chapter 8

476 45 3
                                    

#duk asanadin soyaya #
💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕
💕💕💕💕
💕💕💕
💕💕
💕SAFNAH ALIYU JAWABI

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺🌺
🌺BRIGTESS hope writers association

Bismillahi rahamanin rahim

Farin ciki sosai sadiq yayi lokacin da raihan ya faďa masa batun aikin.
Ranar da zaitafi gun alhaji Mustafa bello algaita,shirinsa Mai kyau yayi labiba harda masa rakiya dan tuni suka shirya.

Lokacin daya isa company nin sosai yayi mamaki ganin girman company,yana shiga kuwa cikin girmamawa aka karbe shi,da farin ciki ya iyaso gida,ranar Inna sadiya harda rawa tsabar murna.

Cikin ikon ALLAH sadiq ma a company ya samu aiki cikin nasara suka fara aiki, kasan cewar su hazukai haďi da tsansar ilimi hakan yasa sukayi ta samun karin girma.

Lokacin da inna sadiya taga raihan yataka mukamin da take fatan ganin ya taka, tuni ta fara hure masa kunne,tun yana basar wa harya fara ďauka,akullum takan Cemasa ,"yaron nan inaso kabuďe idanuwan ka kasani yanzu kafin karfi wata labiba, kaduba yawan matan dasuke zuwa gidannan danyin kamun kafa dani, kyau, Sura, duk babu wacce labiba ta taka kafarta,dan haka tun wuri ka faďa mata ta nime inda dare yayi mata.

Labiba kuwa kullum idan tayiwa raihan zancan auran su saiya ce, "haba saurin mekike,nifa nake ne RAI'ISH nakine mallakar ki, da haka yake samu yarufe mata baki, yaudai tagaji da abinda raihan yake mata Dan yanzu sai yayi sati bai zo gunta ba.

Ďaukar wayar daya saya mata tayi takira Sadiq, daidai lokacin suna tare da raihan, da murmushi ya Kalli raihan yace, "RAI'ISH dinka ce Kekira fa"shareshi raihan yayi kamar baiji abinda yake faďa ba, ganin wayar Tana niman yankewa yasa yayi sauri ya ďauka,da sallama ta fara, sosai muryar ta yadaki kirjinsa lumshe ido yayi sannan ya amsa, gaisuwa sukayi sannan yace, "RAI'ISH yanaji muryar ki kamar baki da lafiya?

Cikin sauri tace, "a a ya Sadiq lafiya ta kalau, kawai dai dama sonake muyi wata magana dakai bansani ba ko kanada lokaci?

,"Eh yanzu dai aiki nake amma IN SHA ALLAH idan Natashi zanbiya ta gidan ku, duk maganar da yake idanuwan sa alumshe take shiyasa bansan lokacin da raihan yafita ba,da mamaki yake kiran sunan raihan amma shiru babu shi babu labarin sa.

Labiba kuwa fashewa da kuka tayi dan sosai halin raihan yake damun ta,bayan sallar isha kuwa saiga Sadiq, da farin ciki ta tarbe shi, lokacin data faďa masa halinda ake ciki game da raihan sosai Abin yabashi mamaki dan shi shaidane kan irin soyayar dake tsakanin labiba da raihan.

Sallama yayi mata da alkawarin zaiyi masa magana.

Washa gari yana zaune a office dinsa saiga raihan yashigo hannun sa sarke dana wata yarinya wacce kallo ďaya zakayi mata kaji kana da bukatar amai, duk jikinta Tasha Blechin ga wani gashin doki data Kara gashin ta, janbaki kuwa kamar wata maiya, gajeruwa ce saidai bacan ba,gata ga kananun ido Kai bata da wani tsari.

Mikawa Sadiq hannun tayi tace, "Hy am zakkiya.

Wani irin kallo ya watsa mata wanda saida tayi saurin janye hannun ta, kallon raihan yayi yace, "wannan fa?

Murmushi raihan yayi yace, "zakkiya sunan ta matar da zan aura kenan, cikin fusata Sadiq ya miki yace, "wasa Kake ko raihan?

Murtuke Fuska raihan yayi dan dama ďaurawa kawai yake da irin walakancin da sadiq yake masa akan wata labiba yace,"nataba yin makamanciyar wannan wasa da kaine"wani irin Dariya Sadiq ya kece dashi harda dukan table din dake gaban sa, ganin yanda sadiq ya mayar dasu mahaukata hakan yasa raihan yaja zakkiya suka fita sai wani nannarkewa ajikin sa take.

Zama Sadiq yayi yama rasa abinda zaiyi, farin ciki zaiyi ko bakin ciki? Shikansa shaida ne kan yanda labiba take mattukar son raihan Dan haka babu wani dalilin dazaisa yayi farin cikin rabuwar su.

Tashi yayi yanufi gida shi kansa yarasa wani yanayi yake ciki.

Ita kuwa labiba ganin kwanaki sai ja suke amma babu labarin raihan,hakan yasa ta yanke hukuncin zuwa gidansu ďanta duba ko lafiya.

Tana zuwa kofar gidan taci Karo da raihan da zakkiya suna fitowa ďaga cikin gidan,tsayawa sukayi suna kallon juna ďaga bisani raihan yaja tsaki ya ja zakkiya zasu wuce, cikin sauri labiba tasha gabansa da mamaki take kallon sa tace,"rai'ish baka ganni bane?

Muryar Inna sadiya sukaji ďaga bayan su tana cewa, "idan yaganki sai mee nace sai akayi yaya?

Sunkuyar da Kai labiba tayi tace, "kiyi hakuri Inna,"

Munafukar yarinya sai anyi magana tashiga bada hakuri kamar agidan su aka halaci hakurin, to bara kiji wallahi kuda wasa kika kara tako kafarki cikin gidannan saina Saba miki, yo inbanda abinki wani sakaran namiji ne zai Auri Mai zamar kanta,dago Kai labiba tayi cikin sauri jin abinda Inna sadiya take faďa, matsowa gabanta tayi tace, "kin tsareni da ido koba haka bane?

Nod dakai kawai labiba tayi hawaye na zarya akuncin ta.haka
Tanaji Tana gani suka wuce suka barta anan, zakkiya kuwa harda gwalo tayi mata.

Da gudu labiba ta nufi gida kuka take da iya karfi ta duk inda ta wuce sai ankalle ta,zata shiga gida kenan suka haďu da Mai anguwa tsayar da ita yayi yace, "labiba lafiya make faruwa?

Cikin kuka tace, "baba raihan ne wai bazai Aure niba, tana gama faďan haka ta shige gida da gudu, murmushi Mai anguwa yayi yace, "hmmm dama ance ta yaro kyau take bata karko, na daďe da sanin wannan ranar Tana nan zuwa, shiyasa nayi dabara na karbe komai ahannun ki,sai lokacin daya dace nabaki zan mika miki duk abinda kika mallaka labiba.

Ware ido nayi nace, "lailai Mai anguwan nan akwaika da farin dabara.

Kuka sosai labiba tayi har saida tagode ALLAH,babu irin hakuri da Inna Mairo bata bata ba amma Sam saida tayi ya isheta sannan ta share hawayan ta,kiran Sadiq tayi ta shaida masa abinda ke faruwa sosai Abin yabashi mattukar mamaki dan duk tunanin sa raihan wasa yake.

Dubashi a office yayi akace yafita ,yana fita bai tsaya ko ina ba sai gidan su labiba, yanda yaga fuskarta sosai sadiq ya tausaya mata, hakuri yabata yace karta damu komai zaiyi daidai da yardar ALLAH.

Lokacin da Inna sadiya ta faďawa malam sule maganar zuwa gidan su zakkiya nema masa Aure, sosai malam sule yayi mate faďa kiran raihan yayi dan yaji ko mahaifiyar sa dole tayi masa, saidai buďe baki yayi lokacin da yaji abinda raihan yake faďa masa...

Please
Vote
Comment
Shere
Follow

DUK A SANADIN SOYAYAWhere stories live. Discover now