chapter 11

465 55 1
                                    

Duk asanadin soyaya...

By

SAFNAH ALIYU JAWABI

Bismillahi rahamanin rahim

Cike da tsoro da fargaba afeeya ta nufi gurin labiba Tana Mai cigaba da zubda kwalla,ganin haka yasa labiba ta shige cikin ďakin da sauri kifa kanta tayi asaman katifar tare da sakin kuka Mai tsuma zuciya.

Cike da danasani afeeya ta tsaya akanta cikin muryar kuka tace, "Dan ALLAH kiyi hakuri ni kaina nayi dana sanin shiga cikin lamarin daba nawa ba,harna aikata wannan babbar laifin, nasan yanzu kina mai cike da jin haushi na, koma ince kin tsane ni ,amma kisani tamkar yar'uwa nake ďaukar ki shiyasa nake jin zafin abinda raihan yayi miki bayan duk halalcin ki agare shi.

Ďago Kai labiba tayi ga mamakin afeeya sai taga labiba ta rungume ta tana cewa, "bansan dame zan saka muku ba, kune kawai nake gani tamkar dangi na, kun kaunace ni alokacin da duniya ta juyamin baya,aku yaushe kuna kwakari mayar da damuwata taku, bansan dame zansaka muku ba, kun gamamin kumai.

Ďago kanta afeeya tayi haďe da share mata hawaye tace, "Karki damu da akwai abinda zaki saka mana dashi aunty labiba.

Cikin sauri tace, "ki faďamin nikuma nayi miki alkawari Yi muku shi idan harbai sabawa addini naba.

Murmushi afeeya tayi tace, "inaso ki cire damuwar raihan aranki, ki ďauka baki taba sanin Saba, aunty labiba ki Mikawa ALLAH duk kannin lamarin ki, ina Mai tabbatar miki ALLAH zai musanya miki da mafifincin alkairi.

Murmushi labiba tayi tace, "nayi miki alkawari IN SHA ALLAH daga rana irin ta yau bazan sake saka damuwar raihan araina ba.

Aranar gabaki ďaya su kwanan farin ciki sukayi wacce sun daďe basuyi irin taba...

*********

Raihan kuwa wani irin bacin rai dabai taba tsintar kansa aciki bane yamai ďirar mikiya cikin kankanin lokaci ya gama haďa gumi,tashi yayi yashiga zarya adakin yana tunanin wace yariyan ce wannan wacce harta samu zarra zagin sa,banda haka harda yiwa matar sa kazafin zina,tashi yayi yashiga toilet Dan watsa ruwa ko zaiji daďin jikin sa..

*******
Tun safe Sadiq ya iso gidan raihan, saidai gabaki ďaya yanda yaga raihan ďin tabbas yasan akwai wata akasa, murmushi yayi yace, "yallabai ya akayi ne?yaufa ranar kace Ango Kake angon zakkiya, dan haka yanzu ba lokacin haďe girar sama da kasa bace, com on tashi ka shirya kasan 10-am za'aďaura Aure ko.

Yake kawai raihan yayi haďe da riku hannun Sadiq yace, "tabbas ni ďin Ango ne amma ba angon labiba ba Sadiq, ba RAI'ISH ďita zan aura ba, Sadiq shin banyi butulci ba? Shin ALLAH bazai kamani da hakkin AISHA labiba ba?ka taimake ni ka taimakeni Sadiq kaji abinda wata yarinya take faďamin jiya dana kira RAI'ISH ďita kuwa?.....zaiyana masa yanda sukayi da afeeya yayi tare da fashewa da kuka.

Sadiq kuwa wani irin zufane ya keto masa Dan koba afaďaba yasan tabbas afeeya ce, jingina Kai sa yayi yace, "kayi hakuri yanzu ba lokacin wannan maganar bace raihan be a man mana idan muka dawo sai muyi magana.

Da haka yasamu ya rarrashi raihan yashirya suka nufi gurin ďaurin Aure.

Bayan andawo daga ďaurin Aure sadiq ya wuce asibiti, sosai yaji ďadin ganin yanda labiba ta watsake Zama yayi shima aka cigaba da Hira Candai yatuna da zancan zagin da afeeya tayi wa raihan.

DUK A SANADIN SOYAYAWhere stories live. Discover now