chapter 16

450 40 1
                                    

DUK A SANADIN SOYAYYA

BY

SAFNAH ALIYU JAWABI

Bismillahi rahamanin rahim

Haka kuwa akayi Washa gari abba yanufi gun mai anguwa, cikin karamcin aka tarbeshi musammam lokacin daya faɗe makkasoɗin zuwan nasa, tiryan tiryan Mai anguwa ya labarta masa iya abinda yasani.

Jin haka kuwa bakaramin faranta ran abba yayi ba, domin babu ɗigon karya alabarin da sadiq yabawa mummyn su.

Da haka suka rabu cikin mutunta juna bayan abba yafaɗa masa kuddirinsa nason Zaman labiba agunsa.

Koda ya koma gida yasanar dasu yanda sukayi da mai anguwa, tsabar farin ciki Hafsah harda taka rawa,dariya sukayi ganin yanda take farin ciki kamar anbata kyautar mota kasancewar abinda take da burin mallaka kenan tun tasowa ta, Sukuwa ganin kankantar ta yasa har yanzu basu bata ba .

Labiba kuwa addu'ar ALLAH yasa haka shiyafi Zama alkairi tayi tashiga ďaki.ilham kuwa rufe kanta tayi kuka iya son ranta ganin babu abinda hakan zai tsinana mata yasa ta hakura ta zubawa sarautar ALLAH ido.

Ďaukar labiba abba yasa sadiq yayi har gida ta ɗauko takardun ta daidai sauran abinda baza'arasa ba suka dawo.

Cikin kankanin lokaci aka sama mata gurbin karatu a kasu kaduna.

******

Zakkiya yace zaune gaban wani kasurgumin kato duk fuskarsa arufe da suma wanda tun daga kansa har gemunsa sumane Mai tsayin gaske, fuskarsa kuwa abar tsoro, cikin tsawa yace, "faɗe duk bukatun ki yarinya kisani bana da lokacin batawa.

Gyara Zama zakiya tayi tace, "Ya boka wanzani kasani inda matsala ne Tsakanina da...

Wani irin gigitatciyar dariyar da yayi Mai kama da fashewar bom shiya firgitar da zakiya Kai harni marubuciyar saida na ije Biro da takarda ta, wangale jajayan idanuwan sa yayi yace,"tabbas Kin kawo kukan ki inda za'a share miki yarinya, daga yau matsalar ki takare, mijinki zai Zama tamkar rakume da akala sai yanda kikayi dashi.

Ďaga hannun sa sama yayi saiga wata farar gora Mai cike da wani bakin ruwa ta baiyana, Mika mata yayi yace, "ki Sani wanna ruwa shizaki zuba masa cikin abincin da zaici, idan harkika samu sa'a yaci tofa ina Mai tabbatar miki babu abinda zai rinka ďauka da mahimmanci samada ke.

Cikin farin ciki zazzkiya tayi godiya haďe da tura hannu cikin jakka ta zaro kuďi Wanda ita kanta batasan adadin suba ta ije masa,tashi tayi da niyyar tafiya taji yana cewa,"tabbas ki kula da ragowar ruwar domin duk ranar data zuba ina Mai tabbatar miki duk wanda ke gurin yana shakar hayakin dake fita daga ciki zaimakance sannan zai nakasa cikin abinda baifi mintina talatin ba.

Tsoro sosai ya baiyana afuskar zazzkiya saidai sanin babu kowa gidan yasa ta amince ta tafi.

*****

Raihan kuwa bayan daya bar gidan su sadiq sosai ya tsinci kansa da nadamar abinda ya aikata GA labiba,domin kuwa gashi abinda ya Raina yana niman tsole masa ido,wani irin ciwon kaine ya dirar masa lokaci ďaya,tunawa da maganar da labiba ta fada masa, adaddafe yashiga gida, baibita kan zazzkiya ba yashige ďakinsa haďe da rufe kofar.

Wanka yayi ko zai ďanji saukin abinda ke damun sa cikin ikon ALLAH kuwa bayan ya fito barci Mai nauyi yayi awan gaba dashi,cikin firgici duk jikin sa gumi Ya tashi da addu'a Ya tashi raďau abakin sa sakamakon wani mummunar mafarki da yayi, Sam Baya MA kaunar tuno abu ďaya daga cikin mafarki.

Mikewa yayi ya ďauro alwala kasancewar anyi sallar La'sa'ar yana barci, idarwar sa tayi daidai da dawowar zazzkiya, sosai ganin sa ya firgita ta Dan batayi tsammanin ganin sa agida awannan lokacin ba,basarwa tayi ta shige ciki, kota kanta baibiba.

Kwafa tayi Tana jin wani irin sanyin daďi aranta ganin zata aiwatar da aikin ta cikin sauri, sanwan abinci ta ďaura nazari tashigayi tana tunanin abinda zata dafa cikin sauri, cuscus ta ďaura cikin mintina kalilan tayi jalof ďin cuscus wanda da taimakon google tayi,wanka tayi ta saka wasu irin fitnanun kaya masu fidda ilahirin surar jikin mutum ,kwance yake yana nazarin mafarki dayayi, sai ganin mutum kawai yayi Akansa tana masa wani irin shu'umim murmushi.

Samun kansa yayi da mayar mata da martani,hakan kuwa bakaramar faranta ranta yayi ba, kwanciya tayi ajikin sa Tana masa tafiyar tsunsu,lumshe ido yashiga Yi, cikin kankanin lokaci ta birkita masa lilsafi, ganin yanda ya daburce Abin kawai yake da bukata yasa ta zame jikin ta.

Kallon ta yake alamu Meyasa,marairaice Fuska tayi tace, "haba infinity Dan ALLAH yanzu ko abinci fa baka ciba, baka jin yunwa ne?

,"kin dafa ne banci ba?

Murmushi tayi tace, "aikuwa nayi maka abinci mai ďankarin daďi sweet heart.

Da mamaki yake kallon zazzkiya wai yau itace dayin girki tashi yayi yace, "kamar kuwa kansa inajin yunwa sosai, tashi sukayi suka nufi falo,jikin zazzkiya har rawa yake batada wani buri daya wuci taga yakai abincin bakin sa, Zama yayi agurin yace, "takawa masa abincin kawai yafi jin daďin cin abincin a carpet.

Zuba masa abincin tayi gabaki ďaya Dama iya cikin sa tayi, ruwa ya ďauka yafara SHA, ďaukar cokalin da zaiyi saijin sallamar Inna sadiya sukaji kamar daga sama,jiki na rawa raihan ya mike kamar wacce yayi shakara baiganta ba haka yake ji.

Zazzkiya kuwa tsabar bakin ciki kamar ta haďe zuciya ta mutu take ji, gaisuwa sama sama tayi mata sannan ta miki, ,"ina zaki tafi?

,"ruwa zan ďauko mata.

,"a a kima barshi aiga wanna ,gabaki ďaya yaďauko ya dire agaban Inna sadiya harda abincin, ita kuwa dama fa kunsan kawar Hafsat Rano ce gun kwadanyi Dan haka babu musu ta ďauki cokali zata fara aika musu dashi.

Cikin sauri wanda harsanda ta zubar da ragowar ruwar dake ije , rike hannun Inna sadiya tayi tace, "Inna kibar masa wannan yanzun zan haďa miki naki lafiyayyiyar abincin,raihan kuwa wanda tuni ransa yagama baci daka mata tsawa yayi yace,"ke Mara hankalin inace da zaki tsayar da ita daga cin abincin da ďanta ya bata?

Murmushi tayi wacce iyakarta Fuska tace, "haba sweet mezaisa na Hana mummy na abinci kawai dai naso na dafa mata wacce tafi wannan haďu ne.

,"murmushi Inna sadiya tayi tace, "Yauwa yar abarka irinku ake so, Kai maza Zoka ďauki abincin ka.

Murmushi yayi dan sosai hakan yasashi farin ciki yace,"OK to ki hanzarta domin tare zamu ci, kina cin naki nima inacin Nawa ko umma, Dariya sosai tayi tace, "hmmm ALLAH yayi muku abarka akkai dai samun irinka awannan zamanin gaskiya sai anduba haka kawai da kaje zaka ďauko mana wata kucaka wai labiba haba.

Wani irin zafi yake ji tun daga tsakiyar kansa har tafin kafarsa ,ganin yanda Inna sadiya ta zage tana zuge labiba da zagi ta mance duk asanadin soyaya yakai matsayin da yake ayanzu kuma duk sanadin tane.

Zaman jiran abincin Inna sadiya sukayi babu Wanda yakuma cewa komai.

itakuwa zazzkiya banda tsinuwa da ashariya babu abinda take kundumawa Inna sadiya.....

Kuyi hakuri da wannan

Love you all

💐JAWABI 💐

DUK A SANADIN SOYAYAWhere stories live. Discover now