Babi na 23- RAHEENAH

218 21 2
                                    

*KUNDIN HASKE*💡

*ALK'ALUMAN MARUBUTAN HASKE*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers*)

*Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai*

    *ƁOYAYYEN SIRRI*

*BABI NA ASHIRIN DA UKU*

    *NA* *RAHEENAT* ( *MRS❤️*)

*Ƙirƙirarren labari ne gajere, akwai abubuwan al'ajabi da rikitarwa aciki ban yi shi ɗan cin zarafin wani ko wata, Allah ya na son bayinsa masu yarda da kaddara mai kyau ko marar kyau Allah ya sa na gama shi lafiya ameen.*

                        *1*

Zaune ta ke bisa maƙeken gadonta na alfarma ta na luluɓe da katon mayafi, kallo ɗaya na yi mata na gane amarya ce saboda yanayin shigar da ta yi. kuka ta ke sosai tamkar ranta zai fita abin ya bani mamaki matuƙa, wannan kukan ya wuce a kirashi na rabuwa da iyaye, to ko auren dole aka mata? Buɗe kofar da aka yi shi ya datse min maganar zucin da nake. Kamilallen  saurayi ne ya shigo ba zai wuce Shekara talatin a duniya, sanye ya ke da manyan kaya farare tass har daukar ido suke yadda ya nufi gadon da sauri shi ne ya tabbatar min cewa shi ne angon.
Subhanallah! Maryam har yanzu kukan kike? Oh Allah na! don Allah ki yi shiru haka kin ji kada ki haifar ma kanki wani ciwon. Da ya ga bata da niyyar daina kukan ya janyota a jikinshi ta sauke ajiyar zuciya nan da nan jikinta ya fara rawa ta haɗiye kukan saboda wannan ne karo na farko da ta haɗa jiki da wani da namiji a rayuwarta kokarin janye jikinta ta ke yaki bata damar hakan, wani karfi ne ya zo mata ta hankadeshi da karfin tsiya ta ruga toillet ta rufe kofar tana kai dubanta ga window ɗin toillet ɗinta ta kurma wani uban ihu ta zube a kasa sumamiya.

da sauri Almustapha ya shiga bandaƙin bai wani bata lokaci ya dauketa cak yayi waje da ita yana kwala ma dreben shi kira, da gudu ya zo ya bude mai gidan baya ya shinfida Maryam wacce babu alamun lumfashi a tattare da ita rufe kofar yayi dreben yaja motar suka fita d'aga gidan. gudu yake sosai saman titi tamkar zai bar garin ikon Allah ne kawai ya kai su *ALMUSTAPHA PRIVATE HOSPITAL* rudewa ya sanya Almustapha mantawa cewa shifa  babban Dr ne da isarsu Ma'aikatan asibitin suka kawo gadon daukar marar lafiya ya shinfida Maryam suka yi ciki da ita da sauri don bata taimakon gaggawa.

Dafa kafadarshi da abokinsa Ismail ya yi shi ne ya dawo da shi d'aga tunanin da ya tafi,

"Haba Almustapha meye haka? Kaida ya kamata kayi juriya saboda yanayin aikinka ya gaji haka amma sai ka tsaya kana kuka tamkar mace, na sani kana jin radadi a zuciyarka da kuma ciwo saboda wannan ne daren da ka jima kana mafarkin ganinshi a rayuwarka sai gashi daren ya zo muku da wani *Ɓoyayyen Sirri* mai rikitarwa amma ka sani duk sanani yana tare da sauki ka jirani a nan saboda halin da kake ciki ko ka bini babu taimakon da za ka iya bata, ka wuce ofis dinka kawai zamu yi iyakar kokarinmu dan ganin mun ceto rayuwarta yana gama maganar shi yayi gaba bai jira jin amsar da Almustapha zai bashi ba".

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ciro hankici a cikin aljihun rigarshi ya goge fukarshi ya nufi ofis dinshi duk inda ya wuce ana gaisheshi bai ma iya amsawa saboda yanayin da ya ke ciki na tashin hankali hannu kawai ya ke ɗaga musu sun mishi uzuri saboda ba haka ya ke ba mutum ne mai fara'a da son jama'a, bude kofar ya yi ya shiga wani kamshi ya bugi hancinshi  ya lumshe idanunshi ya zauna bisa kujera ya dafe kanshi da ya ke barazanar tarwatsewa saboda ciwo da kyar ya bude jakar da ya shigo dashi ya ɓalle maganin (Mediq) ya sha ya kwantar da kanshi bisa kujerar ya rufe idanunshi tamkar mai barci, tunani ya mishi yawa abubuwa da yawa suke mai yawo a kwakwalwa. yana shirin mikewa Yaji ana buga mishi kofa ya bada izinin shigowa Ismail ne ya shigo yana goge zufar fuskarshi ya samu waje ya zauna.

Da ido Almustapha yake binshi kallo ɗaya zaka mishi ka fahimci yana cikin tashin hankali. Gyaran murya Ismail ya yi ya ce,

"Da farko dai ina mai baka hakuri Almus..."

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now