuwa.

Ɗan numfasawa Sooraj yayi tare da ɗago kansa, ɗan kallon Mas'oud yayi sannan ya kau da kansa gefe, lips ɗinsa ya ciza tare dayin wani shu'umin murmushi, wanda shikaɗai yasan ma'anarsa, cikin husky voice dinsa yace. "Babu wani wanda zai fahimci matsalata Mas'oud, idan nafaɗa maka matsalata ba lallai ka yarda ba, idan nace maka bansan waneneni ba nasan bazaka taɓa yarda ba, wannan dalilin shiasa banason nayi sharing damuwata da kowa, saboda damuwata damuwata ce ni kaɗai!" cikin wani irin yanayi ya ƙare maganar tare da haɗiyan wani saliva me ɗaci da ya tsaya a maƙoshinsa.

Cike da mamaki haɗi da rashin fahimta Mas'oud yace "Banfahimci inda kalamanka suka dosa ba Sooraj, me hakan yake nufi?"

"Aure ne banaso Mas'oud, sam banason zama da kowace mace, nafison nayi rayuwata ahaka" ɗan tsagaitawa da maganan yayi tare da kallon kansa, daɗan ƙarfi ya cije laɓɓan bakinsa kana yaci gaba da cewa "Bazan taɓayiwa wata mace amfani amatsayin namiji ba, niba kamarka bane bakuma kamar sauran maza bane, inada rauni Mas'oud inada rauni wanda yake barazanar durƙushewar rayuwata, ita ƙaddara tana iya zuwa wa bawa aduk yanda baizata ba, ta ɓangarena haka tawa ƙaddaran take, amma banajin akwai wata wacce zata rayu dani ahaka, banajin zanyi wani farinciki.... " Kasa ƙarasa maganan yayi sakamakon wani irin nauyi dayaji ƙirjinsa yayi, bada kowani lokaci yacika yin magana me tsawoba, hakan yasa yanzu yakejin kansa tamkar zai faɗo ƙasa, yayinda yakejin tamkar ana hura masa wuta acikin ƙirjinsa. Bottle water Mas'oud ya miƙo masa, babu musu ya amsa bai aje bottle water'n ba har saida ya tabbatar da babu wani sauran ruwa acikin goran, wani irin ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe, ɗago idanunsa da suka soma rikiɗewa daga farare zuwa jajaye yayi ya kalli Mas'oud daya kafesa da idanu, wani ɗan murmushi yayi tare da sanya hanu yashafi sajen dake kwance akan fuskarsa.

''Zan tafi, kada ka manta ranan monday muna da meeting" yanakaiwa nan azancensa ya miƙe tsaye kota bakin Mas'oud bai tsaya jiba yayi gaba, binsa Mas'oud yayi da kallo har ya ɓacewa ganinsa, wani irin iska me zafi Mas'oud ya fesar tare da sanya hannuwansa ya dafe kansa, sai ayanzu brain ɗinsa ke ƙoƙarin harhaɗo masa matsalolin Sooraj, batun yauba ya kamata ace yagano menene matsalan, tunanine barkatai suka shigo cikin brain ɗinsa, wasu abubuwa daya tuno da kuma maganganun da sooraj yafaɗa masa yanzu sune suka taimaka wajen kawo masa haske daga duhun daya shiga, wani irin faɗuwa yaji gabansa yayi yayinda bugun numfashinsa ya soma fita da sauri sauri, abayyane ya furta.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!!" kansa ya kifa ajikin table ɗin, take yaji ruwan hawaye naƙoƙarin cika idanunsa, da sauri ya yi ƙoƙarin maidasu, car key dinsa ya ɗauka, haka ya bar wajen jiki babu ƙwari.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now