Babi na 11_ Kdeey

2.3K 125 2
                                    

*KUNDIN HASKE*

*AL'KALUMAN MARUBUTAN HASKE*

*Haske writers association*

Babi na goma sha d'aya

*TASKAR: Khadija Ahmad😊*

*RAYUWAR NI 'YA SU*

1)
      Zaune nake bayan d'akin kaka rabi ina gunjin kuka me had'e da sheshshe'ka shin me nayi wa mahaifiyata da tayi ko oho da rayuwa ta anya kuwa ni din d'iyar halal ce ko de tsuntoni tayi ta badani ga baba malam wanda nake yiwa kallon mahaifi, magana nake cikin zuci ba tare da nasan ta fito fili ba kawai se jin tafi nayi a kaina d'ago luhum luhum d'in idanuna nayi karaf cikin na haule aikuwa ta fyalla cikin d'akin Inna rahila tana fad'in
"Inna Inna zo kiji abinda aunty yaya ke fad'a"
Dattijuwar mace tafito baki a ta'be "ya akayi haul..."
Katseta tayi dacewa   cewa take wai baba malam bashine ya haifeta ba kuma ita tsintarta akayi..."

"Ke da Allah ki magana a nutse" cewar sagir daya shigo, hararar gefen Ido ta watsa mai tashiga basu labarin abinda nace kaf,
  Inna rahila taja gud'a tare da doka zani "cass yarinya maganarki hakkun"
Galala yaran suka zuba mata na mujiya fadime da ta shigo tun lokacin da haule ta fara zuba tace
   "Inna bangane hakkun ba?"
  "Kwarai duk abinda ta fad'a' ba 'karya ciki"
Ta banka labule ta fad'a uwar d'aka.
Guntun tsaki sagir yayi ya juya zuwa waje dan jin kiraye kirayen sallah fad'ime ma d'akinsu ta fad'a yayin da haule ta mara wa Inna baya.

***
  "Baba malam nikuwa Idan babu damuwa inaso na had'a yarinyar ka rahinatu data wajena su zana jarabawar shiga jami'a wacce za'ayi nan da watanni biyu masu zuwa"

Murmushin jindadi baba malam yayi ya dora da cewa
"To Alhamdulillah, Alhaji wannan magana taka ta faranta min kwarai babu abinda zance se fatan Allah ya jikan mahaifa Allah kuma ya biya bukatu, Alhaji ni mutum ne me son karatu sosai bare karatun d'iya mace dake dede da karantar da al'umma"

"Hakane, amin nagode kwarai Allah ya raya zuri'a, d'azu kuwa naga sirikinka wannan.."
  "Wanne kenan?"
"Yaron medala"
"Af yaje ta wajenku kenan"
"Eh sunzo siyan kayan gini"
"Allah sarki hakane dake kasan mahaifin nasa ke ginin estate"
"Oh Allah sarki, to ni Bari na koma a gaida su Inna, na barka lafiya, ga wannan kasa kati"
"Alhaji baka gajiya, to madallah Allah yayi albarka" bin bayan alhaji kabiru yayi da ido yana me jinjinawa karamci irin na mutumin kafin ya zira kudin cikin aljihun wando ya shiga gida da sallama dede lokacin Abdullahi ya shigo hannunsa rike da takalman ball kallonsa baba malam yayi had'e da girgiza kai a zuciyarsa yana mamakin matasan  yacce suke kwasar kafafu su tafi ball tun bayan la'asar ba za su dawo ba kuma se ana sallah wanda da kunnensa yasha jin ana magana a unguwa kan hakan gashi ko masallacin kofar gidan nasu se su kwashi kwanaki kan su shiga.

***
Bandaki na shiga na wanke fuskata na dauro alwala bayan na fito na bude lokar kayana na zari hijab nayi sallah ko da na idar se na shiga karatun qur'ani kamar ko yaushe sallamar Ahmad naji Yana cewa aunty yaya wai kizo inji babanmu. Se da nakai aya na maida qur'anin mazauninshi na linke sallayar na nufi falon babanmu dake kwayayen fitulun sun mutu saura guda daya se yazamana falon da duhu sallama nayi a nutse bayan an bani izini na shiga tsugunnawa nayi "barka da dare babanmu"
Bece dani tatafar ba se ma daukar remote yayi ya rage karar labaran NTA da yake kallo, jikina yayi sanyi inaji ya shiga kwalawa Abdullahi kira aikuwa se gashi ya leko ta dakinsu baba malam gani dauko bulala kazo  yanzu"
  Tuni jikina ya shiga rawa har bansan lokacin da hawaye ya ballemin ba saukar duka a jikina shi ya dawo dani cikin hankali na, hankali tashe na bud'e baki zanyi magana naji fau fau fau tuni jikina ya saki na fad'i daga can nesa Ina iya jiyo muryar kaka rabi tana cewa "kai Abdullahi uwaka Ibrahim ashe baka hankali bansani ba kasheta zakuyi...." Duff naji komai ya daukemin.

    Ruwan dake kwarara cikin jikina yasa ni tashi a firgice Ina sakin atishawa hakwarana nata harhaduwa da junansu ga wani zugi da jikina kemin a hankali na d'ago kaina karaf na hangoni jikin mirror jikina ko ina shatin bulala ne kwace daga can Ina jiyo hayaniya a falon baba malam muryarsa a sama yana cewa
  "Banda ita yar iska ce dan ta tambayeni kudi nace mezatayi dashi shine zatace wai bana sonta kuma ko tsintarta akayi..."
  "To baka ganin yarinya ce dududu rahinatu tafi shekara ashirin"

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now