Chapter 10

12.4K 1K 56
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ !!!*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*


*WATTPAD*
@fatymasardauna

*Chapter 10*

Baijima da kwanciya ba aka soma knocking ƙofar falon, yana daga kwance yabawa maiyin knocking ɗin izinin shigowa.

Peter ne yashigo cikin falon hanunsa riƙe da wasu ledodi, cike da girmamawa ya rusuna ya gaida ogan nasa.

Amsan ledodin Sooraj yayi haɗe da ciro wallet ɗinsa ya zaro fararen ƴan dubu dubu har guda uku ya bawa peter, karɓa peter yayi yana godiya ya fice daga falon.

Ɗaukan duka ledodin yayi haɗe da nufar ɗakin da take, amemakon yayi knocking kamar yanda ya sabayi kullum, sai kawai ya tura ƙofar ya shiga ciki, a zuciyarsa kuwa yana maijin haushin bautar da yakeyi mata.

Tana kwance akan gado tayi kwanciyar ruf da ciki, bacci takeyi hankalinta a kwance, harara yaɗan wurga mata haɗe da aje ledodin, har ya juya zai fita daga ɗakin kuma sai ya tsaya, kallonta yashigayi tundaga ƙafanta har zuwa kanta, ahankali yataka zuwa inda take kwance, ƙafansa yasa ya ɗan zunguri nata ƙafan, azabure tatashi ta zauna tana mai murje manya manyan idanunta da sukayi ja. Sake kallonta yayi, sai alokacin ya lura tun rigar jiya itace har yanzu ajikinta. "Ƙazama" yafaɗi haka acikin zuciarsa.

"Ki tashi kije kiyi wanka, ke wace irin ƙazamace zaki wuni da kaya ki kuma kwana dashi?" yatambayeta yana mai kawar da kansa daga kallonta.

Ɗago idanunta tayi ta kallesa, gani tayi kamar bashine yayi maganan ba, saboda yanda ya fusge yawani kawar da kansa gefe guda.

Kallon kanta tashigayi, sam rigar jikinta bata da wani alaman abu wai shi datti, ita lokacin da take ƙauye ai sai kaya suyi sati ajikinta ma bata cireba, to inama taga yawan suturun balle ta dinga sanjawa akai akai.

"Idan kin gama ki sameni a falo" yanagama faɗan haka yafice daga cikin ɗakin.

Kamar yanda yace haka tayi, kayan jikinta ta cire taje tayi wanka, tana fitowa awanka still wata doguwar riga ta ɗauka ta sanya, sai dai wannan ba kalan waccar da ta cire bane. Ledan da ya aje mata ta ɗauka haɗe da buɗewa, yau madai robobin take away ne acikin ledan har guda uku, ɗaukan ɗaya tayi haɗe da buɗewa ta soma ci, sosai taci sannan tasha ruwa. Mayafin rigar tayafa asaman kanta sannan tafito zuwa falo.

Yana tsaye agaban fridge yabawa cikin falon baya, jin motsinta afalon yasa batare da ya juyoba yace. "Muje" nufar hanyar fita daga cikin falon yayi.

Yana gaba tana biye dashi abaya har suka ƙaraso inda motarsa ke fake. Buɗe murfin motar yayi ya shiga, key yasanya zai ta da motar, gefen da take tsaye ya kalla cike da takaici.
"Sainace ki shigo sannan zaki shigo?" yatambayeta cikin yanayi naɗan jin haushi. Buɗe murfin motar tayi ta shiga ta zauna, ƙirjinta kuwa bugawa yake kamar zai fito waje.

Tunda suka hau titi bata ɗago kanta ba, wasa take da yatsun hanunta, yayinda ƙwalla suka cika idanunta, ita kanta batasan ƙwallan na menene ba.

Yana gama daidaita parking ɗin motar ya cire earpiece ɗin dake saƙale acikin kunnensa.

"Muje" ya faɗa yana maiƙoƙarin fita daga cikin motar.
Sai alokacin ta ɗago kanta ta kalli inda ya kawota, batasan ina bane, saidai taga mutane nata shiga da fice a wajen, haka ta fito daga cikin motar ta shiga bin bayansa, saida suka shiga cikin wajen sannan tafahimci cewa asibiti suka zo, ji tayi gabanta ya faɗi, aranta tace "Allah Yasa ba allura yakawoni ayi min ba."

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now