Chapter 5

13.3K 1.2K 52
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*
@fatymasardauna

*CHAPTER 5*

Wanene SOORAJ?

Alhaji Mansur Mai Nasara shi ne yakasance uba ga SOORAJ, Alhaji Mansur Mai Nasara wani hamshaƙin mai arziki ne dake zaune acikin garin Kaduna, Alhaji Mansur tsohon commissioner'n Ilimi ne dake zaune a cikin garin Kaduna, cikakken ɗan boko ne shi, wanda yatara dukiya, sannan mutum ne dayake jure gwagwar mayar rayuwa, wannan yasa mutane suka masa laƙabi da suna MAI NASARA, saboda duk wani abu daya sanya agaba saiyayi nasara akai. Hajiya Sulaimiya itace matarsa kuma mahaifiya ga SOORAJ, Hajiya Sulaimiya dai irin wayayyun matan nan ne, don asalinta yar ƙasar Sudan
ce, tana da kyau sosai, tsananin kyawunta yana ɗaya daga cikin abun daya sanya Alhaji Mansur, narka maƙudan kuɗaɗe wajen ganin ya aurota, zama sukeyi cike da so da kuma ƙaunar juna, koda yaushe cikin farinciki suke, shekaransu uku da aure Allah ya azurtasu da samun ƙaruwan yaro namiji, tun daga randa aka haifi SOORAJ Alhaji Mansur yaƙara ganin buɗi acikin arzikinsa, soyayyar duniya suka ɗauka suka ɗaura ta akan yaron nasu, komai Na SOORAJ irin na Mahaifiyarsa ne domin kyawunta ya ɗauko. sosai SOORAJ ke zuba tashen kyau da burgewa tun yana ƙarami, saidai yataso da wani irin hali, miskiline na ƙarshe, sannan sam baida yawan magana, komai nasa atsare yakeyinsa, tun yanada shekara 12 mahaifinsa ya turasa England acan yayi gaba ɗaya karatunsa, tundaga kan secondary school har zuwa Masters ɗinsa, P.H.D ɗinsa ne kawai yayi aƙasar America. Sosai SOORAJ yake da ƙwazo akan dukkan komai, babu ruwansa da kowa, rayuwarsa kawai yake, bashida wani aboki aduniya sama da Mas'oud, sosai abotarsu tayi ƙarfi da Mas'oud, kasancewar sun fara abotanne tun suna ƙanana, gaba ɗaya sirrin Mas'oud SOORAJ yasani, haka shima Mas'oud ɗin yasan wasu sirrukan SOORAJ, saidai akwai wani sirri da SOORAJ ɗin yaɓoyewa kowa, shikaɗai yasan matsalarsa. Tun daga kan SOORAJ Alhaji Mansur baisake haihuwa ba, amma hakan baisa sun tashi hankalinsu ba, kasancewarsu wayayyun ƴan boko, dama ba wani son tara ƴaƴa suke ba, ayanzu dai SOORAJ yana da shekara 30 aduniya, cikekken matashine mai tsananin ji da kansa, rayuwarsa yakeyi maicike da burgewa baruwansa da kowa, abune mawuyaci kaga dariyansa, duk yanda Ƴan Mata keson samun daman kai kansu garesa, hakan baya yiwuwa, domin SOORAJ wani irin mutum ne, da akomai nasa baya sanya mata aciki, duk wata mu'amalarsa baya sanya mace aciki, mace duk kyau da haɗuwarta sam bata gabansa, batama burgesa, duk wani irin karairaya da mace mai lafiya zata zo tayi agabansa bazata taɓa burgesaba, duk tsananin kyawun mace, SOORAJ bata burgesa, shi yariga daya sanya aransa cewa mace bata cikin tsarinsa. Ayanzu yana akine a babban bankin Nigeria dake cikin garin Abuja wato Central Bank Of Nigeria (CBN) yanzuma hutu ya ɗauka shiyasa ya zo Kaduna wajen iyaye da danginsa. A rayuwarsa yana tsananin son iyayensa, sai gashi kuma daga zuwansa sun laƙaba masa auren dole. Wannan shine taƙaitaccen tarihin SOORAJ MAI NASARA.

Kamar koda yaushe idan yana acikin damuwa yakan fita yazaga gari, wani lokaci har ƙauyukan dake kusa dasu yake zuwa, sosai yakejin daɗi idan yaziyarci ƙauyuka musamman irin ƙauyukan da fulani ke rayuwa acikinsu, yauma hakance takasance dashi, hakanan yaji yanason fita daga cikin gari, bayaso yakoma Abuja baije yaɗan zaga gari ba...

Tsab yashirya kansa cikin long pencil jeans black colour,and Black t-shirt, agaban t-shirt ɗinnasa anrubuta ( THE MAN) da farin fenti. white denim jacket fara irinta maza yaɗaura akan rigar dake jikinsa, sosai kayan suka amshi jikinsa kasancewarsa mai farin fata, wasu fararen takalma combat wanda aƙalla kuɗinsu zasu haura sama da 30k yasanya aƙafarsa, hmmm SOORAJ yanason gayu sosai, hakan yasa koda yaushe cikin ɗaukar hankali yake. Da turarukansa masu tsada ya feshe jikinsa, take ko ina naɗakinnasa ya gauraye da ƙamshi. Wayoyinsa haɗe da key ɗin Range Rover ɗinsa ya ɗauka, kana yafice daga cikin ɗakin.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now