chapter 28

452 40 2
                                    

Duk asanadin soyaya

By

SAFNAH ALIYU JAWABI

Bismillahi rahamanin rahim

Da gudu ammi ta nufo gunta tana jijigata haďa da kiran sunan ta, cikin mintina kalilan suka kaita asibiti babu irin gwaje gwajan daba yiba amma ba'agano musabbabin abinda ke damunta ba, sosai hankalin alhaji danko yayi masifar tashi ganin halinda yarsa take ciki aikuwa babu bata lokaci ya baro Dubai Don zuwa inda diyarsa take.

Koda yazo Abubawa sunkara rincebewa domin kuwa wani irin kakkaurar ruwa Mai ďoyin gaske ke fita ta kowani kofa najikin ta, sosai hankalin yan uwa ďa abokin arziki ya tashi.

Batare da bata lokaci ba alhaji danko yasa aka fitar da ita kasar Dubai Don acewar sa Dr basu Eya aiki bane, bangaran Drs ďin kuwa sosai sukayi farin cikin haka Don wallahi sosai warin ke matsifar damun su.

Koda suka tafi maganar dai ďaya ce, babu abinda ke damunta, amma taurin Kai irinna alhaji danko kin amincewa yayi daga nan ya dauki ta sai china, suma dai abinda suka gani kenan amma ganin yanda yaruďe yasa sukayi ta cinye masa Y'an kuďinsa har saida sukaga yana niman komawa karkaf yasa suka fita suka faďa masa gaskiya, aikuwa rashin hankalin da alhaji danko yayi musu asibitin saida sukayi ďana sanin amsar aikin tun farko.

Ganin yanda yake niman Tara musu jama'a yasa suka kira jamian tsaro suka fita dasu harda Mara lafiyar wajan asibitin sannan sukayi musu gargaďi da karda sukuskura sushiga asibitin.

Aikuwa ranan amminta tayi kuka kamar ranta zai fita gashi bazata iya Faďawa alhaji asalin abinda yafaru ba, Don ko shakka babu Sakinta zaiyi itakuwa bata Shiryawa hakan ba.

Hakaa tanaji tana gani tayi shiru(wannan shi akae kira self-respect hahaha) gida suka dawo babu shiri aka shiga yinnna gida.

Kwanan su bakwai da dawowa cikin ďare zakkiya ta tayar da kowa gidan sakamakon yanda take jin zafin ciwon Feye dana ko yaushe , duk suka fito aruďe cikin kuka tace, "please daddy forgive me wallahi it wasn't my fault it was mummy that took me to he's place daddy and now see what has happened, please daddy forgive me.

Gabaki ďaya kan alhaji danko ya ďaure gabaki ďaya yakasa gani abinda take magana Kai , tsugunnawa yayi a gabanta yace," kiyi shiru baby kimin bayani akai mee kike maganar wai?

Aikuwa zakkiya bata rage komai ba ranar saida tafaďa wa kowa ta yanda suke less da Ni'ima harda yanda tarinka Yi gidan raihan da zuwa gida boka harda amfani da ita dayayi .

Salati abba yayi yace, "kin cuceni kin salwantar Minda rayuwar ya,baxance dake komai ba amma kije nasaki ki Sani uku, wata uwar kara mummy ta kwallah tana kuka.

Wani irin Mika zakkiya take Tana jujjuya kanta, da sauri daddy yakaraso gunta yana kiran sunan ta, amma ina cikin mintina uku zakkiya ta amsa kiran ubangijin ta ,ranar daddy da mummy sunyi kuka kamar ransu zai fita.

Washa gari aka ďauki gawar zakkiya aka sadata da gidanta na gaskiya.

Saida kowa ya watse sannan daddy yatafi hargidan Inna sadiya, zuwansa yayi daidai da saukowar raihan daga motarar data ďauko shi daga airport Don saukowar sa kenan.

Da fara'a daddy yamika masa hannu sukayi musabaha sannan yace, "dama kuwa kamar kasan gurinka nazo, wato akwai abubuwa da suka faru tsakanin ka da zakkiya lokacin bana kasar wanda wallahi nasan duk laifin nane, domin kuwa ban tsaya agida na baiwa iyalina lokacina ba bare ayi maganar tarbiyantar da gudan jinina.

DUK A SANADIN SOYAYAWhere stories live. Discover now