chapter 14

423 49 1
                                    

❄❄❄❄❄❄❄
       *DUK A SANADIN SOYAYYA*
                               ❄❄❄❄❄❄❄

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERIN OUR READERS_ 💪)

https://www.facebook.com/100452275039839/photos/a.100452311706502/100452611706472/?type=3

          *P.W.A*✍️

1⃣4⃣

*STORY*

*&*

*WRITING*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

_Kaima ban barka abaya ba mu'az domin kuwa kaima ka taka rawar gani, SAFNAH ALIYU JAWABI bazata taɓa mance halalcin ku agare taba,  ina mattuƙar godiya_


,,,, Cike da mamaki duk suke binsa da kallo ,ɗago hannun sa yayi da niyyar Kara Marin sa, cikin zafin nama mummy tayi saurin riko hannun sa, batayi wata wata ba ta ɗaga hannu ta zabga masa mari,rike da kuncinsa yayi yana kallon ta,nuna shi da hannu tayi tace, "lailai kacika Mara kunya har gida,kuma agabana ba labari ba?  agabana ka ɗaga hannu ka mari ɗana?

,"lailai ka tafka babban kuskuri, amma kaci darajar abu ɗaya shiyasa bazansa ayi min kasa kasa da kaiba,dan haka kafin na rufe ido nabuɗe ka fitar min daga gida.

Murmushi Raihan yayi yace, "Nagode saidai ki Sani kema kinci darajar abu ɗaya shiyasa bazan rama Marin da kika yimin ba, amma inaso ki Sani idan kikaga na fita daga gidan nan  tofa kafata kafar aisha.

Labiba kuwa kamar dama Jira take yakai aya, wani irin tafiyar takama take Wanda ita kanta batasan ta iya ba harta karaso inda yake ťsaye tace, "waye Kai? Wacce aisha Kake nima a gidannan?badai ni aishar bako?

Baki sake raihan ke kallon labiba Dan wani irin mugun mamakin ta dayaji, ,gyara tsayuwar sa yayi yace, "ke aishar nake nima, aishar Raiha.

Wani irin tsawa ta daka masa tace, "Kai  Karna kara ji Karna gani, ko amafarki bana kaunar sake jin sunana abakin ka, bansan kaba,bansan daga wacce duniya Kake ba raihan Kake kowa? ina Mai sake gargadin ka daka fita daga rayuwa ta,bana bukatar ka ayanzu, Kai harma karshan rayuwa ta,kuka ne Mai karfi yaci karfin ta lokacin da tasake kallon kwayar idonsa ta tuna raihan ɗinta fa take gaya masa wannan munanan kalaman.

Cikin muryar kuka tace ,"Mena maka raihan?wani laifin na aikata maka wanda bazaka iya gafarta minba? kabarni nayi rayuwa Mai inganci, sai yaushe zaka daina rusa farin cikin rayuwa ta?ɗan wanna farin ciki da nake ciki ayu MA bazaka bari nayita cikin kwanciya hankali ba?

Bata tsaya jin abinda zai faɗa ba tayi cikin gidan da gudu batare da ita kanta tasan inda ta nufa ba.

Gabaki ɗaya raihan kasa ɗauke idonsa daga kanta yayi harta shige cikin gidan, cikin isa da takama sadiq ya karaso gunsa yace, "alokacin da kaɗaga hannu kamare ni, shin kasan dalilin daya sa banrama ba? Saboda bansan matsayin ka a zuciyar labiba ba haryanzu, amma yanzu naji daga bakin ta,  wanda hakan yakara min kaimi gun nuna maka iyakar ka raihan, sannan ina maka albishir da labiba ta kubce maka kenan har abadan,batare daya tsaya jin amsar Saba yaja hannun mum sukayi cikin gida.

Wani irin abu raihan yaji ya tokare masa makoshi, cikin kunan rai yashiga wancakali da duk kayan dake gurin, saida ya tabbatar babu wani sauran Abin amfani agurin sannan ya nufi gun motar sa wacce tsabar masifa da kishin labiba da yaji lokacin daya hangi sadiq rike da hannun ta, yabarta abuɗe.

Da gudu yabar harabar gidan.

****

Suna shiga ciki suka tarar da labiba kwance asaman two siter sai zabga kuka take kamar wacce aka aikuwa sakon mutuwa,da gudu Hafsah  ta isa gunta, ďagota Hafsah  tayi ta shiga share mata hawaye Tana cewa, "kiyi hakuri sis ki daina kuka Kar kanki yayi ciwo kinji,nayi miki alkawari saina Zane raihan idan Yakuma zuwa gidan nan.

Dariya ne yakubcewa labiba ganin yanda hafsah keson mayar da kanta karamar yarinya.

Murmushi mum tayi tanufi gunta, kwantar da kanta kan cinyar ta tayi tace ,"ki daina kuka aisha komai ya faru da Bawa kisani mu kaddari ne daga ALLAH, Dan haka ki cire damuwar raihan aranki, IN SHA ALLAH Idan ke rabun sane sai kiga kun shirya komai ya koma kamar da, wani irin dam kirjin sadiq yabada jin abinda mum take faďa.

Ita kuwa labiba cikin sauri ta miki zaune, rike hannun mummy tayi tace, "ki Sani tamkar uwa kike aguna Dan haka inada yakinin duk addu'ar da kikayi min tana iya kamani,ki min rai Karki roki ALLAH dawowar raihan cikin rayuwa ta, domin tuni na shafe babinsa daga ciki.

Wani irin ajiyar zuciya sadiq yasake wanda duk kansu saida suka jiyo saukar ta, cikin sauri mummy takai duban ta gunsa, sauke idonsa kasa yayi dan ganin irin hararar da mummy take aika masa.

Sake riko hannun labiba tayi tace, "shikenan kici gabada addu'ar ALLAH yazaɓa miki abinda yafi Zama alkairi, cikin sauri sadiq ya amsa da Ameen, janyo falon dake gefenta mummy tayi ta jefeshi da ita.

Dariya duk kansu sukayi sannan suka cigaba da hirar raihan .

*****
Hon yake kamar zai cire kunnan mutane tsabar kara,da guda Mai gadi Ya wangale masa get,ko tsayawa mai gadi yakarasa buɗe wa baiyi ba, Ya cusa hancin motar sa.

Buɗe kofar falon yayi da karfi saida zakkiya da ƙawayan ta duk suka razana,kallon mamaki duk suke binsa dashi ganin yanda yayi kamar MA bai gansu ba yashigewar sa ciki, sosai yanda ya disgata agaban kawayan ta da take yiwa kurin yana mattukar sonta Ya Sosa mata zuciya Dan haka itama cikin fushi ta tashi ta bishi.

Sukuwa suna ganin ta shige duk suka fashe da Dariya.

Cikin ɗaga murya ta kira sunansa ,"raihan wannan wani irin walakanci ne zaka disgani agaban ƙawaye na?

Banza yayi da ita kamar baisan ALLAH yayi ruwan taba, ganin yana niman Raina mata class yasa taja tsaki tace, "dama shi ɗan talaka kowani irin arziki yayi saiya nuna halinsa, juyawa tayi da niyyar fita daga ɗakin taji anjanyo ta, wani irin gigitatciyar mari taji akuncin ta wanda saida ta rasa ganin ta na wucan gadi.

Nunata yayi yace, "wallahi kikayi kuskuran sake gayan magana wallahi saina Yi maganin ki banza Mara tarbiya.

Da mamaki take kallon sa, tace, "wallahi tunda kamare ni wallahi sainayi maganin ka, sai kayi dana Sanin sani na arayuwa banza kawai, da gudu tabar ɗakin ganin yasake kusanto ta.

Tsaki yayi ya rufe kofar sa, komawa yayi ya kwanta wasu zafafan hawaye suka shiga sauka  kuncin sa, banda dana Sani babu abinda yake, Shidai yasan Sam baiyi sa'ar uwa ba, Dan kuwa duk asanadin ta wannan Abin yake faruwa....

Please manege  love you all

DUK A SANADIN SOYAYAWhere stories live. Discover now