chapter 7

475 56 1
                                    

#duk asanadin soyaya #

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺writing by SAFNAH ALIYU
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺JAWABI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺BRIGTESS hope writers association
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺duk asanadin soyaya
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Bismillahi rahamanin rahim


Da gudunta tabar gidan,kallon kallo suka tsaya suna wa juna kafin Daga bisani suka shige ďaki,har zuwa lokacin babu Wanda yayi wa ďan uwansa magana,cikin dakiya Sadiq yake tambayar raihan abinda yafaru.


Ganin bashida wata sauran dabara yasa ya zaiyana masa duk abinda ke faruwa harda ďaukar dawainiyar karatunsa da labiba take.


Sosai ya tausaya wa labiba rashin iyayanta da tayi nandanan yaji sonta da kaunarta na kara ruruwa acikin zuciyar sa.


Tashi sukayi suka tafi gidan dan bata hakuri amma Sam labiba ta kenkeshi ido tace, "baxata fito ba,haka Suka hakura suka tafi, ranar haka zukatan mutum uku suka kasance cikin kuncin rashin ganin walwalar ďaya ďaga cikin su .


Garin ALLAH na wayewa labiba ta kunsa kuďin da zatayi register makaranta ta aikawa raihan dasu,haďe da gargadin karya dawo dasu,lokacin da yaga kuďin farin cikin abu biyu yayi, na farko zaibiya kuďin project dinda zasuyi, na biyu kuma yasan ta sauko kenan tunda gashi harta aiko masa da sako.


Lokacin da raihan yanunawa Sadiq kuďin data bashi sosai yayi mamaki, amma dai yayi shiru dan bayason yana musu shishigi acikin Al'amuran su.

Bayan suntashi ďaga makaranta suka nufi gidan su labiba suna zuwa akace musu tafita,tambayar yaron yayi inda tatafi,"nima bansani ba amma cewa akayi Mai anguwa yake kiranta.


Jan hannun Sadiq yayi suka nufi gidan Mai anguwa,suna zuwa suka tarar da labiba zaune agaban Mai anguwa sai share hawaye take, cikin sauri suka karasa gunta,tambayar ta abinda ke faruwa raihan yayi .


Aitana ganin sa taji zuciyar ta takarye cikin kuka tace, "ya raihan kaji wai wannan gonar ta baba,waiwasu mutane sunzo sunce tasuce,kawai sun baiwa baba amanarta ne kafin suje sudawo kasancewarsu 'yan Gabon.


Kallon Mai anguwa yayi ya bukaci jin komai abakinsa,abinda ta faďa dai shine Mai anguwa yakara nanata masa.


Wani irin gumene yaji tana saukar Mai lokacin daya tunawa dayayi kuďin da labiba ta t
Bashi,tafaďa masa cewa kuďin Rabin gonar ta tsayar,to yanzo ina zasu samu kuďi subiya su.


Maganar maigari ce tadawo dashi cikin haiyacin sa,yace,"to labiba kindai San kinzo kin bukaci asayar miki da Rabin gonar ko?babu musu naďauki kuďi na baki,to yanzu yaya zamuyi da masu gonar kasancewar ansiyar musu da Rabin gona.


Ďago Kai tayi hawaye na zarya tace, "duk yanda kace haka za'ayi.

Murmushi Mai anguwa yayi yace, "shikenan zamu duba gidan da kike ciki idan takai yawan kuďinsu saimu sayar dashi, idan kuma yafi saimu San yanda za'ayi.

DUK A SANADIN SOYAYAWhere stories live. Discover now