Chapter 11

12.3K 969 55
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ !!!*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

*Wattpad*
@fatymasardauna

*Chapter 11*

Tunda jirgin su ya ɗaga bai buɗe idanunsa ba har jirgin nasu ya sauƙa a NNAMDI AZIKWE Internation airport. Buɗe idanunsa yayi a hankali tare da zare sit belt ɗin dake jikinsa, dubansa ya kai zuwa gareta, wani babban abun mamaki ganinta yayi tana bacci, fuskarta ɗauke da wani bushashshen hawaye, takaicinta ne ya sake kamashi, shi sam baisan ita wace irin bagidajiya bace ba, yanzu aɗan tafiyan da bai wuce 30 minute ba har ace tayi bacci ?

Hanunsa yasa ya zunguri kanta, da yake baccin nata baiyi nisa ba, hakan yasa ta buɗe idanunta, ta sauƙe ƙwayar idanunta a kansa.

Nuni yayi mata da ta cire sit belt ɗin dake jikinta, cire sit belt ɗin tayi tana mai mutsutstsuka idanunta da suke cike da bacci.
Gudun kada tayi masa halinnata na ƙauyanci ta ba da shi agaban mutane yasa ya tusa ƙeyarta gaba suka nufi hanyar fita daga cikin jirgin.

Cikin takunsa na isa yake sauƙowa daga kan matattakalan jirgin, sanye yake da riga da wando na jeans baƙaƙe sai kuma facing cap white colour daya sanya akansa, kalan takalman dake ƙafansa.
Kallo ɗaya zakayi masa kafahimci cewa shiɗin cikakken ɗan gaye ne wanda yake murza naira. babu wani makusa atattare dashi, komai nasa yayi hundred percent, sam a halittarsa ta bayyane bazaka taɓa kawo cewa yana ɗauke da wata damuwa ba, saboda shiɗin irin mazan nanne masu aji da wayewa, sannan yanada cikar halitta, komai nasa abun so ne ga ƴa macen da tasan kanta. yanada kyawun jiki data fuska, ajikinsa dai kam baida wata makusa, amma kuma saidai shikaɗai yasan menene aibunsa, wanda idan da zai bayyana rauninsa a fili, to tabbas da sai kowacce mace ta gujesa, saboda aibun dayake ɗauke dashi, yafi tsananin kyawu da dukiyarsa tasiri wajen rugujewar farincikinsa. idan akayi dubi da lalurar dake damunsa shekara da shekaru to tabbas kyawunsa da haɗuwarsa ba zasu amfana masa komaiba, dama kuma hakane yawanci kowani bawa da irin tasa tawayan.

Yana gama sauƙowa daga kan matattakalan ya gyara zaman facing cap ɗin dake kansa. Wani matashin saurayi ne ya ƙaraso wajen da suke da sauri. Cike da girmamawa ya ce.

"Barka da zuwa Oga"
yaƙare maganar yana mai karɓan jakan dake hanun Sooraj ɗin...

"Yauwa!" Sooraj ya amsa ataƙaice.

Juyowa yayi ya kalli Ziyada dake ta faman murje gajiyayyun idanunta, tana kuma ƙarewa haɗaɗɗen wajen kallo, domin kuwa wannan airport ɗin ya ɗarawa wanda suka baro.

"Kuje mota ina zuwa" yafaɗi haka yana mai ƙoƙarin shiga wata babbar ƙofa ta glass dake cikin airport ɗin.

"Ranki yadaɗe muje ko" wannan saurayin yace da Ziyada, da haryanzu take ta kalle kalle. Babu musu tabi bayansa, sai dai a ƙasan zuciyarta shumfuɗe take da tsoro, zuwa yanzu wata zuciyar na sanar da ita cewa "Sai da ita Sooraj zaiyi" hakanan zuciyarta tasa mata cewa ba banza yake ɗawainiya da ita ba, saidai kuma ta wata fuskar sam baiyi kama da mugayen mutane ba, duk da bayi da sakewa, amma baiyi kamanni da mugaye ba.

Direct wajen wata dan ƙareriyar mota taga sun nufa, buɗe mata gidan gaba ɓangaren mai zaman banza matashin saurayin da ake ƙira da Kamalu yayi, yana mai satan kallon fuskarta, mamakine cike azuciyarsa, yana mamakin a ina ogansa ya samota, yasan Sooraj yakuma san baida wata ƙanwa mace balle yace itaɗin ko ƙanwarsa ce, ya kuma san halin ogan nasa baya neman mata, balle ko yace wata ya ɗauko zasuyi zaman haramci, da wannan tunanin yashiga ɓangaren driver ya zauna.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now