Shafi na bakwai

1.2K 105 5
                                    

*KUNDIN HASKE*

    *ALKA'LUMAN MARUBUTAN HASKE*

    *KUNGIYAR:*
        *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
( *home of expert and perfect writers)*

     
   *AL'KALAMIN*
       *SLIMZY* ✍🏼

*RASHIN IYA ZAMA DA SURUKA*

  *BABI NA GOMA*
  *Shafi na bakwai*

*******Yau ake saka ran ganin watan Ramadan,da safe abubakar bayan ya kammala shirinsa tsab sadiya nata karairaya Tana kwarkwasa da yamutse ya mutsen fuska dik Yana Lura da yanayinta Saida ya karya hularsa Yana fesa turare ta Mike da gudu ta shige bayi ta rufo kofa Tana kakarin amai.....

  Bin bayanta yayi da sauri har kofar toilet din ya taba yaji ta rufe bugawa ya shigayi Yana fadin "sadiya!ke sadiya"

  Murmushine ya subuce mata daga cikin bayin sanan tayi kasa da murya a wahalce tace "Abubakar kaje banason kamshin turarenka Dan Allah ka tafi kaga amai nakeyi"

  Jikinsa ne ya Kama rawa take wani tunani ya Fado Masa..."kodai sadiya ciki gareta?domin abokinsa habibu ya taba fada masa matarsa da tanada ciki ko kamshin turare taji Sai tayi amai"...wani sanyin dadine ya lullubesa.

  Jin da sadiya tayi shiru yasa tayi gyaran murya a wahalce "Abubakar ban iya mikewa na galabaita"

  A haukace ya tura kofar Sai yaji ta bude Tana ganin ya shigo ta luuuu zata Fadi ya tarbeta ya sunkuceta tamkar baby yayo parlor da ita ya shimfideta a doguwar kujera....

  Numfashi kawai take saukewa dakyar tace "Abubakar kiramun shukra"fita dakin yayi da sauri yayi dakin innarsa lokacin shukra ta fito sanye da hijabinta Tasha guga kawarta Maryam na jiranta zuwa makaranta,,

  Ko kallon mama beyiba ya shigo a furgice "shukra je sadiya na kiranki batada lafiya amai ta gamayi yanzun ma Ni ina zaton cikine da ita"

  Wani irin kululun bakin cikine ya turnuke shukra da kyar ta hadiyi mugun miyau cikin sanyin murya tace "ya Abubakar C.A test mukeyi a makaranta yanzun haka na makara kaga Maryam jirana takeyi ma"

  "Makaranta tafi lafiyar matata kenan ko shukra Naga take takenki tashen rashin kunya kikeyi dama sadiya na fadamin bakya ganin girmanta to gashi yanzun abun yakai kaina kafin in bude ido ki bace a dakin Nan kije Kiran da takeyi Miki"

  Har ya juya zai fita baiko gaida mama ba itace tadanyi murmushi tace "Abubakar meya samu sadiyar ne?"

Sai lokacin ya juyo ya Sosa Kai "Ina kwana mama?"

  Bata damuba mama ta karba mishi gaisuwar sanan yake fada mata ai amai takeyi mama tace "Allah ya sauwake Kila juna biyu gareta"

  Ba kunya ba tsoron Allah Abubakar yace "haka nake tunani bari inje insamo Wanda zai dubata"ya fice a dakin jikinsa na sassarfa itadai mama murmushi kawai tayi.....

A dakin sadiya shukra na shiga ta rike kugu "lafiya kike nemana?koko wani sabon makircim ne kikeso ki Kara kullawa?wallahi anty sadiya kiji tsoron Allah kin rabamu da yayanmu sirikarki kin shiga tsakaninta da danta ko kofar dakinta baya kallo yanzun gashi kin tsiro da sabon makirci...."

  Dago Kai sadiya tayi Tana hango tahowar Abubakar ta maida Kai Tana numfarfashi ,Aiko shukra na karasa kalmarta ta karshe Sai a kunnensa ya kasheta da Mari Wanda Saida taji kunnenta yayi dummmmm tankar babushi a jikinta ya dago hannu zai Kara Kai mata mama ta shigo dakin da niyyar gaida sadiya....

  Da sauri ta rike hannunsa "haba Abubakar wanan daga hannu da kayi tamkar kana fada da saanka,bedace ka bugeta da hannunka ba"

  A zuciye Abubakar ya Soma zazzaga masifa "dama sadiya Tasha fadamin irin rashin kunyar da shukra keyi Mata ta fadamin kece kike tarewa yau gashi nagani da idona nadade da sanin cewa bakison matata dama to Zan tattarata mubar Miki gidan "

  Fuuuu tamkar zai tashi sama ya wuce bedroom ita kuwa mama poster tayi a tsaye Tana kallon Abubakar nayi mata mugayen kalamai tamkar ba ita ta haufeshiba yadda yadda yadda rufe ido Yana zazzaga Mata masifa,Abubakar danta da ko magana idan zaiyi Mata saiya tsugunna ya sunkuyar da kansa yau shine saboda matarsa yake zazzaga Mata rashin kunya.....

  Sadiya dake kwance Tana numfarfashin karya kuwa dadine ya kasheta tamkar ta tashi ta taka rawa tabbas tasan yanzun Abubakar ya Zama nata burinta ya cika ta farraka tsakaninsa da mama wadda da take tamkar kishiyarta komi yayi Mata Sai itama yayi mata.... Murmushin gefen fuska tayi ta juya baya tabar mama Nan tsaye....

  Ganin haka yasa mama Kama hannun shukra dake zubar hawaye sukayi daki,dakyar mama ta lallashi shukra ta gyara fuskarta suka wuce makaranta itada maryama dake faman jiranta.....

  ******Wanka Abubakar yayi ya shiga kasuwa beko bude shagoba siyayyar kayan azumi yayi sosai sanan ya biya shagon abokinsa dik Wanda ya kalless yasan Yana cikin damuwa habibu abokin Abubakar ne tun suna Yara har suka Gama makaranta tare suka Fara harkar kasuwancin saye da siyarwar waya mangal plaza ko wanne da shagonsa,

  Habibu ya Dan kalli Abubakar ya tambayesa ko lafiya yagansa haka take Abubakar ya shiga fayyacewa habibu komi"abokina kasan takun sakar da sadiya keyiwa mama a baya to yanzun dik ta canja anyi mata nasiha ta bari Amma yanzun mama da shukra Sundau Karan tsana sun dorawa matata Basu kaunarta har shukra rashin kunya takeyi mata mama nagani Bata cewa komi shiyasa na yanke shawarar barin gidan da matata injecan in Kama mata haya Dan bazan dauki su tsanarmim mata ba ai itama tanada iyaye badaga sama ta Fado ba"

  Gyara Zama habibu yayi sanan ya sauke ajiyar zuciya "kada kafara Abubakar domin zakayi babban kuskuren da baka tabayinsa ba a rayuwarka kada kace zaka guji uwarka akan matarka zaka tafka babban kuskuren da zakayi danasani a gaba,kada ka kuskura kadauki maganar mata domin zata kaika ta baro"

  "Habibu kenan dik yadda kake tunani ba haka bane wallahi yanzun maganar da nakeyi maka wallahi sadiya cikine da ita Dan barota nayi a kwance batada lafiya babu Mai taimakonta,shukra mama ta Goya mata baya ta kada Kai tayi makaranta Kuma wallahi  zatasha mamakina Dan wallahi nadaina yi mata komi Dan ubanta tunda batada kunya batada mutunci taje rashin mutuncinta yayi mata"

  "Hakuri zakayi Abubakar abinda nakeso dakai ka rinka bimcike akan dik abinda zakayi kafin ka zartar da hukunci domin Ina guje maka rayuwarman ka guji uwar data haifeka da yan uwanka akan matarka"

  A zuciye Abubakar ya kallesa"dakata malam ba waazi  nazo kayimum ba shawara nazo tunda bazaka baniba shikenan kaga tafiyata"ya Mike yaja kayayyakinsa ya fice habibu ya bishi da kallo ya girgiza Kai...

******Sadiya tunda taga Abubakar ya fita ta gyagije ta cigaba da tsula tsiyarta Dan yan wake wakenta cikin gida da girgije girgije ta fito kenan taji tsayawar mashin dinsa ta Ruga a guje ta shige daki mama dake aiki ta bita da kallo...tayi murmushi,

  A ciki yayi sallama ya shigo tamkar be taba dariya ba hannu Niki Niki da Kaya da kyar ya bude baki yace "barka da gida mama"

  "Barka kadai ka dawo?"

  A dakile ya amsa da "ehh"ya wuce ta bishi da kallo,

  A parlor ya taddata kwance ta dafe Kai Tana numfashi sama sama Tana ganinsa ta fashe da kuka "Abubakar tunda banida Mai kula Dani ka kaini gidanmu kawai,ace banida lafiya babu Mai kulawa Dani"ta fashe da kuka yasa hannu ya janyota jikinsa Yana shafata Yana lallashinta tamkar jaririya Saida tayi shiru sanan yace "Nida wata shawara na yanke bansan ya Zaki dauketa ba"

Dago Kai tayi ta kafeshi da ido alamar Tana saurarensa ya cigaba da magana "da cewa nayi tunda abin ya Zama haka kodai tashi zamuyi a gidan Nan ne?"

  Wani sanyin Dadi ya rufeta jin mgnr tayi tamkar saukar aradu Bata taba tunanin akanta Abubakar zai bar mahaifiyarsaba yadda yake ikirarin son mamansa da yan uwansa yau gashi burinta zai cika saidai bataso hakanba Dan tafiso a cigaba da buga wasan ta Rama dik abinda akayi mata na bakin ciki....

Dago kanta Abubakar yayi "me kikace babyna"

  Kuka ta fashe dashi "Abubakar yanzun idan munbar Nan Ina zamuje su mama fa?kannenka fa?

*Barka da sallah Allah ya amsa Mana ibadunmu*

*SLIMZY😍*

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now