chapter 3

784 55 1
                                    

❄️❄️❄️❄️❄️❄️                  
    *DUK A SANADIN SOYAYA*
                      ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*💥
_(THE STARS THAT SHINE IN THE WORLD OF WRITER'S)_

https://mobile.facebook.com/Taurari-Writers-Association-109116734087974/?ref=opera_speed_dial

*T. W. A✍🏻*

*STORY*

&

*WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

chaptar*0️⃣3️⃣

*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*

,,,,,,Tana ďago fuska kuwa suka haďa ido wani irin abu taji hartsakiyar kanta Cikin sauri ta mayar da idanuwan ta ta rufe kamar mai barci, ganin haka yasa yaďan tabi Hafsah yace, "ki kula da ita ina zuwa yanzu kinji Lil sis.

Murmushi tayi tace, "to ya'ya saika dawo.

Kamar dama jira take yafita mikewa tayi tace, "Dan ALLAH Lil sis zanďan zaga, jiki na rawa Hafsah ta riko hannun ta takaita toilet ďin, sannan tafito murmushine har yanzu aKan fuskar ta tace, "Kai aunty ilham kinji Sunan data kirani dashi kuwa? ALLAH sunan ma yafi daďi abakin ta.

Murmushi ilham tayi tace, "ke dai Hafsah baki rabo da shashanci, shagwabe fuskar ta tayi" tace, "wallahi bari ya'ya yazo saina faďa masa.

Duk abinda suke faďa tana Jikin kofar toilet din tana jinsu, dariya sosai shirman Hafsah yabata harta fito fuskarta da alamar murmushi,cikin sauri Hafsah ta taso tace, "la aunty shine baki Kirani na taimaka miki ba"

murmushin datake boyewani ya kubbuce mata tace, "yi hakuri kinji bazan kara ba.

Duk kansu dariya sukayi harda ilham ganin yanda tabiye wa Shirman Hafsah.

Sosai taji daďin zama dasu Dan kaso Cikin ďare na damuwar ta sun wanke goma.

Koda sadiq yadawo yasame ta Cikin nishaďi sosai shima yaji Daďin hakan,sai kusan magrib ya mayar dasu gida.

Suna shiga tsalle Hafsah tayi ta ďare jikin mummy tana cewa, "wallahi mom matar yaya tana da kirki sosai kuma karki soki ganta Mom wallahi kyakkyawar gaske.

Murmushin jin ďadin yanda autar ta ta dawo gida cikin farin ciki tayi sannan tace, "kedai yar'nan saidai abarki waya faďa miki matar sane?to kima daina zumuďi matar abakin sani.

Kamar haďin baki gabaki ďaya suka ďago ido suna kallon Mom,jin abinda mom tafaďa bakaramar faranta ran ilham yayi ba, ga mutane biyu kuwa sam wannan maganar batayi musu daďin jiba Cikin sauri sadiq ya mike yace, "mom saida safe.

DUK A SANADIN SOYAYAWhere stories live. Discover now