3

43 3 0
                                    

©️Fertymerh Xarah💞

3

Gidan cike yake da yan'uwa da abokan arziki domin taya su murnar samun ƙaruwa da suka yi.

Sai faman hira ake ana dariya cikin nishaɗi duk wanda zaka kalla a lokacin tsabar farim ciki ce zaka samu a tare dashi, wasu kuwa suna harabar gidan suna aikace aikacen ɗora girki da ruwan wankan me jego da baby.

Mutanen Abuja ma tuni sun iso su Annam itace riqe da jaririya duk wanda yazo ganin baby ita ke badawa kuma ita ke karba ta riqe, tana son yara sosai kuma ita kaɗaice iyayenta suka haifa.

Ko kaɗan mariya batayi tunanin zuwa sokoto domin taya matar ƙanin mijinta samun baby ba hassalima faɗa suka yi da mijinta sosai kan cewa babu inda zata zo, wai Halima ta rainata bata ganin girmanta ko kaɗan yanzu ma idan tazo tasan zata saka yan uwanta su wulaqantata ne.

Babu yanda Alhaji ya iya dole ta saka shi zuwa shi da Annam duk wanda ya tambaya ina Mariya sai suce bata jin daɗi amma zata shigo ranar bikin sunan baby.

Ga ruwan zafi na wankan baby an kawo waye zai yi mata wanka? cewar Nana ƙanwar Halima tana kallon yan uwan nasu cikin farin ciki.

Aa ni zan mata cewar Halima tana kallon su a ruɗe.

Duk falon suka ɗauki dariya wasu har da taba hannayen su,

Oh oh su Halima an kaiga baby yanzu wankan ma kece zaki mata duk yawan mu anan bazakiyi kara ko nuna alkunya ba wannan fa yar' farin ce kada ki manta cewar gwaggo wata matashiyar dattijuwa wacce da alama ƙanwar mahaifiyar su.

Murmushin yaƙe Halima tayi cikin jin nauyi da kunyar abun da tayi to ya zatayi dole ta rufa sirrin abinda suka haifa idan ba haka ba wannan taron da akayi a gidan tsab kowa zai sani kuma koda wani baije waje ya faɗa ba wani zai je ya faɗa, they are all her family but you cannot trust anyone yanzu.

Ba haka bane gwaggo dama ina so na faɗa maku tun ɗazu na manta ne ɗazu a asibiti doctor ya gargaɗe mu da kada muyi mata wanka a yanxu sai bayan kwana bakwai, dalili suna tunanin kamar tana da pneumonia da kyar suka ceto ta saboda numfashi ma da kyar take iya yin sa lokacin da aka haifeta, sun bada kwana bakwai mu sake zuwa da ita asibiti ayi mata bincike sosai idan babu sai acigaba da yi mata wanka.

Fuskar kowa ta nuna jimami da rashin jin daɗin abunda suka ji a yanzu kowa ya soma tofa albarkacin bakinsa na yiwa babyn fatan samun lafiya yasa ba pneumonia ɗin bace zargin likitocin ne kawai.

Halima ta sauke numfashi a hankali ganin ta sami nasara dalilin ta na cewa har tsawon kwana bakwai saboda tasan daga bikin suna su kaɗai ne zasu rage a gidan ta kula da babyn yanda ya dace,amma tambayar Annam ta bazata ta bata tsoro kaɗan.

Momin sokoto shikenan bazaa mata wanka ba har 7 days ai zatayi datti, kina gani fa kowa yana zuwa daga wuri daban daban ya ɗauke ta.

Murmushin yaƙe tayi a karo na biyu tace ai zaa dinga goge mata jikinta da dare idan zamu kwanta a saka mata kayan sanyi haka doctor ya faɗa mu riƙa yi mata.

Haka suka yini a ranar cikin farin ciki da nishaɗi sai tsokanar juna suke dama an jima baa haɗu haka ba yan uwa, da yamma suka soma tafiya.

Da dare Annam kwance da baby sai shafa jikin babyn take tana jin daɗin haka tana lumshe idanuwan ta,

Momin sokoto kizo ki gogewa baby jikinta kamar yanda kika ce ɗaxu.

Halima ta ɗago tana kallon Annam da idanuwanta ke lumshe take maganar,
Tace ki bari na gama abubuwan da nake yi xanyi mata idan kina jin barci ki gyara kwanciyar ki da kyau.

Tace aa ni baxan yi barci ba har sai naga kin gyarawa ƙanwata jikin ta, she is too dirty cant you see, mutanen sun saka mata datti, qamshin jikinta ma babu turare duk sun shanye ta faɗa tana kai hancinta jikin baby ɗin.

Dariya sosai Halima tayi tana faɗin wato qamshin turaren ma shanye shi mutane suka yi kina da ban dariya Annam, kiyi haquri ki kwanta barci idan na gama haɗa kaya da nake zan tashe ki barci kigani.

Promise me zaki tashe ni.
Insha Allah Annam,

Aikuwa ba jimawa barci mai nauyi ya ɗauke ta, Halima tayi murmushi tana cigaba da aikinta tare da mamaki wayo irin na Annam kamar ba yar shekara biyar ba.

Bata yi yunqurin tayar da Annam barci ba sai da ta canxawa baby pampers tayi mata tsarki ta saka mata wani kafin ta tayar da Annam.

Ta daɗe tana mamakin ganin yanda Annam ɗin ta xauna tana kallon yanda take gyara baby ɗin kafin su kwanta daga baya already ta riga da tayi sallama da Alhaji ganin yana da baqi itama tana da nata baƙin.

*

Daren biki gida kam sai hamdala saboda yawan yan uwa da abokan arziki ayyuka suke kasancewar gobe biki.

Daga gefe mariya ce zaune tare da ƙawar ta da basu jima da xuwa ba, shima sai da Alhaji Abdallah yayi da gaske kafin tazo kuma tunda tazo batace a bata babyn ta gani ba, Halima ce da kanta ta kawo babyn taqi karba sai tabe baki tayi tana kauda kai gefe, ai tunda an tilastamin zuwa  naga abunda kika haifa na menene na biyo ni da baby idan ba kinsan kin haɗa min wani munafurci ba.

Halima tayi murmushi tana rungume baby idan da sabo ta saba da halin mariya yan uwanta ma ba wnda baisan irin ƙiyayyar da mariya take mata ba, kuma har yau ba dalilin da zata bayar na cewa ko tayi mata wani laifine kome shiyasa a yanxu haka yan uwanta babu wanda ya kula mariya ko gaisuwar arziki kowa yana abubuwansa kamar babu ta a gidan wanda hakan ba qaramin ƙona zuciyar mariya yayi ba, a ganin ta an wulaqanta tane.

Tace kiyi haƙuri Anti mariya bana nufin ki da sharri na ɗauka koda bakya ƙaunata zaki ƙaunaci wannan baby ki ɗauke ta tamkar Annam domin ita bata da laifi ko wata masaniya akan duniya ma ballantana ke.

Mariya ta tabe baki a zuciyar ta Allah wadarai tayi da kalaman Halima na cewa ta ɗauki jaririyar kamar Annam a fili kuwa banda harara babu abinda take bankawa Halima.

Nana dake gefe tana kallon su duk da batajin maganar su ta ɗaga murya a hankali yanda mariya zata jiyo ta,
Tace yaya Halima tsayuwar me kike yi da baby haka a hannu, dan Allah ki bar harabar gidannan kije ki kwanta ki huta duk wani mai harare harare ya cigaba ko a jikin mu koda kuwa ruwan idanuwan sa zasu tsiyaye.

Ke ni zaki yi wa rashin kunya? Mariya ta faɗa tana kallon Nana tare da nuna kanta da yatsa.

Nana ta tabe baki tare da ɗauke kanta gefe bansan da zaman ki a wurinnan ba sai da kika yi magana rashin kunya na menene ina magana da yaya tane ko na ambaci sunan wani anan?

Mariya tayi ƙwafa cikin bacin rai kamar bazatayi magana ba ganin Halima ta juya batare da tayi magana ba ya saka ta saurin cewa,

Ni fa Hadiza banda Alhaji ya takurani wallahi bazan zo ba, kazo kana cuɗanya da ya'yan talakawa sai su riƙa raina ka suna ganin kamar duka abu ɗaya ne.

Sauran yan uwa Halima suka dubi mariya cikin mamaki, kafin kace kwabo faɗa ake sosai a gidan ana musayar yawu, da gudu Halima taje sashen baƙi ta sanar da mazan halin da ake ciki.

Zuwan su bai hana faɗan ba kamar zasu daki junan su da kyar Alhaji Abdallah ya fita da mariya gidan ransa a bace yake kallon ta bayan sun fito harabar gidan inda ba mutane.

Kin bani kunya, da mutuncina zaki zo ki zubar min saboda na takura ki zuwa ganin ƙaruwar baby, duk fa abinda kike mariya ina sane kuma na sani.

Ni yanzu nice da laifi kenan bayan bakasan meya faru ba har kana yanke hukunci dan kawai nace a bani baby nagani suka soma yaɗa min magana cikin habaici musamman ƙanwar Halima daga ƙarshe ma aka hanani ganin babyn dana zo domin ta sannan kace bazan yi magana ba har fa talaka suka kirani.

To menene aciki mariya? Shi talaka abun ƙyama ne da za'a kira ki dashi kiji bacin rai, look mariya duk take taken ki nasani kada ki kuskura ki batamin rai nan gidan ƙanina ne uwar mu ɗaya uban mu ɗaya ki gayamin dalilin ƙiyayyar da kike yiwa matar sa me tayi maki ne?

Tayi shiru amma a ranta tana ƙalubalantar  Halima da yan uwan ta.

Ba shiri ya ɗauke ta da abokiyarta hadiza ya kaisu hotel yayi masu masauki ace duk girma irin na gidan da wadatattun ɗakuna sai ya fita ya kai matarsa hotel saboda tsoron fitinarta acikin dare,.......

Washe garin suna an ɗauko biki lafiya komai yana tafiya dai dai kamar kar mariya ta bayyana a gidan wata sabuwar rigima ta barke tsakanin ta da yan biki.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now