5

1.6K 142 8
                                    

*KUNDIN HASKE*
          
        Al’kaluman marubata

   KUNGIYAR:-
HASKE WRITERS ASSOCIATION
(home of expert and perfect writers)

*TARE DA AL KALAMIN*

*ZEE YABOUR*

*BABI NA GOMA SHA BAKWAI*

   ......MABUD'IN WAHALA

*06*
*Last page*

   Biki nata matsowa kowanne b'angare na shirin biki, B'angaren Nurah da Sameerah ba wani shiri suke ba, walima kad'ai za'ayi albarka suke nema, dan duk bikin da akayi kid'e kid'e Allah ya tsine masa kuma ba zai yi albarka ba.

     Rahma da Lukman planning grand biki suke wanda zai zama abun magana a gari da fad'in Nigeria gaba d'aya, komai Lukman zai yi, hatta kayan fitar biki shi ya mata akwati biyu.

    Sameerah gyaran jiki sosai Umman ta ta saka ana mata, Da bata dukkan abunda zai gyarata ya siya mata martaba wurin mijin ta, bata gaza wurin bata shawarwarin iya zama da miji, da nasiha akan zaman aure.

     *Rana bata k'arya*
Ranar laraba aka fara bikin su, Yan' uwa na kusa da nesa duk sunzo, Bikin ya kasu kashi biyu, Na Sameerah daban, Na Rahma daban,

   Da safe akayi sa lalle, Da rana Rahma tayi bridal shower tare da k'awayenta, Sameerah kam kwanciyarta tayi kuryar d'akin Umman ta, Yan'uwa duka suna sashen Gwaggo ana damawa dasu, Dangin Mahaifiyarta ne kad'ai a sashen su.

      "Halin dangin mijin ki na bani mamaki", Cewar Aunty Habiba k'anwar Umma, Umma tace " Hmm duniya ce ke rud'in su", "Gaskiya Allah ya musu kwad'ayi, kiga yadda suka juya baya saboda kawai mijin Rahma nada kud'i", Cewar Aunty Raliya Yayar Umma, " Duniyar ce ta lalace sai kana dashi ake yi dakai", Umma ta fad'a, Aunty Habiba tace "Allah yasa mu dace", Suka amsa da " Amin", Aunty Raliya ta k'ara da "Dan ma Allah yasa Sameerah nada hankali, ai da sai ta shiga damuwa", " Wallahi kuwa", Cewar Aunty Habiba, "In Shaa Allahu sai ta samu farin ciki a gidan mijinta fiye da zaton mai tunani", " Da Yardar Allah kuwa"

    Sameerah na jiyo su daga d'aki ta amsa da "Allah Amin", Burin ta kenan a ko da yaushe.

   Anyi biki lafiya, Sameerah sunyi walimar su wacce addini ta yarda da ita, Yan'uwa Nurah sunzo tamkar su had'iyeta kowa so yake yayi hoto da ita.

     Rahma ansha bukukuwa, sunyi Dinner ta gani ta fad'a, kaf dangin babu wanda aka tab'a ma biki irin nata, Yan'uwa kowa so yake ya rab'eta, Ta kwashi rawa a gaban iyayensa da kowa, basu ga laifin ta dama Yan boko, Gaba d'aya Zaria da Kaduna da wasu garuruwan maganar bikinsu ake, anata posting a social media, Abunda Rahma ke so kenan tana ta jin dad'i, da k'ara jin kanta on top, da ganin tafi kowa sa'a.

    Ranar asabar aka d'aura aure, Manyan mutane sun halarta ciki hadda gwamna, kar ku so kuga bakin Gwaggo da Rahma, sai k'ara fankama suke.

     " Mukam sai hamdala da godiya, zuciyar mu fara tas, bama hassada da bak'in ciki shiyasa alkhairi ke bin mu, d'aurin auren ya'ta hadda gwamna", Gwaggo ta fad'a wanda da Umma take, Tayi tamkar bata ji ta ba, Aunty Habiba ce ta kasa hak'uri tace "Shi arzik'i ai ba anan yake ba",

    Gwaggo ta mik'e cike da fad'a tace " Ke kuma dawa kike?", "Da wanda ya tsargu", " Hassadar ta kasa b'oyuwa kenan, toh wallahi nan gani nan bari dukiyar uban wani", Aunty Habiba ta tuntsire da dariya tace "Ina abun da za'ayi muku hassadar", Nan fad'a ya kacame tsakaninmu, Kowa yace ai Aunty Habiba ce bata da gaskiya, Aiko ta musu tass tace Dole suce bata da gaskiya tunda suna kwad'ayin abunda za'a Sam musu, Duk yawansu tak'i shiru, Ganin tana da baki sosai, Kowa yaja bakinsa.

    Da daddare aka fara shirin kai Amare, Motoci kusan goma masu azabar kyau suka zo daga gidansu Lukman, kowa ya dinga tururuwar shiga, kowacce burinta taje taga yadda gidan yake, ba wanda ya damu da ganin gidan Sameerah, sun san ba abun arzik'i za'a zuba ba.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now