chapter 1

3K 128 1
                                    


I most read 🏃🏃🏃🏃🏃🏃

*DUK A SANADIN
SOYAYA*

~ By safnah aliyu jawabi*
(Jawabi)

Bismillahi rahamanin Rahim





Zaune yake cikin office dinsa saman table dinsa kuwa ciki take da takardu aiki yake Amma kamar ba zasu kare ba, Dan tsaki yaja sannan ya dauko robar ruwan dake gefen shi yasha rike kanshi yayi Dan bakaramar ciwo take masa ba,karar bude kofar da yaji,hakan baisa ya dago ba Dan yasan duk duniya mutum daya ne yake shiga office dinsa Kai tsaye.

Shiru sukayi nadan mintina sannan yadago Kai ya kalle shi yadanyi murmushi sannna yace"wannan Kuma kowa yataba shi yazo zai sauke akaina oho, afili Kuma yace" kazauna Mana abok... tsawar da ya daka Masa shiya hanashi karasa maganar yanuna shi da hannun Yana cewa"

karka kara kirana da abokin ka,bazan taba kasancewa aboki ga maci Amana ba,bana fatan kasancewa aboki ga Mai tsansar butulci,bana fatan kasancewa aboki ga mutumin da yake mance alkairai,
Nakasa yarda wai yau Kaine kake juyawa AISHA~LABBEBAH baya,bayan Duk alkairan ta agare k...

Shidinma tsawa yadaka Masa cikin bacin Rai Dan sosai maganar shi ta mugun Bata mishi Rai idon sa kuwa harta sauya saboda tsananin bacin rai yace,"kasani sadiq duk duniya Kai ne mutum na farko da zaka'iya duban fuskata kafadamin duk abinda kake so batare da na nuna maka matsayi na ba.

kasancewar ka aminina tun yaranta,Amma Kuma kasani hakan bawai Yana nufin baka damar fadan duk abinda yazo bakinka bane.

Sannan zancan AISHA~LABIBBAH kasan cewa naso aisha kai shidane akan haka,tabbas aisha tayimin abubuwa dayawa duk A SANADIN Soyaya Kuma inaso kasaka aranka har duniya ta tashi bazan taba mancewa da aisha ba Kuma nafada mata ba sau daya ba basau biyu ba duk lokacin da take niman wani taimako ta nemeni Zan Mata ko wani iri ne,zancan aure na da itah ne babu bazan iyah auran taba get that in to har heard.

yakare ke maganar da buga hannun shi saman table dinsa karar saidai ta firgita sadiq,cike da ma'maki yake kallon shi sannan yace,"kamar yanda kace bazaka iyah auran AISHA ba Raihan Haka Nima bazan'iya yin abota da kaiba sannan zancan idan tana niman taimako zaka taimaka mata to mun gode 🙏🙏bama bukata,sannan ka rubuta ka ije wallahi saikayi nadamar abinda ka aikata asannan Kuma lokaci ya kure maka sai wani lokaci.

Yana kaiwa daidai Nan yasa Kai yafita.

Rikicewa iya rikicewa Raihan yayi dasauri yabi bayan sadiq Yana Kiran shi Amma Ina tuni haryaja motar sa yabar harabar company din.shiru Raihan yayi sannan yakoma yadaiko key din motar sa shima yafita daga company din.bai tsaya ko inah ba sai kofar gidan su AISHA Yana zuwa saukowa yayi daga motar yashiga gidan kasan cewar yasan itah kadaice take rayuwa acikin gida Yana shiga ya kwalla mata kira.

Cikin sauri ta fito Dan ko amafarki taji wannan muryar to babu shakka tasan ma'mallakin ta,tana fitowa yabita da kallon uku saura kwata yace,"ki yanzu Aisha sai yaushe Zaki San (annabi)ya fako?saiyaushi Zaki gani cewan Raihan dinda kika sani daban Dana yanzu?sai yaushe Zaki gane cewan nafi karfin ki?sai yaushe Zaki San cewa inda Yan aiki na suke kwana yafinan sau dari?yafadi haka tare da nuna gidan.

To bara kiji Abu na karshi dazan kara jaddada Miki shine babu Ni babu ke kidauka baki taba ganin Raihan ba Kai bakima tabajin maikalar sunan ba ,sannan kinyi nasarar rabanida aminina sadiq Amma kisani saina kuntata rayuwar ki saina hukuntaki.

Yana kaiwa Nan yajuya Yana rufe hanci alamar wari yakeji agidan duk da kamshin turaran wuta dake tashi acikin gidan cikin saure Tasha gaban shi tana kuka tsananin kuka duk idonta sun kumbura da alamu ta dade tana aikin kukan tace"Dan ALLAH Raihan karkamin haka karka manta da alkawarin da muka daukar wa juna,yanzu harzaka iyah mancewa da labibar ka?nicefa labibar raiha...

Saukar marin da tajine yahanata karasa maganar cike da mamaki take binshi da kallo Wai yau itace Raihan muradin zuciyar ta yamara.

Cikin daga murya yanuna ta Yana cewa,"inah Mai tabbatar miki duk Randa kika sake hada kazamar sunan ki danawa wallahi saina mugun Saba miki,cikin bacin Rai yasakai yafita daga gidan.

Itah kuwa sugunnawa tayi agurin tana kuka Saida tayi Mai isarta sannan ta tashi ta shiga ciki jiri na diban ta.

****
Shikuwa sadiq Yana fita gidan shi yanufa Yana zuwa yazauna Yana tunanin butulci irin na Dan Adam Dan shidai ko amafarki aka fada mishi cewa Raihan zaijuyawa Aisha baya to babu shakka zaice a a,Amma saigashe yau ba mafarki yake ba Amma hakan na faruwa,tashi yayi ya fara safa da marwa Dan samarwa kanshi mafita,Haka dai yadauki kusan Rabin awa Yana Abu daya saidaga baya yadauki makullin motar sa yafita.

Yana fita bainufi ko inah ba sai gidan su AISHA Yana zuwa shima yashiga da sallama ya shiga gidan jin anyi shiru ba'a amsa ba yasa yadan tsaya Dan baisan awani yanayi zaiganta ba jin shirun yayi yawa yasa shi karasawa da sauri saidai mezaigani🙄

Thanks alot friends inah alfahari daku domin kunkasance kuna bibiyar Al"amarina ,to inah fata Zaku karbi wannan sabon liltafinin nawa da hannu bibbiyu.love you all 🖤🖤🖤🖤

DUK A SANADIN SOYAYAWhere stories live. Discover now