4

1.2K 123 9
                                    

KUNDIN HASKE

ALK'ALUMAN MARUBUTA🤝🏻

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡💡💡

*Wattpad:-Ummishatu*

TARE DA ALK'ALAMIN

*UMMI A'ISHA*👌🏻

*BAK'ON YANAYI...!*❤
  (Kafar sadarwa)

*Babi na Ashirin da d'aya (21)*

*Ita daukaka tamkar rigar aroce ta kan barka a lokacin da taso ko da kai baka shirya barinta ba.*

*4*

   ***D'an numfasawa nayi bayan na dakata daga labarin da nake baiwa harun wanda ya bada hankali da dukkan nutsuwarshi yana saurarena,nasan alla alla yake nazo gabar da yake son ji wato dalili ko makasudin da yasa Abul khair ya juya min baya har ta kaimu ga haka,

Ajiye cup din dake hannunsa yayi wanda baisha ko rabin tea din da na zuba masa ba,

"Anty ya kuma kikayi shiru? Dan Allah ki sanar dani abunda yafaru...."

Hawaye na na share na dan dubeshi sannan nasaki murmushin yak'e wanda bahaushe ke cewa yafi dariya ciwo,daga kaina sama nayi alamar tunani sannan ga hawaye na kwaranya daga idanuwana sannan na dora daga inda na tsaya,naci gaba da fadin,

"Tunda Abul khair yasamu aikin nan yake samun wasu mahaukatan kudi kamar me nan fa muka shiga fantamawa da shanawa cikin daular arziki,

Babu bata lokaci yasiyi wani kantamemen fili yasoma ginawa gini irin na zamani ginin da sai masu uwa agindin murhu acikin gwamnati suke yinsa,lokaci kankani Abul khair ya zama young millionaire,abangaren adalcin da yake yimin kuwa babu abinda ya canja domin ko suttura ya dinka nima yakan dinka min daidai adadin yanda ya dinka,ya gyara gidan iyayensa yayi masa kwaskwarima sannan agefe daya kuma yana cigaba da kera tamfatsetsen gidanshi da yake ginawa mai kama da gidan gwamnati domin wannan gida abun kallone tabbas Abul khair ya debo gidan da zafi,

Kullum a office dinsu cikin fita kasashen ketare da manyan jahohin Nigeria suke,abul khair baya wata guda bai je kasashen ketare ba domin ya samu karbuwa dari bisa dari a ma'aikatar tasu,

Cikin wannan yanayi ranar da bazan taba mantawa ba Abul khair yaje lagos ran gadin wani aiki kamar yadda suka saba koda ya tashi dawowa haka ya lodo mana uwar tsarabar kayan sakawa masu tsadar gaske da kayan jariri domin lokacin inada karamin cikin haidar wanda Abul khair ke jin tamkar yashige Cikin cikina suje suyi rayuwa da abinda ke jikina tare,hatta kulawar da yake bani ta karu akan ta da saboda ina dauke da gudan jininsa acikin cikina,

A wannan tsarabar da yakawo mana hadda wata rantsattsiyar hadaddiyar waya mai masifar tsada kirar kamfanin Samsung,

Tofa zuwan wannan waya shine ya zame mini sanadi kuma ummul aba'isin din tashin hankali na da shigata kunci,

Kasancewar Abul khair bai cika zama agida ba yasashi bude min Facebook account da WhatsApp wanda zan dan rinka shiga ina debe kewa kuma shima ina dan hira dashi koda bama tare duk da shi bai wani cika ma amfani da wayar ba domin aikinsu babu hutu basa samun zaman da zasuyi wadannan abubuwan awaya,

A hakikanin gaskiya nima bawai ina zamane inyita hira da mutane awayar ba kasancewar banida abokan hirar ma amma kuma a Facebook akwai wani group kwaya daya na koyon girke girke wanda nake ciki amma shi mata da maza ne, cikin haka wata rana sai daya daga cikin members din group din tace ta bude wani group na mata zalla a kafar sadarwa ta WhatsApp duk wadda keyi ko take da sha'awar shiga group din to ta ajiye number dinta za asata aciki,banyi k'asa a gwiwa ba nima ba ajiye tawa number din domin dama WhatsApp nakan fi sati daya ban hauba saboda banda abokin hira sai dai ashe dana sani ne zai biyo baya,ashe mafarin tarwatsewar farin cikina ne ke gayyata ta wanda da ace inada masaniyar hakan da wallahi gara ace banda babbar waya har karshen rayuwata domin itace ta zame mini sanad....."

Shiru nayi sakamakon fitowar innah wacce ke fadin,

"Kai harun yau baza kaje kasuwar bane? Ai yakamata katashi saboda rana har tafara yi nasan yanzu baffanku na can yana zuba idon ganinka...."

Badan yasoba ya kalli innah sannan nima ya kalleni amma baiyi magana ba,ganin innah ta juya zuwa cikin daki yasashi yin azamar fadar abinda ke bakinsa,

"Anty.....meya faru bayan shigarki group din? Shin hakan shine dalilin Yaya na wulakantaki har haka?"

Kallonsa nayi da jajayen idanuwa na wadanda ke tsiyayar da ruwa sama sama sannan nace,

"Harun kaga Inna ta fito tayi maka magana to kayi hakuri kaje ka tafi kasuwa insha Allah zakaji wadannan amsoshin tambayoyin naka nan bada jimawa ba"

Haka ya mike jiki asabule yafita cikeda tausayina jin fitarsa yasanya innah sake fitowa inda tazo ta zauna taci gaba da bani baki tana cewa inci gaba da hakuri insha Allah wata rana sai labari.

Haka al'amura suka cigaba da gudana amma har tsawon wasu kwanaki bamu sake zama tare da harun ba bare na karasa masa labarin da nafara bashi koda yake ni dinma a dan wannan tsakankanin ban fiya lafiya ba inata fama da rashin lafiya yau fari gobe tsumma amma abul khair ko arzikin yace min sannu ban samuba sai su innah da harun keta fama dani,tun daga wannan lokaci kuma lafiya tayi min karanci kullum ina kwance jinya tamkar zan mutu duk na kare nafita hayyacina ga ciki wanda yafara girma dan har yacika wata na bakwai Abul khair kuwa ko son ganina ba yayi yanzu,duk na rame nayi wani irin baki hatta gashin kaina ya kade,

Cikin wannan yanayi nakuda ta kamani wadda azahirin gaskiya cikin nawa bawai ya isa haihuwa bane kawai dai inajin wahala ce ta taso min da nakudar domin cikina watansa bakwai,da innah da harun ne suka kaini asibiti acan na haifi yar santaleliyar yata mace mai kamada ubanta sak sai dai yarinyar itama bata da wani kuzari kasancewar bakwaini ce sannan gata yar firit da ita babu girma labo labo da ita,

Nima tunda na haihun kwance nake ana yimin karin ruwa su innah keta kaiwa da kawowa akaina har muka yi kwana biyu amma har lokacin Abul khair baizo ba kuma nasan anfada masa dan tun kafin ayi haihuwar harun ya sanar dashi cewa gashi ankawo ni asibiti zan haihu kuma bayan haihuwar ma harun yasake kiransa yafada masa amma fafur yaki zuwa duk da bacin ran da innah ta nuna na rashin zuwan nasa,

Babu Abul khair babu alamarsa har mukayi kwana hudu acikin na biyar dinne da yamma ina kwance kan gadon da nake jaririyar na cikin gadonta agaban nawa innah da harun da haidar na zaune cikin dakin aka bude kofar dakin aka shigo,wani rantsattsen kamshi ne yafara kawowa hancinmu ziyara sannan ta bayyana cikin wata shegiyar bakar doguwar riga mai mutukar kyau da tsada sai walwali take tana rike da yar yarta najla dukkansu sunsha ado cikin shiga mai kyau fuskarta kuwa sai kyalli takeyi tamkar mudubi,

Ayangance da rashin girmamawa ta gaida su innah sannan tayi musu Allah yaraya abinda aka haifa,da sanina nikam na rufe idanuwa na dan kwata kwata bana kaunar ganin koda mai kamada itane,

Ina jinta ta tako har gaban gadon da nake tana fadin,

"Sannu Radiya yajikin? Ansamu karuwa ko? To Allah ya raya mana...."

Ko bude idanuwa na inkalleta banyi ba bare har takaini ga amsa maganganunta da takeyi wanda nasan babu komai acikinsu face makirci,mungunta da kuma mugun nufi,ina jin lokacin da ta yiwa su innah sallama ta tafi batare da ta ko zauna ba, nikam dauriya kawai nayi wurin rike hawayen dake kokarin fallasa ni ta hanyar zubowa domin kukan zuci nakeyi,

"Mutum....mutum dan Adam abin tsoro hakika wasu mutanen babu komai acikin ransu face bakar mugunta da mugun nufi..."

Washe garin ranar da safe Abul khair yazo kuma aranar muke saka ran cewa za a sallamemu,inata murnar ganinshi amma shikam haka yashigo rannan ahade fuska adaure yasha Ash din shadda mai tsada,baiko bi takan jaririyar da na haifa masa ba dan ko kallonta baiyiba bare insa ran zai dauketa ya miko min wata ninkakkiyar takarda yajuya yafita dama kuma lokacin ni dayace acikin dakin innah tana gida shi kuma harun yaje karbo mana sallama idan har hakan zai yuyu acewarsu gara mu koma gida inyaso ayi mana maganin hausa daga ni har yarinyar domin dukkaninmu bamuda isasshiyar lafiya,

Jujjuya takardar da yabani nashiga yi a hannuna araina ina tunanin to me kuma Abul khair yake nufi ko wani abu yasake faruwa ne? Takardar na zubawa ido domin nasan dukkanin amsoshina wadanda nake bukata suna cikinta,jikina na rawa haka nasoma warware takardar.......

*_Ummi Shatu_*👌🏻

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now