Chapter 20

11.8K 1K 90
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

             *SOORAJ !!!*

  *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

             *WATTPAD*
        @fatymasardauna

#romance

           *Chapter 20*

Numfashinta ne yasoma ƙoƙarin ƙwacewa, saboda tsabar tsananin tsoron da ta samu kanta aciki, ƙasa tayi da idanunta, tana me kallon hanun da aka rufe mata bakinta dashi, hanun namiji ta gani, wanda ke ɗauke da kwantattun gargasa da sukayi luf akan farar fatarsa,  jikinta ne ya ɗauki tsuma, wani irin tsoro mai ƙarfi ya ziyarceta,   wani ɗan corridor dake cikin kitchine ɗin ya shiga da ita,  ɗan sassauta riƙon da yayi mata yayi, ba tare da ya sake mata bakinta ba, ya juyo da ita suka zama suna fuskantar juna,   idanunta ta zaro waje tana me sake kallonsa.  Sake mata bakinta yayi, tare da ɗaura hanunsa akan laɓɓansa cikin ƙasa ƙasa da murya yace.
"Shiii!! kada kimin ihu, ina da baƙi a falo ki zauna anan kada ki fito"  yana gama faɗan haka ya saketa,  tare da juyawa ya nufi hanyar fita daga cikin kitchine ɗin,  bakinta a wangale haka ta bisa da kallo har ya fice, wata irin ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauƙe, tare da jingina bayanta da jikin bango, har acikin zuciyarta tayi bala'in tsorata, duk atunaninta wanine daban yazo saceta,  hanunta ta ɗaura adaidai kan chest ɗinta dake ta bugawa da ƙarfi, aƙalla takusan mintuna 9 ahaka, kafun tasamu ta iya daidaita nutsuwarta, kan wani plastic chair dake cikin kitchine ɗin ta zauna,  tare da kifa kanta akan cinyoyinta. 

Shikuwa Sooraj yana barin kitchine ɗin, komawa cikin falo yayi, wajen  abokan business ɗinsa, da suka kawo masa Ziyara, yana zaunene amma gaba ɗaya hankalinsa naga ƙofar kitchine, sam  bayaso tayi gangancin fitowa,  ba tsoronsa ganinta da zasuyiba, tsoronsa shine wani irin bahagon kallo za suyi masa?  tabbas ba lallai suyi mishi kyakkyawan zato ba, shikuwa ko kaɗan bayason ayi masa irin wannan kallon.  Sunjima suna tattaunawa akan business ɗinsu, kafun daga bisani sukayi masa sallama, har bakin motarsu ya rakasu, shima daga rakiyarsu bai dawo cikin gidanba, motarsa ya shiga ya fice daga gidan gaba ɗaya.

Jin anata ƙiraye ƙirayen sallan ne yasata takowa saɗaf saɗaf taɗan leƙa cikin falon,  ganin ba kowa acikin falon yasa ta sauƙe ajiyar zuciya. Fitowa daga cikin kitchine ɗin tayi ta wuce ɗakinta. 

*MONDAY*

Yau yakasance ranar da zasu fara exam, 8:00 am daidai zasu shiga exam ɗin inda zasu fara da Biology.   Zaune suke akan wani bench su dukansu ukun,   kallon Shukra da Nasmah Ziyada tayi murya asanyaye tace.
"Tun safe ƙirjina yaketa bugawa, wani irin tsoro nakeji, anya zan iya zana exam ɗinnan kuwa?"

Kallonta Shukra tayi tare da ɗanyin murmushi.
"Zaki iya mana, ki daure ki ƙarawa kanki confidence, amma ai babu wani wahala"   Shukra tace haka cikin son ƙarawa Ziyada ƙarfin guiwa, shiru sukayi daganan basu sake cewa komai ba.   Takwas na cika dai dai suka shiga jarabawa, 1 hour suka ɗauka suna rubuta exam ɗin, cike da jin daɗi  Ziyada ta miƙa booklet ɗinta,  sannan tafito daga cikin exams hall ɗin, tsayawa tayi ajikin wata bishiya tare da lumshe kyawawan idanunta, wani nishaɗi takeji acikin ranta saboda tana da yaƙinin cewa zata ci duka tambayoyin da ta amsa.  Su Nasmah ne suka fito nan suka haɗe suka ci gada da hiransu,   kasancewar yau paper biu zasuyi  ƙarfe 10 daidai suka sake shiga wata jarabawan na Islamic.  Suna kammala jarabawan  kowa ya fara haramar komawa gida, tsayawa tayi tare da dafe goshinta,  gaba ɗaya ta manta batace da Kamalu driver yazo ɗaukarta da wuri ba,  gashi yanzu sun gama exam kowa na ƙoƙarin ko mawa gida.   Kai tsaye ta nufi babban ƙofar gate ɗin makarantar.   Tana fita daga cikin gate ɗin ta soma kalle kalle, batasan ya zatayi ba don bata da wata mafita, gashi su Shukra sun tafi.  Wata baƙar motace tazo ta tsaya agabanta, hakan yasa ta ɗan ja baya.   Ahankali ya sauƙe glass ɗin windo'wn motar,  kyakkyawar fuskarsa ta bayyana wacce ke ɗauke da murmushi.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now