2

1.4K 140 7
                                    

KUNDIN HASKE

ALK'ALUMAN MARUBUTA🤝🏻

💡 *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

*Wattpad:-Ummishatu*

TARE DA ALK'ALAMIN

*UMMI A'ISHA*👌🏻

*BAK'ON YANAYI...!*❤
    (Kafar sadarwa)

*Babi na Ashirin da d'aya (21)*

بسم الله الرحمن الرحيم

*Sadaukarwa ga k'ungiyar haske,hakika albarkacin Kai hula ke yin daraja...!*

*2*

    ***Tsawon mintuna biyu zuwa uku sannan innah tasoma da cewa,

"Nasan kina son mijinki kuma bakya san saba masa to nidai bazan gaji da fada miki gaskiya ba,ya kamata kema yasan kinada martaba da daraja bawai sai idan matsala ta taso masa ba a lokacin ne zai tuna dake....haba yar nan kamar wacce ya kulle miki kwakwalwa? Ni bawai nufina ki sab'a masa ba amma nafi son kema ki kwaci yancinki,kiduba fa ki gani bakida wuni bakida kwana yana can wurin matarsa yana sheke ayarsa ke kuma yabarki anan kina fama da rayuwa to har yaushenki zaki tsaya ki zauna ki zuba idanu kina kunsar wannan bacin ran?"

K'asa nasake yi da kaina ina sauraren fadan innah wanda ta inda take shiga bata nan take fitaba jin ta dan tsagaita yasani sake yin kasa da kai cikin sanyin murya nace,

"Innah kiyi hakuri wallahi sai mun yiwa abul khair uzuri tunda ada ba haka yakeba k'addara ce kawai data gifta ta sauyashi yazama haka..."

"Ai shikenan Allah yaganar dashi gaskiya ke kuma yakara miki hakuri"

"Amin innah"

Yunkurawa nayi zan tashi nan naji innah nacewa haidar yaufa me sunan nashi zai dawo daga gombe wacce tarba zaiyi masa? Nidai sa kai nayi nafita ina murmushin yarintar da naji haidar din nayi,

Gefen gado nasamu na zauna bayan na kammala dukkan ayyukana kamar yadda nasaba, karkashin pillow na nabankada na ciro wani littafi na hausa wanda marubuciya ummi Aisha ta rubuta mai suna kamar da wasa wanda nake karantawa saboda debe kewa,agefe daya kuma ga radio na yar karama tanayi inda nake sauraron shirin girke girken mako atashar radio tarayya dake nan cikin garin kaduna,

Duk da cewa ina kayatuwa da nishadantuwa da labarin da nake karantawa amma haka na ajiye littafin na tsunduma kogin tunani,

Ko acikin mafarki abaya idan akace min zan samu kaina cikin wannan bakar rayuwar bazan yarda ba,jin rayuwata nakeyi ahalin yanzu tamkar acikin mafarki wai yau nice acikin wannan bakon yanayin sanadiyyar kofofin sadar da zumunta na zamani,bada ban kada nayi sakarkaba ba da tabbas babu abinda zai hanani inyi Allah wadai da wadannan kofofin sada zumuntar domin amafi yawan lokuta sharrinsu da bala'in dake tattare dasu yafi alkhairansu yawa domin nima ata sanadiyyar su nafada kuncin da nake ciki wanda ya haifarwa da rayuwata da ruhina babban tabon da nagagara samun maganinshi haka kuma shine ya jefeni cikin matsalar da narasa mafita har yau dinnan,

Tunanina ne yakatse sakamakon jiyo sallamar Abul khair da nayi kafin daga bisani kamshin turaren sa yasake tabbatar min da zuwan nashi.

Ina nan kwance inda nake naji shigarshi dakin innah kamar yadda yasaba,nikam nasan babu abinda zai kawoshi dakina domin bata ni yakeba abinda ka damu dashi kuwa shine kake tsayawa tsayin daka wurin bashi kulawa gashi ina son ganinsa saboda akwai naganar da nake so zamuyi dashi,

Tsawon kimanin mintuna 20 yashafe acikin dakin inna batare da yafito ba,ina zaune jugum nama kashe radion da nake ji sakamakon son jin fitowarsa haidar yashigo da gudu ya fada kaina kamar dama yasan ina nemansa,dago kansa nayi ina kallonsa,

"Waye yazo haidar?"

Cikin murna da fara'a yace min,

"Daddy....."

Nima murmushi nayi sannan nashafi kansa nace,

"To maza kaje wurinsa idan kaga yafito zai tafi kace ina son yin magana dashi"

Mikewa yasake yi yafita da gudu wanda har sai da gabana yafadi gudun kada ya yanke jiki ya fadi.

Ina jiyo haidar na fada masa sakona lokacin da suka fito daga dakin inna amma sai najiyo yana cewa haidar,

"Kai kada ka dameni sauri nakeyi ana jirana..."

Inna ce tafito tace ai koman saurin da yakeyi yana da kyau yashiga wurina yaji numfashi na kuma yaji matsalata,badan yaso ba yanufo dakin da nake wanda ina iya jiyo duk abunda ke faruwa daga inda nake,

Fuskarshi babu fara'a yashigo yana rikeda hannun haidar yasamu kan stoll ya zauna yana fuskantata,saida nafara gaisheshi ya amsa sama sama sannan nafara sanar dashi makasudin son ganinshi da nakeyi wato maganar saka haidar a makaranta,wani basaraken numfashi yaja ya sauke sannan ya furzar da iskar da ta cika masa hanci ya kalleni idonshi jajur,cikin bacin rai yace,

"Ke meyasa ahar kullum dakikiyace ne? Meyasa sam bakya aiki da tunani? Yanzu fa second term aka shiga taya za akai yaro makaranta?"

Sunkuyar da kaina nayi nace, "Amma Abul khair ai tun first term nafada maka kace baka da kudi abari sai second term..."

Tun kafin inkarasa yamike tsaye yana fadin,

"To yanzun ma banida kudi saboda jiya Monday naje nayiwa najla registration kuma na kashe over 200k banda sauran abubuwan tsarabe tsarabe da na sissiya,sai ku bari sai next year...."

Daga haka yasa kai yafita shida haidar suka barni da baki abude nayi suman zaune,yanzu yar mitsitsiyar yarinyar da ba tafi shekara biyu ba akaje aka kashewa wadannan uban kudaden a makaranta za asata a play group amma haidar gashi nan shida ya isa makarantar shine ba asaka shi ba kuma ba tun yau nake yimasa maganar ba,

Kuka nayi sosai sannan naji sanyi acikin zuciya ta kuma na saka araina washe gari da yardar Allah zan kai haidar makarantar gwamnati wadda ke makotaka da layinmu tunda ubansa yaki sakashi to ni zan sakashi inyaso komai ta fanjama fanjam dan bazan bar rayuwar yarona ta lalace ba abanza yana zaune babu islamiyya babu boko danma duk ina koya masa agida yanzu ya iya 1_100 sannan ya iya ABCD haka duk na koya masa state and capital,a bangaren arabiyya ma babu laifi yasan bakake su alifun ba'un sannan musamman na siyo fawakiha littafin hadisai marassa tsawo nake koya masa domin haidar yarone mai kaifin basira duk abinda na fada masa to ya daukeshi kenan acikin kwakwalwarsa dan ko alqur'ani yanzu yayi izuh daya da rabi.

Saida nagama shakar bacin raina sannan nafito na kama ayyukan rana nan nayi nagama kuma aranar Baffa yadawo wato kakan haidar mahaifin babanshi inda yazo mana da tsaraba mai tarin yawa,

Daren ranar yau kasa bacci nayi kawai ina tunanin rayuwata wadda ke cikin yanayi na tangal tangal yanzu,badan kar nayi sabo ba sai ince wanda ya mutu hakika ya huta domin rayuwar nan wahala gareta babu komai cikinta face gwagwarmaya da fito na fito da wahalhalun rayuwa,dakyar nasamu na dan runtsa zuwa asubah na tashi,

Yau kam na shirya tsaff domin kai yarona makaranta shiyasa ma tunda sanyin safiya na kammala komai bayan na sanarwa su innah,

Agaba nasaka shi muka tafi makarantar bayan su innah sun gama saka mana albarka da ni da haidar din gaba daya tare da yimasa addu'ar dacewa da kuma nasara acikin rayuwarsa......

*_Ummi Shatu_*👌🏻

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now