Babi na 21- Ummy Aysher

1.7K 136 6
                                    

KUNDIN HASKE

ALK'ALUMAN MARUBUTA🤝🏻
 
💡 *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

*Wattpad:-Ummishatu*

TARE DA ALK'ALAMIN

*UMMI A'ISHA*👌🏻

*BAK'ON YANAYI....!*❤
    (Kafar sadarwa)

*Babi na Ashirin da d'aya (21)*

بسم الله الرحمن الرحيم

*Wannan dan takaitaccen labari sadaukarwa ne ga uwa mabada mama aljannah mai masoya da yawa,bishiyar kan hanya kowa ya rabeki sai yasha inuwa,wato k'ungiyar haske,hakika dan halak baya manta alkhairi Allah yaci gaba da yimiki jagoranci tare da tsareki daga sharrin duk wani mai sharri keda jama'ar cikinki,iya wuya ana tare.*😘

*1*

     ***"Kafafen sada zumunta wadanda ake yiwa lak'abi da social media aturance hanyoyi ne masu mutukar karfi wurin taimako dan sadar da zumunci da kuma samun nishadi,sai dai nikam agareni sun zama iftila'i da kuma tushe na bakin cikina haka kuma sun zama ummul aba'isin na jefani cikin masifar rayuwar da nake ciki ahalin yanzu,tabbas zanso kowacce mace ta san labarina ko dan gujewa fadawa yanayin da na fada",

Wani guntun tsaki naja ina kore sauron da keta faman yimin kuka acikin kunne tun mintuna biyar da suka gabata,tashi zaune nayi na janyo kwalin maganin sauro na kunna sannan najuya na kalli haidar wanda keta sharar bacci duk da koke koken da sauro keyi,firfita naci gaba da yimasa ina shafar sumar kansa domin ina jin kaunar yaron nan har cikin raina kuma hakan baya rasa nasaba da irin tsantsar soyayyar da nake yiwa mahaifinsa,

D'an tsagaitawa nayi da abinda nakeyi sakamakon bugun kofar da naji anayi afalo tabbas shine ko tantama banayi domin bugun kofarshi daban yake kasancewar yana gudanar da komai cikin yanga da jan aji,nasan abinda ya kawoshi shiyasa nayi hanzarin dauko yar kwalbar farar humra ta dake ajiye gaban mudubi na bi dukkan sassa da lungu na jikina na shasshafa yayinda shi kuma keci gaba da munafikin bugun da yake yi bai fasa ba,

Cikin sanda na dauki yar wayata wadda na kunna fitilar dake jikinta wadda haskenta dashi ne nake amfani tun bayan da nepa suka dauke wuta,

Ahankali nake sadadawa gudun kada innah taji dan sam bana son taji shigowarshi,jin alamun zan bude kofar yasashi daina bugun da yakeyi,ko kallo na baiyi ba yawuce ciki bayan na bude masa kofar,kai tsaye dakina yawuce yayinda nikuma na tsaya na maida kofar falon na rufe kamar yadda take afarko,

Abakin gadona na sameshi zaune yana shan kamshi,zama nayi can nesa dashi ina kallonsa,kamar koda yaushe kyakkyawar fuskarshi daure take wanda har kana iya hango bacin ran dake kwance saman fuskar tashi amma hakan baiyi wa kyansa nakasu ba haka kuma bai samu damar dakushe kyawun fuskar tashi ba, "Abul khairi kenan" shine abinda nafada acikin raina domin nasan abinda yakawo shi wanda adayan biyune zuwa uku imma matarshi tayi tafiya ne ko kuma sunyi fada ta hanashi kanta ko kuma bata da lafiya tana lalurar mu ta mata,

"Zo ki dauke haidar daga nan ki sauya masa wuri...."

Shiru nayi batare da na motsa ba kuma har lokacin idona na kanshi kurr,

"Meye kika zuba min ido kamar baki taba ganina ba? Ni ba zama yakawo niba idan kuma bazaki baniba intashi intafi...." Yafada cikin rashin walwala yana mai sake bata fuska,cikin murmushi na kalleshi nace,

"Wane ni inhana mai kaya kayansa,ai kayanka ne sai yanda kaso zakayi dashi..."

Bai tanka ba dan haka natashi naje na yiwa haidar shimfida can kasa nesa da gadona sannan nadawo na zauna a inda nake zaune da bayan na kashe wayar hannuna wadda agogonta yanuna karfe goma sha biyu nadare saura wasu yan mintuna,

Duk da ba wata soyayya ya nuna min a lokacin ba hakan bai hana tsumin soyayyar shi dake cikin zuciya ta motsawa ba shikam sam ba burgeni ne agabansa ba a'a biyan bukatar sa kawai yake nema wadda da zarar yasamu to zai zargawa karensa igiya yakara gaba,

Hakan kuwa akayi domin bayan kammaluwar komai bai kara ko minti goma ajikin dakin ba numfashinsa na daidaita yamayar da kayansa batare da yasake bi takaina ba yawuce yafita daga cikin dakin,tsawon wasu yan mintoci ina kwance daga bisani natashi nafita naje narufe kofa nasake dawowa na dan kishingida wai azuwan in dan huta sai intashi intsarkake jikina tunda naga lokacin ba afi karfe daya da rabi ba,tunanin Abul khair naketa yi wanda shi ko tsoron dare bayayi duk ranar da matarshi bata nan ko aka samu matsala komai nisan dare shikuma gashi jarababbe haka zai yanko daren yazo gareni,murmushi nayi na  rungume hannaye na akirjina ina jin wata sabuwar kaunarsa tana mamayar dukkanin wata mugudanar jini dake jikina da tunaninsa bacci yayi nasarar yin gaba dani wanda bani na farka ba sai misalin karfe 7 nasafe.

Cikin rashin jin dadin wannan bacci da nayi natashi ina kallon inda haidar yake kwance har lokacin bai tashi ba shima baccinsa yaketa yi babu takura,hijabi nasa na lallaba nafita falo domin acan bandaki yake yana girke tsakiyar dakina da na innah wadanda ke kallon juna,

Ni inbanda jiya ma yaushe rabon da inkwana da janaba ajikina,sam bana wannan sakacin kullum da zarar anyi abinda akayi yana tafiya nake zuwa in tsarkake jikina shikam sai yakoma gidansa yakeyi,to abinma da ba koda yaushe yake zuwa ba,wani sa',ilin sai yafi watanni biyu baizo min ba idan suna yar dadi da matar tasa sai ansamu matsala ni ake nemana wanda hakan ba karamin ciwo yake yimin ba amma duk da haka wai dan tsabar rashin wayo da rashin zuciya gamida rashin azancin dabara kullum zuciyata cikin bege da kaunarshi take,

Wasu hawaye masu zafi na goge bayan na kammala wankan sakamakon tunowa da rayuwar baya da nayi wato shekaru biyu da suka gabata kafin na samu kaina cikin wannan wahalalliyar rayuwar marar 'yanci marar dadin gudanarwa,

Cak naja na tsaya sakamakon ganin innah da nayi tana rike da carbinta ta bude kofar falo tashigo,bata yimin magana ba tawuce cikin dakinta nikuma jikina kamar anzare min laka haka na wuce nawa dakin duk irin bata bakin da inna keyi wurin yimin kashedin nadaina bari Abul khair yana zuwa yana kebancewa dani tunda banda daraja a idonshi yatashi abanza,haka nidai nayi salla cikin rashin kuzari tamkar kazar da kwai ya fashewa aciki,

Haidar naje nayiwa wanka bayan yatashi dan nikam na gagara shiga dakin innah gaisheta domin nasan tagane cewa Abul khair yazo daren jiya,

Sai bayan da nagama shirya haidar na je na hada abun karyawa sannan nashiga dakin inna na sameta zaune itada haidar tana tayashi wasan da yakeyi da tulin uban kayan wasanshi wanda Rahinatu kanwar abbanshi ta siyo masa watanni hudu da suka shude,

Tamkar munafukar da tazo daukar darasi haka na gurfana na zuba gwiwowina gaban innah kaina akasa na kasa dagowa,

"Inna ina kwana...?" Nafada cikin sanyin muryata,

"Lafiya lau 'yarnan....ya kwanan mai gidan nawa?"

Murmushi nayi na kalli haidar wanda ke saman cinyarta yanata wasanshi dan dama haka take kiransa dashi nima kuma bata fadin sunana dalilin Abul khair shine babban danta shima ba kiran sunanshi takeyi ba sai dai tace wannan yaron,

Yunkurawa nayi na mike zan fita bayan na ajiye mata kayan karin kumallon nata amma sai ta dakatar dani ta hanyar fadin,

"Zo ina son magana dake yar nan..."

Komawa nayi na sake durkusawa ina rarraba idanuwa kamar wacce tayiwa sarki karya.........

*_Ummi Shatu_*👌🏻

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now