chapter 5

546 48 5
                                    

❄️❄️❄️❄️❄️❄️                  
    *DUK A SANADIN SOYAYA*
                      ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*💥
_(THE STARS THAT SHINE IN THE WORLD OF WRITER'S)_

https://mobile.facebook.com/Taurari-Writers-Association-109116734087974/?ref=opera_speed_dial

*T. W. A✍🏻*

*STORY*

&

*WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

chaptar*0️⃣5️⃣

*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*


,, Cikin ikon Allah labiba bata wani ji ciwo mai tsanani ba,hakan yasa da aka tambaye ta sunan garin su babu bata lokaci tace,"Kaduna kuma ta faɗa sunan unguwar su, koda mutanan anguwar suka same labarin abinda yafaru,tuni hankalin kowa ya tashi Dan kowa yasan irin dattakwan da iyayan labiba suke dashi.

Cikin kankanin lokacin aka sadasu da gidan suna gaskiya saidai muce ALLAH yajikan su.

Sosai mutuwar iyayan labiba ya tabi kowa dan irin kukan da labiba take akullum,idan kaga raihan saika rantse iyayan sane suka rasu.

Bayan anyi sadakar arba'i labiba taci gabada zuwa makaranta saidai tsoro da take yawan jine yasa bata samun isansan barci gashi ita kaďai ce a gidan,ganin haka yasa tanime anema mata masu haya dansu ďebe mata kewa, sannan kuɗin data karba ta rinka biyan kuɗin makarantar ta, harzuwa lokacin da yan uwanta zasu shigo garin.

Cikin kwanaki kalilan kuwa aka samu ƴan haya, dubu goma shabiyu suka biya na shekara, haka zamansu yakasance gwanin sha'awa dan sosai malam audu da matar sa luba suke kula da ita sosai.

Lokacin da aka biya labiba kuďin hayan nata Tana zaune ta saka kuɗin agaba tana tunanin abinda zatayi dasu, cikin sauri ta tashi jikin ta har rawa yake tafita daga gidan, bata isaya ko ina ba, sai gidan su raihan,tana zuwa ta tarar da sadiya wacce take kiranta Inna sadiya tace, "sannu da aiki Inna "

Cikin zaro ido tace, "wani aiki kika bani? Eye nace, "wani aiki kika bani,da kike min sannu?

Muryarta har rawa yake tace, "k..k..kiyi hakuri Inna.

"munafuka kullum cikin bada hakuri kamar dangin maroka,mekike Nima?

"Inna dama bawani abu bane kuɗine na kawo wa ya raihan,cikin sauri sadiya ta mike har zaninta nan kwancewa,murmushi tayi tace, "haba yar abarka ai saiki faɗamin tun farko zauna bara nakira shi, ciki sauri ta nufi ɗakin raihan, tana tsaye sai gasu sunfito tare saidai, Sam babu walwala afuskar raihan ganin hakan yasa labiba tasha jinin jikin ta.

Sunkuyar da kanta akasa tayi tace, "ya raihan ina kwana?

,"Lafiya lau ya akayi?

Kuɗin dake cikin hijabin ta tafitar tace, "ya raihan gashi ka biya kuɗin jam ɗin ka dashi.

Ido ya tsare ta dashi yace, "ainah kika samu kuɗi?

Cikin sauri Inna sadiya tasa hannu ta kwace kuɗin,duk kansu kallon ta suke cike da mamaki tace, "me kuma haka yarinya ta kawo maka kudi maimakon ka karba kayi godiya, amma saika tsareta da wasu tambayoyi marasa ma'ana.

DUK A SANADIN SOYAYAحيث تعيش القصص. اكتشف الآن