Chapter 15

11.4K 1.1K 67
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ !!!*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*
{United we stand and succeed our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
*https://ww.facebook.com/kainuwawritersassociation*


*WATTPAD*
@fatymasardauna

#romance

*Chapter 15*

Cikin sanyinta ta nufi inda teacher Abdallah ya nuna mata. Ɗaya daga cikin ƴan matanne ta bita da wani irin kallo. teacher Abdallah yana ganin ta zauna ya fice daga cikin class ɗin bayan ya bata jakar makarantarta mai kyau.

Gaba ɗaya jinta take atakure, kasancewar kusan gaba ɗaya rabin ƴan ajin idanunsu na kanta.

"Sannu!" matashiyar budurwan dake gefenta ta faɗa, wacce aƙalla bazata wuce sa'an Ziyada'n ba.

Sai alokacin Ziyada ta ɗago da kanta ta kalli wacce tayi mata maganan. murmushi tayi mata haɗe da cewa "Yauwa!"

Murmushi itama yarinyar tayi tare da sake cewa.
"Sunana Nasmah, kefa?"

"Sunana Ziyada" Ziyada ta bata amsa tana mai ɗan faɗaɗa fari'an dake kan fuskarta.

"Nice name!" Nasmah tafaɗa tana mai ɗaukan wani text book dake gabanta.

Ɗan satan kallonta Ziyada tayi haɗe da yin murmushi, duk da cewa bata fahimci me Nasmah'n take nufi ba.

Shiru Ziyada tayi bata sake cewa komai ba, yayinda suma ƴan matan sukayi shiru, Nasmah gaba ɗaya hankalinta nakan littafin dake hanunta, yayinda wacce ke gefen Ziyada ta ɓangaren damanta kuwa ko ƙala bata ce ba, sai dai time to time tana yawan kallon Ziyadan, maganane abakinta amma saboda halin jin kai irin na Shukhra ta kasa cewa komai.

Wani malami ne ya shigo cikin ajin, dukansu ɗaliban suka tashi tsaye haɗe da gaidashi, sai da ya ɗan yi rubutu kaɗan akan white board ɗin da ke cikin ajin sannan ya basu izinin zama.

Darasin Maths yake koyar musu cike da ƙwarewa, yayinda gaba ɗaya ƴan ajin suka bada attention ɗinsu gareshi, ciki kuwa hadda Ziyada, wacce ɗigo ɗaya na daga cikin abun da yake koyarwa bata fahimta ba, jinsa kawai take, tana kuma kallon yanda yake solving guestions. Tambaya yayi da sauri wacce ke gefen hagunta, wato Shukhra kenan ta ɗaga hanu, ya ta da ita ta bashi amsa, ƴan ajine suka hau yi mata tafi. Haka dai ya gama yi musu karatun ya fita abunsa. Yana fita baifi da mintuna 5 ba wani Malamin Biology ya kuma shigowa. Tunda malamin yafara darasi'n ta kafe allon da idanu, turanci yakeyi musu cike da ƙwarewa, sannan gaba ɗaya explanation ɗin da yayi musu da turanci yayi su, tunda ya shigo babu wani wanda yayi Hausa haka kuma shima ko A akalmar hausa bai ambata ba, kamar dai yanda wancan malamin maths ɗin yayi haka shima wannan ɗin, hakanne ma yasa sam bata fahimtan komai, domin kuwa turanci zalla suke basa ko ɗan surkawa da yaren da zata gane wato Hausa, lokacin da taga kowa ya ciro littafinsa yana rubutu itama sai ta buɗe jakarta wanda Teacher Abdallah ya bata, bayan littatafai dake cikin jakan hadda wasu tarin kayan snacks. Wani littafi ta ciro haɗe da pen. Dayake Teacher Abdallah ya ɗan koya mata rubutu a lesson ɗin da sukayi, hakan yasa rubutun bai wani bata wahala ba, sai dai kuma bata wani ƙware sosai ba. Gani tayi shima kafun ya fita saida yayiwa ƴan ajin tambayoyi, amma inda Allah Ya taimaketa ita bai tambayeta ba, kuma ko dama ya tambayeta saidai ta bashi amsar shiru. Yana fita wani malamin yakuma shigowa shima dai yaɗan jima yana musu darasi kafun ya fita. Yana fita aka buga ƙararrawan fita break, gani tayi da ɗai ɗai ɗaliban ajin ke ficewa zuwa waje, Shukra ce ta miƙe tafice daga cikin ajin.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now