chapter 27

440 39 3
                                    

Duk asanadin soyaya

By

SAFNAH ALIYU JAWABI

Bismillahi rahamanin rahim

Cokali hudu tayi tafara jin wani masifaffiyar ciwon Mara, tun tana daure wa harta fara salati jin yanda bayanta ya amsa lokaci ďaya.

Kallon ta ilham tayi tace, "lafiya aunty labiba meke damunki?

Nuna mata cikin ta tayi Tana yarfe hannu alamar tana cikin matsanan cin Hali, cikin nuna ko inkula ilham tace, "sannu bara naje naďan watsa ruwa na kwanta ALLAH ya sauwake,binta da kallon mamaki labiba tayi Tana aiyana wani abin aranta ganin yanda ilham ta nuna halin ko inkula.

Ďaga Kai tayi tace, "ilham kozaki taimaka ki kira min Y'a sadiq Dan ALLAH "

Wani mugun kallo ta aika mata dashi sannan tace, "hmmm kinga nikam bana da kuďi awaya bare na kira miki shi.

Wani irin ihu labiba tayi ganin jini na zuba ta kasarta,ilhma kuwa dawowa tayi ta tsaya akanta tana dariyar mugunta tace, "tabbas na daďe ina miki kallon sakarya amma ban tabbatarwa ba sai yau, waike tunanin ki harkin Kai macan da zatayi girki naci?

Hmmm gaskiya kam kin tabbata shashasha, to kisani wallahi koda Nakira miki Y'a sadiq babu abinda zai iya tsinana miki, Kai koda kuwa asibitin duniyar nan za'a zaga dake inama tabbatar miki bazaki rayu ba,domin kuwa maganin zubda ciki na zuba miki,sannan kaďan akace nazuba Idanna zuba dayawa tabbas mutuwa zakiyi,ganin babu wani amfani da rayuwar ki take tsinana min shiyasa na zuba dukka,don haka tun yanzu kifara niman yafiyata akan cin amanata da kikayi.

Wani irin mahaukaciyar duka sadiq ya rufeta dashi tamkar mahaukacin zaki, dukanta yake haďa da naushi  ,bakinta da hancinta gabaki ďaya jini suke zubarwa,da kyar labiba ta jamasa Riga Tana masa nuni da jinin dake kara yawa,tura ilham cikin ďaki yayi wanda gabaki ďaya kamar Ma bata numfashi haka ta koma ya kulle yajefa 🔑 cikin aljihu.

Da gudu yafita da ita daga gidan, number afeeya yakira yace, "tasame su a asibiti labiba ba lafiya,aikuwa arikice afeeya tayi waje tana kiran driver,cikin mintina ta isa asibitin rike hannun Sadiq tayi tace, "yaya Tana ina aunty labiba Tana ina bro?

Rarrashinta yake saiga likita yafito,da sauri suka isa gunsa, "Dr ina fatan dai  anyi nasara?

Share zufa Dr yayi yace, "Alhamdullah saidai gaskiya tana da bukatar jini domin ta zubda jini sosai, kuma mun samu nasara ďan baifita ba, saidai Dan ALLAH adinga kulawa.

Murmushi jin daďi afeeya tayi tace ,"IN SHA ALLAH.

Zuwa sadiq yayi aka ďinba jinin sa aka saka mata saida yaga komai ya daidaita sannan yanufi gida, ďakin daya kulle ta aciki yashiga, haryanzu tana nan yanda yabarta, ruwa Mai Kankana yaďauko ya watsa mata, sauke nannauyar jiyar zuciya tayi, sannan ta fashe da kuka Mai ban tausayi.

"ilham.

Ďago Kai kawai tayi Don Sam bama zata iya buďe baki ba tsabar yanda take jin nauyin ta, "lailai kin kasance daga cikin azzaluman mutane, kin kasance Daga cikin mutane masu Fuska biyu, ALLAH ya isa tsakanina dake kije idan duniyar nanne ina Mai tabbatar miki ta isheki Riga da wando, akarshe ina Mai farin cikin sanar dake na sakike1 nasakike 2 nasakike 3 bana bukatar Zama da maci amana arayuwa ta ,yana kaiwa nan yayi ficewarsa yabarta tana kuka kamar ranta zai fita,dana sani Mara amfani ke cinta.

DUK A SANADIN SOYAYAWhere stories live. Discover now