Chapter 41

13.1K 1K 133
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

             *SOORAJ !!!*

     *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

               *WATTPAD*
         @fatymasardauna
#romance

               *Chapter 41*

Ahankali ya zuro da ƙafafunsa ƙasa,  tare da rumtse idanunsa wanda suka kaɗa sukai ja tamkar waƴanda aka watsawa garin barkono,  hannayensa ya sanya ya dafe kansa dake barazanan tarwatsewa, wani iri yakeji acikin kansa tamkar ana doka masa gudu ma, cikin ƙarfin halin daya aro ya dasawa kansa ya miƙe tsaye tare da soma binbango yana neman hanyar da zai sadasa da toilet,  zuwa yanzu ko gani sosai baya iyawa,  wani irin duhu ne ke neman mamaye ganinsa, sunan Allah Yashiga ambata acikin ransa yana me tafiya ahankali,  ƙafafunsa  ne sukayi masa nauyi, haka yakeji  tamkar an ɗaure masa su da kaca,  aninayen dake jere reras agaban rigarsa ya soma cirewa, tare da sanya hannunsa  ya kunna shower take ruwa yasoma zuba ajikinsa, duka hannayensa ya sanya ya dafe bango tare da rumtse kyawawan idanunsa, yayinda ruwa ke dukan naked skin ɗinsa, still ambaton Allah Yaketayi acikin ransa, ahankali yakejin nutsuwar daya rasa na dawo masa, yayinda yaji gaba ɗaya jikinsa yayi weak, zuciyarsa kuwa har yanzu fast fast haka take bugawa, sake lumshe idanunsa yayi tare da ɗan cizan laɓɓansa,  ko ka ɗan bayason tuno mafarkin da yayi wanda tunda yake bai taɓayin makamancin irin saba,  bayan hannunsa yasa yaɗan naushi bango tare da kashe shower'n, wani white towel ya ɗaura akan waist ɗinsa tare da ɗaukan wani ɗan ƙaramin towel yashiga goge jiƙaƙƙiyar suman kansa,  koda ya fito daga toilet ɗin, zama yayi akan dressing mirror tare da ɗaukan body lotion  ya shiga shafawa jikinsa,  yana gamawa ya feshe jikinsa da wani irin body spray me daɗin ƙamshi,  black pencil crazy jeans and white t-shirt ya sanya, kasancewar anyi ruwa sannan akwai sanyi sosai agarin yasanya shi ɗaura black leda jacket akan rigan,  wayoyinsa ƙiran Samsung galaxy  S20 da kuma iphone 11 pro max ya zura acikin aljihun jacket ɗin nasa, wasu irin combat shoe yasanya masu kyau da tsada, ahankali ya ƙarasa gaban mirror tare da ɗaukan facing cap white colour ya sanya akansa, baƙaramin kyau shigan yayi masa ba, yayinda sajen dake kwance akan fuskarsa keta shinning.  Farfumed ya fesa ajikinsa kana ya nufi hanyar fita daga ɗakin, ahankali yake sauƙowa daga kan haɗaɗɗen matattakalan da zai sadasa  da wani katafaren falo wanda yagaji da haɗuwa,  yana ƙarasowa cikin falon yanufi wajen wani haɗaɗen fridge wanda yake na glass, gaba ɗaya kana iya hango duk wani abu dake ciki, buɗe fridge ɗin yayi tare da zaro gwangwanin malt, ɓalle murfin yayi tare da kai bakinsa jikin gwangwanin,  8 minute kacal ya shanye gaba ɗaya malt ɗin, tare da wurga gwangwanin cikin dustbin. Cikin takun dake nuna tsantsar aji da kuma nuna cikakken zarransa na ɗa namiji, ya fito daga cikin ƙawataccen hotel ɗin, wanda anan yake da zama tunda yazo Singapore, hotel ne mai kyaun gaske don yana ɗaya daga cikin manyan hotels ɗin da akeji dasu a ƙasar Singapore,  tafiya yake da ƙafafunsa yayinda yashiga cikin  ƴan ƙasar yasaje dasu sak, kasancewar kalan fatarsu iri ɗayane danasa yasanya bazaka iya banbanceshi da suba, babu wani ɗaya acikinsu da zaice ya ɗarasa hasken fata,  wani ƙaton club yanufa inda maza masu aji ke zuwa, kowa dake cikin club ɗin harkan gabansa yake babu ruwan kowa da kowa, wasu suna shaƙatawane da ƴan matansu yayinda wasu keshan wine, wasu kuwa rawa kawai sukeyi,  kan wata kujera da take ita kaɗai ya zauna tare da zaro wayansa don yanaso yayi vedio call da Mas'oud,  ɗaya daga cikin masu aiki a club ɗinne ya tambayashi tsakanin Alcohol da wine wanne yake da buƙata. kansa ya girgiza tare da cewa ya basa drinks kawai, hakan kuwa akayi inda ma aikacin ya cika masa gabansa da drinks kala kala, nan ya maida hankalinsa ga wayarsa tare da dannawa Mas'oud ƙira.
         Nigeria
Kasancewar Yau asabar babu makaranta hakan yasa bata tashi da wuri ba sai wajen 9, kasancewar yanzu sam bata aikin gidan Oummu ta ɗebi wadatattun ma'aikata wanda sukeyin girki da komai, fitowanta a wanka kenan zama tayi agaban mirror tare da shafa mai ajikinta, sama sama ta shafa powder akan fuskarta tare da ɗan goga man baki abakinta,  wata doguwar riga na black lace ta sanya, sosai rigan tayi mata kyau,  tsayawa tayi tana me kallon kanta a madubi,  ita kanta tasan tayi wata ƴar rama wanda bakowane zai gane hakan ba har sai  in wanda ya lura,  tana ƙoƙarin ɗaura ɗankwali  ne aka turo ƙofar ɗakin nata, murmushi ne ya bayyana akan fuskarta cikin yanayi na girmamawa tace "Barka da safiya Oummu!"

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now