Chapter 52

18.8K 1.4K 253
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

            *SOORAJ!!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

                    *Wattpad*
            @fatymasardauna
#Love

                *Chapter 52*

Ajiyar zuciya Oummu ta sauƙe tare da yi masa duban tsab, so take ta gano wani abu da zuciyarta take zargi.
Shikuwa cikin nutsuwa ya nufi ƙofar da zata sadashi da ɓangarensa, sam bai yarda yaƙara kallon Oummu ba, balle har yabari tayi masa tambayar da zai kasa bata amsa,  har ya buɗe ƙofar part ɗin nasa ya shige,  Oummu bata daina kallonsa ba, ajiyar zuciya kawai ta sauƙe, da tunani kala kala acikin ranta  ta nufi stairs inda ta hau sama.
Yana shiga cikin ɗakin kai tsaye bathroom ya nufa, ahankali ya tura ƙofar bathroom ɗin ya shiga,   tananan kwance cikin jakuzzie'n  kamar yanda yabarta, ko motsawa batayi ba, saima ƙara shigewa cikin ruwan dake cikin jakuzzien tayi, idanunta alumshe suke kamar wacce take bacci, saidai kuma azahirin gaskiya bawai baccin takeyi ba,  daɗin ruwan dake ratsa jikinta ne yasanya tayi kamar me bacci,  jin motsin buɗe ƙofarsa yasanya taƙara nutsewa acikin ruwan,  ahankali ya tako har ya kawo jikin jakuzzie'n da take kwnace, kettle ɗin dake hannunsa ya ajiye, ɗan kallonta yayi kamar zaice wani abu kuma saiya fasa, juyawa yayi yafice daga cikin toilet ɗin.
Jin motsin fitarsa daga cikin bathroom ɗin yasanya ta sauƙe ajiyar zucia, cikin ɗan kuzarin daya rage mata haka tayi wanka,   koda ta fito daga cikin Jakuzzie'n kaitsaye wajen da yake aje towels ɗinsa ta nufa, ahankali take tafiya tana ɗan rumtse idanunta haɗi da cije laɓɓanta, duk da kasancewar ta ɗanji daman jikinta bakamar ɗazu ba, amma duk da haka tana ɗanjin zafi kaɗan, wata farar Bathrobe ta sanya ajikinta,  ahankali take tafiya don batajin zata iya ɗaga ƙafarta da kyau, murɗa handle ɗin ƙofar ta fito,  ganin bata ganshi aɗakin ba yasanya ta nufi drawer da ɗan sauri,  ɓangaren da kayanta ke cike aciki ta buɗe, wata orange colour babu gown me faɗin wuya ta sanya, sosai rigan ya amshi jikinta duk da kasancewar bai bayyana shape ɗinta ba, amma ya amshi jikinta sosai, agurguje tasa hijab tare da tada sallah, dan sosai rana taƙara fitowa, koda ta idar da sallan bata tashi akan sallayan ba, zama tayi tare da somayin azkar, daidai lokacin ya turo ƙofar ɗakin yashigo hannunsa ɗauke da wani babban basket,  aje basket ɗin yayi tare da sanya hannu ya cire t-shirt ɗin dake jikinsa, take murɗaɗɗiyar surar jikinsa ta bayyana, zama yayi akan sofa wanda ke malale saman tiles ɗin ɗakin, babban basket ɗin yajawo gabansa tare da ɗaukan plate, food flask ya ciro daga cikin kwandon haɗi da buɗewa, soyayyen chips da egg ne aciki, kaɗan ya zuba chips ɗin acikin plate, kana ya ƙara ɗauko wata kula wanda take ƴar madaidaiciya,  koda ya buɗe kulan sauce ɗin tomatoes nd onion ne  wanda yayi kyau sosai, kaɗan ya zuba sauce  akan chips ɗin,    fork ɗin ya sanya acikin plate,  da ɗaya ɗaya yake tsakalan chips ɗin yana kaiwa bakinsa, ahankali yake tauna abincin cikin wani irin salo da burgewa,  shafa azkar ɗin tayi tare da ɗan juyowa ta saci kallonsa, ganin hankalinsa ba akanta yake ba, yasanya ta kasa ɗauke idanunta daga kansa, sosai ya ƙarayi mata kyau a ido, bakinsa dake motsawa ahankali ta kalla, komai nasa gwanin burgewa, yanayin komai acikin nutsuwa,  idanunta taɗan lumshe a hankali kana kuma ta buɗesu alokaci guda, sam takasa janye idanunta daga garesa,  tanaji ajikinta cewa batakai matsayin da wannan haɗaɗɗen gayen zai ƙirata da sunan matarsa ba,  tanaji ajikinta ya ɗarata da komai,  shi na musamman ne, komai nasa yafita daban dana sauran maza,   kowani bugun xuciyarta da tarin soyayyarsa take tafiya, haka kuma kowani numfashi da zata shaƙa tare da zazzafan soyayyarsa yake shiga,   idanunta ne suka ciko da ƙwalla wanda kuma batasan na menene ba,   ahankali yake tauna abincin dake bakinsa, sarai yasan cewa shi take kallo, don tuntuni jikinsa yabasa cewar kallonsa take, ahankali ya ɗago da kansa yayinda ya watsa mata kyawawan fararen idanunsa,  wani irin shock taji ajikinta alokacin da idanunsa suka faɗa cikin nata, take tayi ƙasa da kanta tare da turo ɗan ƙaramin bakinta,  teeth ɗinta tasanya taɗan danne lips ɗinta,  ahankali tasoma wasa da yatsun hannunta.
Wani ɓoyayyen murmushi yayi cikin husky voice ɗinsa yace.
"Bani ruwa."  sanin cewa da ita yake yasanyata ɗago da kanta ta kallesa, gani tayi kamar bashine yayi maganan ba, domin kuwa tuni ya maida kansa ga abincin dake gabansa wanda ko rabi baikai ga ci ba.
Miƙewa tsaye tayi  taku biyu zuwa uku da tayi ta ɗan tsaya tare da rumtse idanunta,  haryanzu tana ɗanjin zafi, ahankali taci gaba da takawa harta ƙarasa gaban ɗan maidaidaicin fridge ɗin dake cikin ɗakin, wanda yake da murfin glass daga nesa kana iya hango abubuwan dake cikinsa.
Buɗe fridge ɗin tayi tare da ɗauko goran ruwan swan wanda yake da sanyi sosai,  ƙarasowa garesa tayi, ƙoƙarin rusunawa take don ta miƙa masa bootle water'n, batare da ta ankara ba yasanya hannunsa ya jawota gaba ɗaya tafaɗo  jikinsa, hannayensa yasanya ya matseta ƙam acikin jikinsa,  ɗan ƙaramin bakinta tasake turowa gaba, cikin yanayi na shagwaɓa tasoma ƙoƙarin zillewa daga jikinsa,  hannunsa yasanya inda ya zare hijab ɗin dake jikinta, take dogon gashinta wanda keta shining ya watso zuwa kan fuskarta, ɗayan hannunsa yakai yayinda ya matsar da gashin nata wanda ya ɗan rufe gefen fuskarta,  kyawawan idanunsa ya sauƙe akan kyakkyawar fuskarta,  lumshe idanunta dake cike da ƙwalla tayi don bazata iya jure ganin cikin idanunsa ba,  hannunsa yasanya yaɗan shafi gefen fuskarta, ahankali yayi ƙasa da idanunsa inda ya sauƙesu akan beautyful breast ɗinta wanda kusan rabinsu suka bayyana ta saman wuyan rigar dake jikinta, kasancewar rigar nada faɗin wuya,  lumshe idanunsa yayi tare da yin ƙasa da kansa, inda ya haɗe forehead ɗinsu waje ɗaya,  yatsansa yasanya ahankali yake shafa kan laɓɓanta masu taushin gaske, iskan bakinsa ya ɗan hura akan fuskarta ta, ahankali taɗan buɗe idanunta, wani irin sanyi takeji na ratsa gaba ɗaya ilahirin jikinta, yayinda takejin daɗin abun da yakeyi mata akan bakinnata,    aɗan hankali ya ɗago kansa, jawota jikinsa ya sakeyi tare da gyara mata zama akan cinyarsa,  fork ya ɗauka tare da ɗan cakan chips kaɗan,   fork ɗin yakai dadai saitin bakinta,  cikin wata irin murya me sanyi yace.
"Buɗe bakinki!."
Yanayin yanda yayi maganan cikin sanyi yasanya taji wani irin abu yabi jikinta har zuwa tafukan ƙafanta, samun kanta tayi da kasa musa masa, ɗan ƙaramin bakinnata ta buɗe, ahankali ya sa mata fork ɗin acikin bakinta,  idanunta ta rufe sannan tasoma tauna chips ɗin ahankali kamar yanda ɗazu taga yanayi, idanunsa ya zuba mata yana kallon yanda take sarrafa bakinta wajen cin abincin,wanda hakan yaƙarawa fuskarta kyau. tana gama cinyewa yaƙara sa mata wani acikin bakinnata, haka yadinga sa mata abincin acikin bakinta,  yayinda ita kuma take taunawa ahankali,   chips ɗin yaƙara ɗebowa yakai bakinta,  shagwaɓe fuska tayi tare da girgiza masa kae alaman taƙoshi, ajiye fork ɗin yayi tare da ɓallan tissue ahankali ya goge mata ɗan ƙaramin bakinnata, bootle water'n da ta kawo masa ya ɗauka tare da ɓalle murfin, cikin wani ɗan ƙaramin cup ya zuba ruwan tare da ɗaukan cup ɗin yakai bakinta,  bakinta ta ɗaura ajikin cup ɗin ahankali take zuƙan ruwan, lumshe idanunsa yayi yanajin wani irin sanyin ƙaunarta na ƴawo acikin jikinsa,  hannunta tasanya taɗan matsar da kofin daga bakinta,  kallonta yayi da lumsassun idanunsa,
gane abun da kallon nasa ke nufi yasanya taɗan turo bakinta gaba, cikin shagwaɓa tace. "Naƙoshi."
Aje cup ɗin yayi tare da sanya hannayensa ya kama waist ɗinta, cikin kulawa ya matso da fuskarsa daf da nata, forehead ɗinsa ya ɗaura akan nata, har takai ga hancinsu na gogan na juna, idanunsa ya lumshe ahankali yake fitar da wani irin numfashi,  itama lumshe idanun nata tayi tare da sakar masa jikinta gaba ɗaya, sosai yanda numfashinsu ke cakuɗa dana juna yasanyashi jin wani irin kasala na sauƙar masa,  ɗan matsar da fuskarsa gefe yayi, ahankali yake ɗan goga mata lallausan sajen dake kwance akan fuskarsa agefen nata fuskar,  lumshe idanunta tayi tare da sakin wata irin ajiyar zuciya, sosai hakan da yakeyi mata, ke yi mata daɗi, musamman yanda lallausan gashinnasa ke gogan fresh skin ɗinta, hannunta ta ɗaura akan shoulder ɗinsa, yayinda shikuma ya kai bakinsa daidai saitin kunnenta, slowly haka yake yawo da harshensa acikin kunnenta,  kasa jurewa tayi har saida ta ƙara shigewa cikin jikinsa, bakomai ke zautar da itaba kamar yanda harshensa ke yawo acikin kunnenta, gefe guda kuwa ga daddaɗan ƙamshinsa dake zautar da ita,  ahankali ya kwantar da kansa akan wuyanta, numfashi yake fitarwa ahankali bakinsa ke motsawa da alama wani abu yake son faɗa, tabbas yana so ya furta mata saidai yanajin zuciyarsa nayi masa nauyi, yanajin kamar bayanzu yakamata ace ya faɗa mata ba,  sake lumshe idanunsa yayi haɗe da matseta acikin jikinsa, sosai ƙamshin dake fita ajikinta keyi masa daɗi,  mintuna sama da goma suka shafe ahaka batare dakowannensu ya ƙara ƙwaƙƙwaran motsi ba, tuni Zieyaderh kuwa wani irin bacci ya fara fusgarta, don aduk sanda tajita cikin jikinsa wani daɗi takeji na musamman, sannan tana samun wata irin gamsuwa,  ahankali yaɗan janye jikinsa daga nata, duban fuskarta yayi, itama dubansa tayi  da idanunta wanda suka fara ɗan lumshewa, ɗaukanta yayi caɗak inda ya ƙarasa da ita zuwa kan gado, kwantar da ita yayi akan gadon tare da jawo blanket ya rufe mata rabin jikinta, sunkuyowa daidai fuskarta yayi lumshe idanunsa yayi ahankali ya ɗaura laɓɓansa akan nata, slowly yaɗanyi sucking lips ɗinta, hannunsa yasanya yashafi gashin kanta,  ɗagowa yayi tare da kashe mata gaba ɗaya hasken ɗakin,  hannayensa ya tura cikin aljihun wandonsa kai tsaye ya nufi hanyar fita daga cikin ɗakin.
Tanajin ficewarsa  ta lumshe idanunta, sannu ahankali tarin ƙaunarsa ke ƙara ratsa cikin jiki yana huda jijiya da ɓargonta.

Daga ɓangaren nasu kai tsaye babban compound ɗin gidan ya nufa,  direct wajen da cars ɗinsa ke ajiye yanufa, wata ɓaƙar mercedes benz ya shiga, koda maigadi ya wangale masa makeken gate ɗin, ahankali ya cilla motar tasa kan titin dake shimfuɗe direct tundaga ƙofar gidannasu har zuwa ƙarshen hanyar da zata fitar dakai a unguwar tasu ta Maitama.

Sannu ahankali yake murza steering  motar, zuciyarsa ɗauke take da tunaninta mai tarin yawa, sosai yakejin wani abu na musamman agame da ita na game gaba ɗaya jikinsa,  da tunani kala kala acikin ransa yaƙaraso haraban babban asibitin.
Cikin nutsuwa yake tafiya yayinda ya nufi hanyar da zata sadashi da office ɗin Dr.Waleey.
Amna sakateriar Dr.Waleey na ganinsa ta miƙe da sauri cikin mayen sonsa da tajima tanayi taɗan ƙaraso da sauri, cikin ƙasa da murya tace.
"Ranka ya daɗe barka da zuwa." 
Kansa kawai ya ɗaga mata batare daya ce da ita komai ba, ganin fuskarsa atsuke kamar koda yaushe yasanya ta juya da sauri ta nufi office ɗin na Dr.Waleey,   bawani jimawa tafito inda tanuna masa ƙofan office ɗin alaman ya shiga, baiko kalli inda take ba ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shige ciki.
Dr.Waleey naganinsa ya saki murmushi tare da tasowa ya bawa SOORAJ ɗin hannu suka gaisa,   kujera ya nunawa Sooraj ɗin, bayan Sooraj ya zauna ne yajawo kujeran dake facing na Sooraj din shima ya zauna.
Cikin rashin sabo da yawan magana Sooraj yaɗan ɓata fuska, cike da aji yasanarwa Dr.Waleey irin zazzafan zazzaɓin dake damun jikinsa, sannan yaƙara da sanar masa yanda kansa ke masa bala'in ciwo kamar zai rabe gida biyu.
Murmushin tsananin jin daɗi Dr.Waleey yayi don aɗan  bayanin da Sooraj ɗin yayi masa tuni yagano abun dake damunsa,  cikin jin daɗi da kuma son kwantar masa da hankali Dr. Waleey yayi ajiyar zuciya, tare da gyara zama,  kana yace.
"Ƙwarai naji daɗin wannan labarin SOORAJ, tabbas alamomin zazzaɓi da ciwon kannan da kakeji alamane dake nuna cewa kaima yanzu kazama cikakken Namiji mai lafiya,  dama cutarka ba da ita aka haifeka ba, sannan kuma ba sihiri ko shafar aljanu bane, cuta ce da Allah Kan iya sawa kowani bawa,  Allah Shi ya ɗaura ma kuma gashi ayanzu shi ya yayema, tabbas wannan yana daga cikin ƘADDARANKA  dama ita Jarabawa takanzowa bawa ta inda baizata ba, sannan idan tayi tsanani Allah yakan sauƙaƙata, kada kayi mamakin samun lafiyarka SOORAJ saboda cuta da kuma sauƙi duk na Allah Ne, Allah Ne kaɗai kan iya bayar da lafiya ga bawa aduk lokacin dayaso."
Ɗan numfasawa Dr.Waleey yayi tare da ɗaukan wata farar takarda yaɗanyi rubutu kaɗan akai, miƙawa Sooraj paper ɗin yayi cikin kulawa yace.
"Ga wannan idan kafita sai kasaya a babban pharmacy, magungunane da zasu sauƙaƙa wajen hana zafin zazzaɓin yin ƙarfi, bare har yakai ga ya dameka, kuma sannan zazzaɓin ya shigeka ne saboda yanayin yanda ka sarrafa jikinka batare daka saba ba, Insha Allah Nanda wani lokaci  komai zai dawo normal, sannan ayanzu zakanajin wani irin feeling na tasomaka sosai, kada kace zaka jure abunda kakeji,  ka ƙoƙarta yin sex akai akai zai taimaka ƙwarai  wajen dawo maka da cikakkiyar lafiyarka."

Amsan papern Sooraj yayi tare da miƙewa tsaye, jin surutan da Dr.Waleey'n  keyi, har yasanya kansa ya fara yi masa ciwo, hannu ya bawa Dr.Waleey inda sukayi musabaha daga nan yayi masa sallama, koda ya fito daga cikin office ɗin na Dr.Waleey haka Amna tabisa da wani irin mayataccen kallo harya ɓacewa ganinta, sosai yake tsananin burgeta, kama daga yanda yake dressing da kuma yanda yake aiwatar da komansa cikin nutsuwa,  haka kuma sosai MISKILANCI nsa ke burgeta, duk da cewa miskilancinnasa ya zarce misali amma ahaka take kwaɗayin rayuwa dashi, saidai kuma tasan kamar yanda wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa, haka shima yayi nesa da ita, don yazama kamar wutsiyar raƙumi itakuwa tazama tamkar ƙasa, dama ance hanyar jirgi daban hakama na mota daban.

Yana isa compound ɗin asibitin direct inda motarsa take ya nufa, yana shiga yabata wuta.

Gudu sosai yake shararawa akan babban titin  dazai sadashi da unguwar ta Maitama, sanye yake da  baƙaƙen kaya ajikinsa yayinda yasanya wata baƙar mask ya rufe gaba ɗaya fuskarsa, idanunsa kawai zaka iya hangowa,  ayanda yakejin zucia da ransa na tafasa yanajin komai ma zai iya aikatawa, ayau bayajin zai iya haƙuri yashanye ɓacin ran da SOORAJ ke ɗura masa,  SOORAJ ya ƙwace masa komai, a sanadin sa yarasa abubuwa da dama, asanadin SOORAJ yarasa babban matsayin dayake kai, sanadin SOORAJ company'nsa wanda yake matuƙar ji dashi ya durƙushe,  akodayaushe sunan companyn ƙera abayas na SOORAJ dake Dubai ne ke yawo ƙasashe ƙasashe ba nasa ba kamar yanda yakeso,   SOORAJ yasashi ya rasa abubuwa da yawa, ciki kuwa harda yarinyar dayake fatan kashe ƙishin ruwansa akanta,  saboda haka baya tunanin zai iya barin SOORAJ ya rayu cikin duniya.

SOORAJ kuwa ganin ya kusa shigowa cikin unguwar tasu ta maitama ne yasanyashi ɗan ƙara gudun motar, daidai zaisha wata kwana batare da ya kula ba wata mota tayiyo kansa da gudun gaske, shima batare daya taka birkin motar tasa ba yayi kan motar, wani irin karo da sukayine yasanya gaba ɗaya motocin nasu tashi sama, alokaci guda kuma suka faɗo ƙasa, cikin ƴan mintuna ƙalilan gaba ɗaya motocin suka fara fitar da hayaƙi. 

*Vote*
*and*
*Comment*

           fatymasardauna

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now