Chapter 16

11.1K 991 52
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ !!!*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*
@fatymasardauna

#romance

*Chapter 16*

Saturday!

Kamar dai yanda kowa ya sani saturday ranar hutuce ga yawancin ɗaliban makarantar boko. To haka ranar yau ta kasance saturday wato (Asabar). Zaune take aƙasa ta tanƙwashe ƙafafunta, jakar makarantarta ne agabanta, sai kuma wani littafin English ɗin dake riƙe a hanunta, lecture'n da akayi musu jiya take dubawa, so take karatun ya zauna akanta sosai, don taji malamin nacewa wani sati zai basu Assignment. Tunda tayi sallah ta ke riƙe da littafi, gaba ɗaya hankali da nutsuwarta naga littafinta so take ta iya duk wani abu da aka koya musu, a yanda ta ba da himma ne yasa ta fahimci wasu abubuwa da dama, wato shi karatu ɗan naci ne idan kanace masa da yardan Allah Zaka iya, sannan zaka gane komai sannu ahankali, yarda da wannan da tayi ne yasa abubuwa da yawa dake cikin karatun da take suka zauna akanta. Yunwar da ta soma ƙwaƙulan cikinta ne yasa ta aje littafin haɗe da jingina bayanta da jikin gado, ajiyar zuciya ta sauƙe, tare da lumshe idanunta da suke cike da bacci, kasancewar daren jiya bata wani samu isashshen bacci ba, domin kuwa jiya ba tayi bacci da wuri ba, har sai wajen ƙarfe 12:30 na dare sannan ta kwanta, karatu tayi sosai, sannan gashi kuma yau tayi tashin sassafe sakamakon wani irin zazzaɓi dake ta sanɗanta tun jiya da rana, amma dayake zazzaɓin baiyi ƙarfi ajikinta ba hakan yasa bata jikkata ba.
***
Duk da cewa yau Asabar amma bayajin zai iya zaman gida, shi kansa yasan yana da buƙatar hutu amma kuma yasan ko ya zauna agida hutun nasa bazai samu yanda yakeso ba. Fitowarsa awanka kenan yana ɗaure da towel a ƙugunsa, sannan kuma ga wani ɗan ƙaramin towel still dake riƙe a hanunsa, yana tsane ruwan dake kansa. Yana gamawa ya ɗauko handryer, da shi yayi amfani wajen busar da gashin kansa, mayinsa mai ƙamshi ya shafa, sannan ya ɗauki comb ya shiga taje sumar dake kansa, mayukan gashi har kala uku ya shafawa kansa, take gashin kannasa ya ƙara bayyana sheƙi da kuma walwali. Dogon wandon jeans wanda ke ɗauke da zane irin na kayan sojoji ya sanya, wandon irin mai yawan aljihunnan ne sannan ƙasan wandon atsuke yake da rubber, wata farar t-shirt ya sanya ajikinsa, take kyawunsa ya sake bayyana sosai kayan suka amshi jikinshi, kasancewarsa namiji mai murɗaɗɗiyar surar jiki, gun ƴar ƙaramar drawer'n da yake aje drugs ɗinsa ya nufa, wani magani dake cikin sachet ya ciro, tare da ɓallan guda biyu ya watsa abakinsa, sannan yakora da ruwan swan. Hanunsa riƙe da goran swan ɗin ya nufi falo.

Yana shiga cikin falon ya soma bin ko ina dake cikin falon da kallo, ko alaman datti babu acikin falon, hakanne ya tabbatar masa da cewa tabbas gyara falon akayi, duk da cewa dama babu wani datti acikin falon, amma dai kallo ɗaya zakayi kasan an gyara falon.

Kitchine ya wuce ya tafasa ruwan zafi acikin heater cup, yana gamawa ya juye a flask. Zama yayi akan dinning tare da haɗa tea ɗinsa. Sanya kofin tea ɗin yayi agaba ya kasa koda ɗauka ne yakai bakinsa, sai jujjuya spoon ɗin dake hanunsa yake acikin cup ɗin, yanayin yanda ya nutsu yayi shiru shine abun da zai baka tabbacin cewa tunani yakeyi. Tabbas kuwa tunanin yake, maganganun da mahaifinshi yayi mishi masu tsauri su suke damunshi, bai ɗauka fushin da mahaifannashi keyi dashi har yakai haka ba, bai taɓa tunanin suma zasuƙi fahimtarshi ba, maganan da Abbanshi yayi mishi akan cewa wai ya nemo matar aure ya aura, acikin ƴan ƙanƙanin lokaci idan ba haka ba kuma kada ya sake ƙiran wayanshi shine abun dake damunsa, tabbas hukuncin da Abbansa yayi mishi yayi tsauri da yawa, koda wasa baitaɓa tunanin zasu sake kawo mishi maganar aure nan kusa ba, ya ɗauka zasu fahimceshi a wuce wannan stage ɗin, ashe abun ba haka yake ba. Wayarsa dake gefensa ne tasoma ƙara alaman shigowan ƙira, jikinsa a sanyaye ya ɗaga ƙiran tare da kara wayar akan kunnensa.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now