Babi na Farko_ Nana Diso

18.4K 802 15
                                    

*KUNDIN HASKE*

            _Al 'kaluman Marubata_

     KUNGIYAR:-

     *HASKE WRITERS ASSOCIATION* (home of expert and perfect writers)

   TARE DA AL 'KALAMIN✍🏼
           *NANA DISO*

*DARAJAR MUTUNCIN MU.....*
       _('yan zamani)_

     
BABI NA DAYA

    Wani dogon tsaki taja sannan tace Haba hajjaju wallahi zan siyar da akuyar nan yaza'ayi k'awaye na masu class su shigo gidannan jiya ma muna waya da minister sai ga kukan akuya maaaaah haba gaskiya bazata sabu ba, sai karya nayi masa nace a tv muke kallo.

       " Haba walida yanzu abunda kike fada ya dace kin dauki iyayenki ba abakin komai ba wato basu da mahimmanci atattare dake wallahi kiji tsoron Allah dubi yadda kika koma sai kace karuwa.

     " ke iya bakinki fatima kafin naci ubanki wallahi talauci har wani abun so kayan bala'i ke bari kije banga abun alfahari agidannan ba kuma zanfita zan nemi cigaba wallahi kibini a hankali nagayamiki dai!

    " fatima ce tasaka kuka tace gaskiya Allah ya wadaran wasu 'yan zamanin wallahi hajjaju harda laifin ku ke da Abba tana kawo muku kudi kunayi mata shiru bakusan sanaar da take ba..
     
      " Hajjaju ce tace lallai ne Munada biye mata Amma kinga walida wallahi tafi karfina Tasakawa kanta wani irin buri ga kuma son abun duniya dubi yadda ta mai da kanta fara dubi yadda tasaka karin gashi ga wani abun ido Allah dai ya shiryata ke kuma Allah yasa bazakiyi halinta ba...

     walida ce tafito sanye da wasu shaidanun kaya duk sun kamata tana kamshi wani irin murmushi tasaki sannan tace sai kuyita magana indai magana ce baku gaji ba ni nayi gaba Honorable yazo yana jirana.

        Babu wanda ya kulata acikin su gaba daya suka cigaba da harkar gabansu..

    Mu'azzam ne ya sakko daga kan babur dinsa yanata sauri har sai da yasha gabanta walida yanzu wannan rayuwar dakika daukarwa kanki mai billiwa ce? yanzu duk irin soyayyar da na nuna miki yanzu kin yardata? walida aure ne ya kamace mu yanzu ba wannan yawon da kikeyi ba.

    " Tofar da yawu walida tayi tace kai wai kana shaye shaye ne? kai wani irin dan iska ne ka kalle ni kace zaka aure ni ka haukace? banza talaka matsiyaci kafara zuwa kazama alhaji mai kudi sai kazo kasamu lokacina Amma wallahi kama raina ni , Mu'azzam kake ko wa? Dallah bani wuri kafin na kifa maka mari stupid kawai doye gaye....

      Jikinsa ne duk ya mutu sannan yayi gefe yana kallonta cike da kaunarta da soyayyar ta cikin kunar rai ya karasa gidan sai da suka gaisa da hajjaju sannan tace " nasan walida ce ta bata maka rai mu'azzam kayi hakuri Shaidan yariga yayi mata k'ida akanta...

     " Hajiya zanje nakara kuratu zan kuma cigaba da bussiness dina inshaaAllahu sai nima nasamu rufen Asiri hanyar kuwa da walida take kai itace mafi rashin tabbas din hanya kuma nasan sharrin kawaye ne na 'yan zamanin nan...

   "Tabbas maganarka haka take kuma har kullum bazan daina yi mata addua ba har ranar da zata gane...

     walida tan bude motar tace Alhaji na na kaina gomnan gobe da yardar Allah yanaga ka bata rai ne?

    " Haba walida yazaki barni a shanye kinsan dole sai dake zan tafi haba sweety?

    " Shine kake bata rai to sai nabar maka motarka wallahi mutum bashida uzuri kuma kaga karka kara cemin sweety ba'a daura ba kagane??

     " Naji Allah yabaki hakuri muje to... " yanzu kayi magana da zaka kawomin wani karatu na yara???

       " Allah ya huci zuciyar ki walidata yanzu wani hotel mukayi???

KUNDIN HASKE💡Där berättelser lever. Upptäck nu