Chapter 24

11.6K 1.2K 81
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

        *SOORAJ!!!*

   *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

        *Wattpad*
   fatymasardauna

#romance

*Taƙabbalullaha Minna Wa Minkum. May Allah make us stead fast on the path of the righteous,elevate our iman, forgive our sins and bless us abundantly.   Ameen Ya Rab!!!*
*🥀EID MUBARAK My Lovely Fans🥀*

         *Chapter 24*

Kamar amafarki haka taji sauƙan hanunsa acikin nata.

Da sauri ta waiwaya zuwa gareshi, amma sai taga ko motsi baiyi ba, hasalima idanuwansa   akulle suke da'alama bai dawo cikin hayyacinsa ba.  Ahankali ta koma ta zauna tare da kafe sa da ido,  zara zaran eye lashes ɗinsa da suka kwanta luf luf take kallo, ahankali tayi ƙasa da idanunta tana kallon ɗan ƙaramin pink lips ɗinsa wanda suka ɗan bushe. Idanunta ta sake mayarwa kan lallausan sajen dake kwance akan fuskarsa, baƙaƙen hairs ne kwance luf akan fatarsa, komai nasa me kyaune kuma gwanin burgewa.  Kanta ta mayar jikin gadon tare da lumshe idanunta.  Wani irin tausayinshi takeji,  daga wani ɓangare na zuciarta kuwa tunanin Farouk ne yazo yayi tsaye.  Bazata  iya faɗin me takeji game da shi ba, amma tabbas akansa tanajin wasu baƙin al'amura suna ziyartan ta.  Zare hanunta dake cikin nasa hanun tayi tare da miƙewa tsaye, toilet tashiga ta ɗauro alwalan sallan isha'i. 

Tajima tana zaune akan sallayan. Wasu siraran hawayene suka silalo daga cikin idanunta, kallonta takai zuwa garesa,  wasu sabin hawayene suka sake fitowa daga cikin idanunta, hakanan batasan me yasa ba aduk sanda ta ɗaura idanunta akansa takanji zuciarta ta karye, tasan da cewa ita mai raunice tun tuni, amma akansa raunin da takeji na dabanne.  Tajima zaune akan sallayan har kusan 9 pm sannan ta tashi ta koma bakin gadon ta zauna.  Kanta ta ɗaura adaidai saitin kanshi tare da lumshe idanunta. Mintuna goma tsakani bacci ya ɗauketa batare da ta shiryawa hakan ba.

Ahankali breath ɗinta ke fita, yayinda hucinsa ke sauƙa adaidai saitin kunnensa, ahankali yasoma buɗe idanunsa har ya waresu gaba ɗaya, akan zanen pop'n dake cikin ɗakin ya tsayar da idanunsa,  sosai idanun nasa suka sauya kala daga farare zuwa kalan ja, sannan lokaci guda suka ƙanƙance sai tarin eye lashes dake samansu wanda yayi wara wara,  wani irin ciwo yakejin kansa nayi masa, yayinda yakejin wani zogi na musamman adai dai chest ɗinsa.  Lumshe gajiyayyun idanunsa yayi tare da sauƙe wata gajiyayyar ajiyar zucia.  Ahankali ya ɗan yunƙura tare da ɗan jingina bayanshi ajikin pillow, saida ya ɗan cije pink lips ɗinsa sakamakon wani irin zogi dayaji ƙirjinsa nayi,  hanunsa yakai kan wani ɗan madanni dake gefen gadonnasa ya ɗan danna da ƙarfi har saida yayi ƙara.   3 minute tsakani saiga wata Nurse tashigo cikin ɗakin da gaggawa.  Ganinsa azaune yasa tashiga tambayarsa jikinnasa.  Da kai kawai ya iya amasa mata, ganin haka yasa tafita da hanzari don ƙiran Dr.Moh'd.  

Baƙaramin daɗi Dr. Moh'd yaji ba sakamakon jin cewa wai Sooraj ya farfaɗo, da ƙwarin guiwarsa haka ya nufo ɗakin da Sooraj ɗin ke kwance.

Checking ɗinsa yayi sosai sannan ya tambayesa ko akwai wani abu dake damunsa.  Kai kawai Sooraj ya iya girgizawa,  sannan yayi masa nuni da chest ɗinsa daidai inda aka ɗaure da bandage. Alaman nanne kawai ke masa zafi.
Wasu magungunan kashe zogi Dr. Moh'd  ya basa ya sha, sannan yace masa yaɗan kwanta zuwa da safe.  Har Dr.Mohd yagama abun da zaiyi yafita Ziyada na bacci bata sani ba.  Shiru haka Sooraj ya koma ya kwanta tare da lumshe idanunsa,  tunanine cunkushe acikin ransa, _ƘADDARA_ itace abun dake ɗawainiya da rayuwarsa, sau da yawa yakansamun kansa acikin ƙuncin rayuwa, sai dai dole ayanzu zai daure don yaga yayi faɗa da zuciyar da take ƙoƙarin hanasa ɗaukar ƙaddaransa.

SOORAJ !!! (completed)Onde as histórias ganham vida. Descobre agora