Chapter 37

11.3K 1.1K 128
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
           
             *SOORAJ!!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*
       
            *WATTPAD*
      @fatymasardauna
#romance

*This page is dedicated to you my dear @Zeety delight... heart you dear*

            *Chapter 37*

Da tsananin farinciki ɗauke akan fuskar ko wannensu Oummu da Malam Garba suka shigo cikin gidan, Inna Ma'u na ganin hakan wani ƙaton baƙinciki ya ɗarsu azuciyarta, hakanan taji ajikinta cewa hanyar ƙaruwa suka tattauna, ae kuwa nan ta ƙudura aranta cewa Oummu na tafiya sai tayi maganin Malam Garba, yadae santa ae yakuma san wacece ita.

Kallon Zieyaderh Oummu tayi fuska ɗauke da murmushi tace "Inaga ya kamata ae ace mutafi tun yanzu, kada tafiyan dare ya kamamu"   
Jin abun da Oummu tace yasanya ƙirjinta bugawa, ahankali ta ɗago idanunta tare da ɗan satan  kallon mahaifinnata, cikin rashin sa'a tasamu shiɗinma kallonta yake, da sauri tayi ƙasa da kanta, murmushi yayi tare da cewa "Bakomai kuje Zieyaderh Allah Yakiyaye hanya ya tsare, nima inanan zuwa tunda yanzu nasamu adreshin inda kuke." 
Wani irin sanyi ne Zieyaderh taji na ratsa zuciarta, sam batayi tunanin mahaifinta zai barta ta koma ba. 

"Chab amma kuwa Garba kayi banzan hali, yanzun barinta zakayi ta koma, oh wato kaidai ba ka gaji da jin zagin da mutane ke mana agarinnan ba, karka manta fa duk  akan ɓatanta sunanmu ya ɓaci,  to babu inda zataje tananan tadawo kenan!" Inna Ma'u ta faɗa amasifance, don sam bata tsammaci haka ba.

"Haba Ma'u meyasa ne bazaki sanja ba, dan Allah Kibar yarinyarnan tayi tafiyarta, tafara karatu acan birni, tsayar mata da karatunta bashida wani amfani"  Malam Garba yafaɗi haka cikin ɗan lallashi saboda yasan halin kayansa sarai ba mutumci.

Cike da kumfar baki Inna Ma'u tace "Dole kace haka mana saboda ƴar kace, ai dama ninasan banice na haifeta ba, kuma zaman birni kam wannan algungumar ƴar taka ta gama yinshi....." Bata gama rufe bakinta ba taji sauƙar wani abu me ɗan nauyi akan cinyarta,   idanu ta zaro lokaci guda tare da haɗiye maganan dake bakinta, take yanayin fuskarta ya sauya daga ɓacin rai zuwa murmushi. "To Alhamdulillah, irin wanga farare bugun can babban birni, Hajiyan Birni Allah ya ƙara arziki!" Inna Ma'u tafaɗa bakinta har kunne,   kuɗine masu yawa Oummu ta aje mata don rufe bakinta, ai kuwa lokaci guda sai ga bakinnata ya rufu .    cike da nishaɗi tace.
"To yanzu sai yaushe zaku kuma dawowa?"    yanayin yanda tayi maganan tana me ƙoƙarin cusa kuɗin cikin lalitantane yabasu daria amma sai suka gimtse, ɗauke da ɗan murmushi Oummu tace.
"Nan bada jimawa ba Insha Allah, Nangaba kaɗan kema nasan zaki kaimana ziyara!"

"Sosaima kuwa, kice  ziyarori ma ba iyaka ziyara kaɗai ba, don fa basau ɗaya zanzo ba!!" Inna Ma'u tafaɗa cikin jin daɗi, dama ita abun duniya shine kanta.

Har wajen mota suka rakasu,  bayan motar  Oummu ta buɗe wanda ke shaƙe da kaya, Kamalu driver tasanya ya shiga ciro kayan yana kaiwa cikin gidansu Zieyaderh, kayan abincine kala kala da kuma wata leda dake ɗauke da kayan sawa, atamfofi da shadda irin na maza, godiya kam ba irin wanda baban Zieyaderh baiyi mata ba, duk da yanuna mata cewa kayan sunyi yawa, amma saitace masa ba komai,  koda ta bashi kuɗi ƙin amsa yayi babu yanda batayi dashi ba amma haka yaƙi amsa, Inna Ma'u kuwa daɗine ya isheta, musamman ma ganin ana shigar da kayan abinci cikin gidanta.  Haka su Zieyaderh suka baro cikin ƙauyen zuciarta cike da kewan babanta.    Har bacci tayi a hanya kafun su iso, gaba ɗaya zaman mota ba daɗi ji take duk jikinta yayi mata wani iri.

Suna isa gida kowa ɗakinsa ya wuce, don gaba ɗayansu agajiye suke,  da ruwan zafi tayi wanka kana tabi lafiyar gado.

Sunday. 
Yawanci duk ranan weekend atare suke cin abinci akan dinning,  tun 8 tatashi tayi wanka,  riga da sket na 1million stones tasanya wanda suka amshi jikinta sosai, tayi kyau.  Wani ɗan madaidaicin mayafi ta sanya ta rufe jikinta, a kitchine ta samu Oummu cike da ladabi ta gaida ta,  fuska ɗauke da fari'a Oummu ta amsa mata,  yauma kamar koda yaushe itace ta shirya gaba ɗaya abincin akan dinning.   Ƙamshin turaren Almustapha daya shiga hancinta shi yasanyata ɗago da kai ta ɗan kalleshi, ƙasa tayi da kanta tare da gaidashi,   amsa mata yayi yana me jan kujera ya zauna, sosai yau ɗin tayi masa kyau acikin shigarta,  duk da cewa bai taɓa ganin kwalliya akan fuskarta ba amma gaskiya tana da kyau sosai.  

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now