14

1.3K 122 20
                                    

*KUNDIN HASKE*

*Al-K'aluman* *Marubuta*

KUNGIYAR:-

*HASKE WRITER'S* *ASSOCIATION* ( _Home of expert and_ _perfect writer's_ )

*BABI NA GOMA* *SHA BIYAR*

*KWAD'AYIN* *WASU IYAYEN.......*

_Tareda Alk'alamin_

*Ayshat D'ansabo lemu*🖊

1⃣4⃣

A kujeran dake kusa da Matarsa yazauna fuskan sa d'auke da mad'aukakin murmushi yake fad'in

"Marabanku Aliyu yaudai gani ga Amarya tubarkallah masha Allah "

Alhaji sarki ya k'are mgn idanunsa akan Nadeeya dake murmushi kafin ta bud'i baki tagaidashi ya amsa cikeda harka

Daganan hira suka fara da Aliyu inda Hajiya Ramla tayi anfani da hakan ta janye Nadeeya zuwa bedroom d'inta dake down stair's

Ahankali take janta da hira tareda nasihohi masu kashe jiki , lokaci guda Nadeeya ta yaba da karamci da mutuncin Hajiya Ramla , abnd yafaru adaren jiya da Aliyu yashiga dawo mata har zuwa lokacin zuciyanta na cikeda tsoro da firgici idn ta tuna yadda Aliyu yayi anfani da karfinsa ya biya buk'ata da ita ta haramtacciyar hanya, tamkar ta gayawa Hajiya Ramla damuwanta sai kuma tadanne abn azuciyanta sbd girman laifin daya aikata d'in

Sunjima sosai agdn don sai byn la'asar ya d'auke ta suka koma gd , shima ajeta kawai yayi tajuya batare daya shiga cikin gdn ba ,

Tuni masu yi mata aiki har zuwa girki sun fara hada-hadan shirya abncin da zaaci na dare , koda Nadeeya ta shiga kaman koyaushe takan shiga ta duba yadda abubuwa ke tafiya , sannu tai musu ta duba komi yayi mata falo takoma ta kunna kallo wanda gaba d'aya hankalinta baya ga TV d'in azahiri ta lula duniyar tunani

Ruk'ayyah ce ta fado ranta tana ayyana itakuma ko wace wainan take toyawa a gdn Kamal d'in? Tunda basu tab'a haduwa tunda sukai auren sai dai waya kawai , ganin tunani nason damunta yasata shiga WhatsApp domin debe mata kewa idn tayi hira da frnds d'in ta

*

A Paris kuwa koda suka sauka wani abokin Kamal jan fatane yazo d'aukan su a airport d'in zuwa k'ayataccen Hotel d'in dazasuyi masauki , tun suna hanya Ruk'ayyah ke sauraren yadda Johnson keta yabata , Kamal ko sai wani murna yake tamkar wani soyayya sukeyi da Ruk'ayyah

Koda suka isa masaukin su bak'aramin k'ayatar da Ruky Hotel d'in yayi ba tabbas ya yadda waje wajen ne ,d'akin daya kama kansa tasan sai yara masu jida naira wanda suka isa sannan

Single room ne mai d'auke da tafkeken bed dakomi na alfarma , sai toilet da corridor daya raba tsakani shiya fara shiga yai wanka yafito sanye da rigan wanka ajikinsa

Ruk'ayyah ya duba wacce take zaune bisa bed d'in, agajiye take matuk'a sbd wannan ne karon farko data fara tafiya harta bar kasarta ta haihuwa , kamal ne ya furta

"Hey! Babe shiga kiwanka ko kafin inmana order d'in abnci , kudaina wani sumi-sumi nazo dakene domin inhuta da albarkatun jikinki da kyau , bana buk'atan duk wani qauyanci da wani face da kikeyi "

Yakare mgn yana isa bakin bed d'in yafara kok'arin bud'e trolley d'in sa domin fito da kayan sa , itakuma Ruky ta mike jiki asanyaye ta shige bathroom d'in daya fito wanka tayi da alwala ta fito d'aure da babban towel wanda a bathroom d'in suke sabbi fil tazari guda

D'auke kai tayi tamkar batasan yana d'akin ba , shikam tunda ta fito mayun idanunsa nakanta ne yana karemata kallo

Zama tayi tana bud'e trolley d'in data zubo kayanta ta ciro mai tafara shafawa, byn tagama ne ta zari wata doguwar riga takoma bathroom d'in tasanyà ta fito lokacin shima ya shirya cikin k'ananun kaya yana kokarin d'aukan phone's din'sa ta fito

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now