2

1.5K 136 6
                                    

KUNDIN HASKE

ALKALUMAN MARUBUTA🤝

*💡 HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*

*Wattpad :-AyusherMohd*

TARE DA ALKALAMIN

*Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*MENENE MATSALAR?*

*Babi na Ashirin*

Part 2

  Dayake sun saba da junansu hankali a kwance suka fuskanci juna, duk da ta sha wahala saboda wannan ne karanta na farko na kusantar d’a namiji.

Sosai suke shan soyayyarsu dan Abdul na nuna mata kauna itama haka take kokarin farantamai rai, hankalinta ya kwanta.

Yau wata daya kenan cif dayin auransu, tana kitchen tana karasa wanje kwanukan datai abinci dasu, tana gamawa ta dauko tray din data jera flask na abincinsu ta nufi falo.

Ganin baya falan yasa ta ajiye akasan carpet sannan ta nufi cikin daki, wayarsa ta kalla dake ajiye a gefen gado zuciya ce ta fara rinjayarta akan dauka, dan jiya taji haushin yanda tunda ya dawo aiki yake rike da ita ko hira basuyi ba har sukai bacci.

Daukan wayartai zuciya daya sai dai tana zana pattern din taga wayar na sanar da ita bata xana daidai ba.

Bata kawo komai a ranta ba a lokacin sai dai ta fara kokarin bude wayar bata ankara ba taga wayar ta nuna mata ta kulle sai nan da minti biyar.

Ajiye wayar tai ta fito falo, tana fita Abdul na fitowa, hasken dayaga wayarsa tayi ne yasa ya nufeta.

Ganin abinda ke jikin wayar ne yasa yanayin fuskarsa ya canza tare da kallan kofar dakin, kaya ya saka kawai ya dau wayarsa ya xauna a daki yana dadanawa.

Zahra kam ganin har a wannan lokacin Abdul bai fito ba yasa ta nufi dakin, ganinsa a kishingide yana dana wayarsa fuskarsa dauke da murmushi yasa taji zuciyarta tadan yi zafi, kallansa tai tace “Yallabai ka fito?”

Eh yace ba tare da ya kalleta ba, fuskarta dauke da murmushi tace “ka taso muci abinci.”

Mikewa yai fuskarsa ba wani alamar fara’a ya nufi kofar, murmushi tai tare da sakalo hannunta cikin nasa, cikin salo tace “an fara saida jamb dazu na kira Sani yacemin an fara.”

Kallanta yai yace “oh lokacin yayi?”

Da sauri tace “eh yaushe kake ganin zanyi registration din?”

“Banda kudi yanzu ki jira sai anyi albashi.”

Toh tace hankali a kwance, zama sukai ta zuba musu abinci a babban plate dinsu, shinkafa fa wake da mai dayaji ne ta dauko salad din da yasha hadi ta zuba akai sannan tasa mai spoon dinsa a gefensa dauka yai suka fara ci, yana ci yana dana wayarsa, jefi jefi tana kallansa xuciyarta na kara yin xafi ganin duk maganar data kawomai katse maganar yakeyi, hakan yasata yin shiru har suka gama cin abincin.

Kwanukan ta kwashe tana kitchen tana daurayewa tajishi daga falo yace “na fita.”
Kafin tai wata maganar ma taji an jawo kofar falan.

Haka ta gama wanke wanken abinda suka bata ta fito falo ta zauna ta dau wayarta tana duba group na Matsalolin Mata wanda take ciki tana ganin yanda mata ke fadar matsalolinsu a boye ana kuma basu shawara.

Tana zaune har magrib ta kusa, text ta turamai sai dai ba reply, sake turamai wani text din tai nan ma ba reply hakan yasa ta ajiye wayar kawai ta mike tai wanka tai sallar magrib.

Wata shara sharar rigar bacci ta saka ta shafe jikinta da farar humra tayi kyau sosai duk da ba kyakyawa bace sosai sai dai tanada dirinta sannan intai kwalliya tana fitowa das.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now