Chapter 38

12.6K 1.1K 243
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

          *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

             *WATTPAD*
        @fatymasardauna
#romance

             *Chapter 38*

Ɗago kansa yayi daga jikin steering motar tare da sakin wani murmushi mai ɗauke da tarin ma'anoni,  agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya duba, ƙarfe 11 dae dae,  ɗan ƙaramin tsuka yayi tare da tada motar ya cillata kan titi.

Zieyaderh kuwa tana gama koke kokenta baccine ɓarawo ya saceta wanda sai yanzun ta tashi,  ji tayi yanayinta ya sauya tamkar wata marar lafiya,  bathroom tashiga tayo wanka,  tare da dawowa ta zauna akan gado, tv ta ƙurawa ido amma azahirin gaskiya hankali da tunaninta ba ga tv'n yake ba, tunaninsa ya matsanta mata, lallai tana da buƙatar me fayayyace mata halin da take ciki,  Shukra, itace wacce ta fara faɗo mata arai, tabbas tasan idan tasamu Shukra to zata fayyace mata komai, to amma idan Shukra ta bata amsar da zai hautsuna tunaninta fa? ajiyar zuciya ta sauke tare da soma ƙoƙarin shanye hawayen dake cikin idanunta, sam yau haka taji zaman gidan ya isheta, komai jinsa take ba daɗi.

Wuse zone 4

SOORAJ, zaune yake akan wata kujera dake kusa da haɗaɗɗen dinning table ɗin dake cikin falon, cup ɗin coffee ne agefensa yayinda yake signing ɗin wasu papers dake gabansa,   Mas'oud ne ke zaune akan kujeran dake facing nasa, wayar dake hannunsa ya ajiye tare da kai dubansa ga Sooraj,  cikin yanayi na ɗan damuwa yaƙira sunansa.

Batare daya tsaida aikin da yakeyi ba, batare kuma daya ɗago ba yace "Ummm"    

Gyara zama Mas'oud yayi tare da cewa "Oummu tayimin magana akan auren Almustapha da Zieyaderh, sannan tace dani gobe Abba zaizo nakuma ce mata zan sameshi muyi magana, gaskiya RAJ nayanke shawaran zan sanar da Abba komai adangane da rashin lafiyanka!"   

Aje pen ɗin hannunsa yayi tare da ɗago kansa ya dubi Mas'oud.

"Faɗa masa matsalata bashida wani amfani Mas'oud, kabari kawai badai aure suke so nayi ba, nashirya zanyi" Yafaɗi haka cikin halin ko inkula.

"Yin aurenka bashine mafita ba Sooraj samun lafiyanka shine abunso, ya zakayi da matar idan har baka samu lafiya ba?" Mas'oud ya tambaya cike da tsananin tausayinsa.

Murmushin gefen baki Sooraj yayi tare da ɗan cizan lips ɗinsa, adai dai wannan lokacin shikaɗai yasan me yakeji.

Ɗan numfasawa Mas'oud yayi tare da cewa "Amma RAJ auren Zieyaderh da Amustapha abun na damuna sosae!"

"Why?" Sooraj ya tambaya ataƙaice.

"Sooraj"  Mas'oud yaƙira sunansa.   Ɗago kai yayi ya kalli Mas'oud ɗin batare daya amsa ba, shima Mas'oud din kallonsa yake, tabbas shikam akwai abun daya jima yana hangowa acikin idanun SOORAJ, amma baitabbatar da abunba sai ayanzu,  wani tarin tausayin Sooraj ɗinne yasake kamasa, haƙiƙa Sooraj baisan komaiba agame da so, shi mutum ne wanda yake rayuwarsa shi kaɗai, baya sharing damuwarsa da kowa,  saboda haka ba lallai ya fuskanci cewa wani abu na damunshi ba, koda ma yafahimci hakan ba lallaine yasan menene abun ba.  Kawar dakae gefe Sooraj yayi tare da miƙewa tsaye key ɗin motarsa ya ɗauka tare da cewa "Nagama signing papers ɗinnan, ka kula sai munyi waya!"

Kasa ce dashi wani abu Mas'oud yayi harya fice,  shikam Allah Yasani tausayin SOORAJ yake, tabbas yau ya hango damuwa me tarin yawa a cikin idanun SOORAJ.

Monday

Tun kafun 7 yau tagama shiryawanta, bata da wani buri wanda ya wuce taje ta sanar da Shukra damuwanta kozata ji sauƙi acikin zuciyarta, duk yanda Oummu taso ta tsaya tayi break ƙi tayi haka ta tafi makarantar da yunwa acikinta.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now