chapter 26

467 38 8
                                    


Duk asanadin soyaya

By

SAFNAH ALIYU JAWABI

Bismillahi rahamanin rahim

Da kuka tashiga gida da sauri sha'awa wacce yanzu take zaman zawarci gidan su tatare ilham cike da nuna tausayawa tace, "Yi hakuri ba kuka zaki yiba wallahi ďaura ďamarar yaki zakiyi Don kwatarwa kanki yanci yarinya.

Cikin kuka tace, "Toni Ya zanyi kindai san babu abinda banyi ba danganin tabar gidan amma gabaki ďaya abin ya faskara saima guzurin cike da take da.

Shiru sha'awa tayi can tace, "Nasamu mana mafita saidai bansani ba ko zaki iya.

Bakinta har rawa yake tace, "wallahi kuwa zan iya sha'awa ki gaggauta faďamin, kinji Dan ALLAH.

"Na farko dole saikin San yanda akayi kika samu ciki cikin kankanin lokaci, bayan haka zanbaki wani magani saiki zuba mata acikin Abin SHA, cikin zaizube kinga kenan naki ďan zairiga nata fitowa duniya idan matakuma samun wani kenan, koya kika gani?

"to gaskiya shawarar ki tayi saidai kisani bafa kullum Y'a sadiq yake nuna bukatar sa akaina ba,idan kuma na nuna mai share zancan yake ko kuma yace, "yawan sex yana kawo mutuwar jiki da sauri,toda hakan zancan zaibi ruwa.

Murmushin mugunta sha'awa tayi tace, "to basai ki nime wani yayi miki ba ya'isa yace banashi bane?

Gabaki ďaya jin ilham ya ďake zufa kawai take jin abinda sha'awa tace ,da mamaki take kallon ta tace kina nufin nayi zina da Aure na? Hmm haba haba ina bazan iya ba.

"To shikenan naga dama bani Nakira kiba, kekizo da kafarki ,Don haka idan kina ganin shawarar dana baki baiyi ba saiki nima wata,nikam iya inda nasan zan iya taimaka miki kenan

Murmushi tayi ta ďauki Jakarta tace, "Karki damu shawarar ki tana kan hanya zankira ki awaya saimu tsara yanda Abin zaikasance, kinga baima San nafita ba karya dawo baiganni ba, cikin sauri tafita daga gidan.

Sha'awa kuwa Dariya tasaki harda rike ciki tace, "hmmm lailai ilham baki sanni ba, wallahi tun daga Randa nayi ido hudu da sadiq naji duk duniya babu namiji daya dace Dani sama dashi, kuma naďauki alwashin kawar dake nashiga kuma nazauna da uwar gidan sa lafiya, Dan nagane Hakan kawai shine mafita Dani kike zancan.

*******

Wasa wasa lamarin raihan yayi nisa takai duk tarin dayayi sai gudan jini yafaďo, gabaki ďaya yarame saidai duk yanda yake jin jikin hakan baisa yafaďawa Inna sadiya ba, haka kuma bandaina tunanin labiba ba.

Ranar da jikin ya motsa sosai saida aka dangana da asibiti badan ransa yaso hakan ba ganin babu yanda ya iya yasa kawai ya hakura.

Sosai Dr yake masa faďa lokacin da aka samu yadawo daidai, kallon Dr yayi hawaye nagangara yace, "Dr babu bukatar shan magani ko kuma daina tunani domin kuwa itace komai nawa, itace duniya ta kaga kuwa daina tunanin ta tamkar barin duniyar ne gabaki ďayan ta.

Gyara zaman glass ďinsa Dr yayi yace, "wacece ita?

Shiru yayi can yashiga bashi labarin labiba, Dr ya tausaya masa sosai yace, "tabbas raihan kayi kuskure saidai kasani ba laifin kabane haka ALLAH ya hukunta bakada tsime baka da dabara dole sai hakan tafaru, kayi tawakkali IN SHA ALLAH komai zai wuce.

DUK A SANADIN SOYAYADonde viven las historias. Descúbrelo ahora