9

1.7K 199 12
                                    

KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association💡

(Home of Experts and perfect Writer's)

*SANADIN K'AWA*

NA

*khaleesat Haiydar*

BABI NA GOMA SHA HUDU


9




A hankali ta bude ido ta ga kanta kwance kan gadon asibiti ga Amminta a xaune gefenta kana ganinta Kasan ta yi kuka ba na wasa ba, daga gefenta a tsaye Umar ne ya jinginar da jikinsa da bango ya rungume hannayensa, sae mamar Safiyya da ma Safiyyar da makwabtansu kusan uku, ko wanne kallonta kawai yake, Safiyya da ita ma kana ganinta kasan tayi kuka ba na wasa ba ta riko hannunta tace "Are you okay fatima" kallonta kawai fatima take, Ammi tace "Amira" nan ma shiru, Umar ya karaso yana kallonta a sanyaye yace "Say something pls fatima" wani daga makwabcinsu ya fita sai ga sa da likitoci har biyu, magana likitocin biyu suka dinga mata su ma amma shiru sai kallonsu kawai take, can sai ga hawaye idonta, wanda hakan ya kara tada hankalin Ammi da mutanen cikin ward din don tun da aka kawota asibiti likitocin suka tabbatar masu da an shaka mata wani abu, but bayan nan basu gano komai ba kuma, daya daga likitan ya bukaci kowa ya fita duk suka fita, bbu irin maganan da likitan bai mata ba amma bata ce komai ba, daya likitan dake gefensa yace "This is serious" daga haka ya fita, sai ga shi sun dawo da wani likitan, duk dube duben da suka san ya kamata ayi mata sun mata amma basu gano komai ba. Har yamma suna asibitin amma Fatima bata cewa komai sai hawaye, nan likitocin suka basu shawarar a tafi da ita neuro psychiatric don duba kwakwalwarta, Umar ya biya kudin asibitin bayan anyi discharging dinsu suka koma gida kafin a fara shirin kaita wani asibitin Tunda Husnah taji dawowar fatima kuma bata magana ta daga hankali xata je damaturu gun kakarta, duk da mahaifinta bai amince ba haka ta hada kayanta da goyan bayar innarsu ta yi wucewarta ta bar suleja. Washegari da safe aka tafi da Fatima asibitin da aka ce, duk iya bincikensu su ma basu gano komai ba kuma suka tabbatar da bbu wata matsala tare da brain dinta, nan suka dawo gida Ammi na kuka duk ka ganta sai ta baka tausayi don har ta rame, All this while kuma Umar was by her side duk da shi yana kkrin rage nasa damuwar ita yana kwantar mata da nata, rokon Allah aka dukufa yi mata aka kyale asibitin. Bayan kwana biyu Ammi na tsakar gida da yamma tana dama mata kunu Ummi na wanke wanke wani yaron makwabta ya shigo wai ana sallama a waje, Ammi tace "Waye?" Yaron yace "Wani mutumi a mota" Ammi tace "Toh kace ya shigo" don duk tunaninta abokin marigayin mai gidanta ne don jiya ma ya xo, yaron ya juya ya fita, gyara Hijab din jikinta tayi ta sa Ummi ta shimfida tabarma, bayan kusan minti biyar aka shigo gidan da sallama, tun da ya shigo Ammi ke kallonsa, shi kam kallo daya yyi mata ya sauke kai ya nufi tabarmar da ke a shimfide ya xauna bai sake yarda sun hada ido ba murya can kasa yace "Ina yini mama" har lkcn tana kallonsa tace "Lafiya qlau sannu da xuwa" yace "Yauwa nagode" rasa abinda xai ce yyi, Ammi tace "Amma ban gane daga ina ba" ya d'an shafa kai a hankali yace "A'a dama... dama xo duba jikin fatima ne, ashe abinda ya faru kenan" tace "Allah sarki, to mun gode, da sauki Alhmdllh" kallon Ummi tayi tace "Duba ko idonta biyu Ummi" Ummi ta mike ta shiga dakin ta fito tace "Idonta biyu Ammi" Ammi ta kallesa tace "Toh amma kuma bata magana fa har yanxu bare ta fito ku gaisa" sai a lkcn ya dago da sauri yana kallonta yace "Bata magana kuma?" Ammi da har hawaye ya kawo idonta tace "Eh har yanxu ana ta rokon Allah" ya mike yace "Toh xan iya ganinta don Allah mama" Ammi ta d'an yi jim, can a hankali tace "Toh tana ciki...." dakin ya nufa ya shiga ciki, kwance take sai dai ba bakin kofar take kallo ba, ya karasa har kusa da ita yana kallonta, a hankali ya durkusa kusa da ita yace "Fatima....." Dago kai tayi suna hada ido ta mike xumbur ta yo waje da ido tana kallonsa a tsorace, ja baya ta fara yi tana girgixa kai hawaye cike idonta, ya matsa kusa da ita ya kamo hannunta yace "say something now.... Talk to me" Ta fashe da wani matsanancin kuka jikinta na rawa tace "Na shiga uku, don Allah don annabi ka wuce, kayi hakuri, why did u follow me" lumshe ido yyi na kusan second biyar sannan ya bude, can ya hade girar sama da ta kasa yace "Then why are u pretending u can't talk?" girgixa masa kai tayi da sauri, yace "Answer me" hawaye sosai take cikin sanyin murya tace "Because I don't knw what to tell my mother, ban san me xan ce ma Ammina ba" d'an murmushi yyi yace "Kinga kilan shi yasa na xo da kaina in mata bayani"....." Xaro ido tayi ta kamo hannunsa a rikice tace "Wayyo ni, don Allah ka rufa min asiri kar ka min haka" shiru yyi ya kafa mata manyan idanuwansa, Wanda hakan ya sa ta sauke idonta kasa, murya can kasa yace "Ohk then, tashi ki rakani xan wuce" yana magana ya ciro wayarta dake aljihunsa ya ajiye a gabanta, kallon wayar kawai take a tsorace, cikin muryar kuka tace "Aa na bar...." Yatsu biyu ya daura a lips dinsa yana mata wani irin kallo ba shiri ta hadiye abinda xata ce, ya mike yace "Tashi ki rakani" ba musu ta tashi tana goge hawayen idonta, yana gaba ta bi bayan sa suka fita dakin, har wani bari jikinta yake, tun da suka fito Ammi ke kallonsu, fatima ta kasa kallon mahaifiyarta tana iya kkrin ganin bata bar hawaye ya sakko mata ba, ya ce "Mama ni xan koma, Allah ya kara lfya" Ammi tace "Toh mun gode sosai, Allah saka da alkhairi" kallon fatima yyi yace "Allah ya sauwake" ta hadiye abu da kyar ta ki cewa komai ya mata wani kallo yace "Allah ya sauwake nace!" a hankali tana wasa da yatsunta tace "Ameen nagode" murmushi yyi ya nufi zaure bai kuma juyo ba har ya fita gidan.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now