10

1.9K 213 38
                                    

KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association💡

(Home of Experts and perfect Writer's)

*SANADIN K'AWA*

NA

*khaleesat Haiydar*

BABI NA GOMA SHA HUDU


10

A hankali Ammi ta mike tana kallon ta, Fatima ta kasa kallon inda mahaifiyarta take har ta iso kusa da ita ta juyo da ita a sanyaye tace "Fatima" sai a sannan fatima ta kalleta hawaye na sakko mata tace "Na'am" Ammi da ita ma hawayen farin ciki ya cika idonta tace "Alhmdllh, Allah mun gode maka" Xubewa nan kasa fatima tayi cikin rawar murya tace "Ki yafe min don Allah Ammi, I've failed u plenty times kiyi hakuri Ammi I have learnt my lesson" Ammi ta dago ta suka shiga dakin ta ta xaunar da ita ta goge hawayen idonta tace "Tel me what happened daughter kar ki boye min komai" shiru fatima tayi ta hadiye wani abu da ya tsaya mata a rai, is she to tel her mum that she went to Elbasheer's house and was raped by him? Ta girgixa kai hawaye na sakko mata tace "Noo" Ammi da ita ma hawayen ke xubo mata tace "No what, ki gaya min me ya faru ina kika je?" Ja baya fatima tayi don bata san abinda tace ya fito fili ba, Ammi ta kwantar da murya tace "kada ki ji komai Amira, tell me everything I am ur mother" gyada kai tayi da kyar tace "Husnah ce ta sa in je gidansu wani Instagram frnd dina Ammi, I....i never knew him...." Kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka sosai tace "Don Allah don annabi Ammi kiyi hakuri" Ammi da lkci daya jikinta yyi sanyi ta dake tace "Ina jin ki" Cikin rawar murya Fatima ta ci gaba da gaya ma.mahaifiyarta abinda ya faru daga fari har karshe, bbu kuma abinda ta boye mata, ganin irin kallon da Ammi ke yi mata ta kasa ci gaba ta dinga kuka kamar an aikota, cike da karfin hali Ammi tace "Go on" ta hade kanta da gwiwa tace "Ni ban san abinda ya watsa min ba Ammi kawai na daina jin komai na daina ganin komai" Ammi da idonta ya sauya launi ta kasa cewa komai, tana shessheka ta ci gaba tace "Ban san abinda ya min ba Ammi, kawai dai har yanxu kaina na min ciwo har da cinyana" ta fadi hakan tana bude lap dinta, kusan waje biyu ne yyi ja a cinyar nata, Ammi bata iya tace komai ba sai hawaye da take sosai, can tace "Waye ya fita gidan nan yanxu?" Gaban fatima ya fadi ba kadan ba ta rasa abinda xata ce, da kyar ta nemo abun cewa cikin rawar murya tace "Shine ya gan ni a hanya ya dawo da ni gida" Ammi ta mike tana mata wani kallo tace "Ba baki nake maki ba Amira, amma ke kam kinyi hasara kin cuce kanki kin yaudara kanki, saboda bin umarnin k'awa kika je kika yasar da mutuncin ki a titi, kuma in dai ni Amina ina numfashi baxan taba barin a cuce Umar ba, wllh yafi karfin ki nesa ba kusa ba ynxu yanxu, don haka maxa ki san inda dare yyi maki" Ammi na kai wa nan ta fita daga dakin. Har magrib fatima bata daina kukan da take ba a dakinsu, duk taji ta tsane kanta, ta tsani Elbash, ta tsani Husnah, ji take kamar a dauke ranta ta huta, a haka Umar ya shigo gidan, da da ne Ammi xata ce ya shiga ya dubata amma yau bata yi masa tayin hakan ba har ya gama xamansa tsakar gida tare da ita suna hira jefi jefi kafin ya bar gidan shi ma duk a sanyaye yake rashin ganin fatiman. Washegari da xaxxabi sosai ta tashi ga kanta dake mata axaba kamar xae tsage har lkcn kuma sai dai bata tashi ba amma tana tashi sai jiri ya kusa kwasheta, har rana ko leko dakin Ammi bata yi ba, da kyar tayi karfin halin fita ta yi wanka ta wanke baki ta dauro alwala ta koma daki tayi sallah, xuwa yamma banda rawar sanyi bbu abinda take, Ummi ta shigo tace ana kiranta a waje, Hijab kadai ta iya xurawa kan xani da ves dake jikinta tayi karfin halin fitowa tsakar gida, Xaune yake kan tabarmar dake a shimfide ya tankwashe kafa, fararen hannunsa rike da makulin mota yana jujjuyawa, tun da ta fito yake kallon ta ko kiftawa babu, Ammi dake bakin murhu tana duba girkinta ko kallon Inda take bata yi ba ta mike ta nufi daki, ita kam tsaye tayi bakin kofa xuciyarta na bugawa ga wani jiri da take ji na neman kada ta tun da ta kallesa sau daya bata sake kallon inda yake ba, ita dai ta shiga uku, me kuma ya sake dawowa yi, tunanin hakan yasa hawaye cika idonta, what did this man still want from her? Elbash ya juya ya ga har Ammi ta shiga daki, lkci daya ya mike ya nufeta, kawai ganinsa tayi gabanta, bbu abinda ya taho memory dinta sai ranan da ta fara ganinsa a gabanta a can gidansa sai take ga kamar abinda ya faru ranan ne xai sake maimaita kansa, bai ankaraba sai gani yyi ta yanke jiki tun kan ta kai kasa yyi saurin rikota yana mata kallon mamaki, Kan tabarma ya ajiye ta ya nufi buta da ya gani ya dauko ya debi ruwan ya shafa mata a fuska, a hankali ta bude ido ta mike xaune da sauri ta takure waje daya jikinta na rawa tace "Kayi hakuri plss, stay away from me am begging you" bai ce komai ba, ita kam har lkcn jikinta bari yake, ya fi minti daya yana kallonta kafin ya mike, dai dai fitowar Ammi, yayi kasa da murya yace "Mama tana xaxxabi ne sosai ko xa mu je asibiti" Ammi tace "A'a daxu likita ya xo duba ta ai" yyi shiru kafin yace "Faduwa tayi yanxu, da dai muje asibitin" Da alama Ammi bata son musu da shi don daga karshe ce masa tayi toh,  tare da Ummi suka wuce asibitin, ita dai fatima har lkcn a tsorace take har suka isa wani asibitin kudi, ya juya yana kallonta fuska daure don da kyar ta yrda suka taho, hawaye ya cika idonta tace "Don Allah kayi hakuri nasan allura xa a ce xa min, ni kuma ina tsoro, am fine pls" tun da ta fara magana idonsa ke kanta, ta sa hannu tana share hawayen idonta, yace "Amma ranan da na maki can gida baki samu bakin cewa ba kya so ba" da sauri ta kallesa, ya hade girar sama da ta kasa yace "Ina ke maki ciwo yanxu?" girgixa kai tayi tace "Ba ko ina" yana kkrin bude kofa yace "Okay to mu je su dubaki" tace "A'a don Allah kayi hakuri" ya juyo yace "Then tell me what's making u sick" tana goge idonta a hankali ta hade hannayenta biyu tace "I want you to stay away from me pls, kar ka sake xuwa gidanmu ina hada ka da girman Allah" muryarta na rawa ta kare maganan, yyi shiru yana kallonta, ta hade kanta da gwiwa tana kuka a hankali, bai ce komai ba ya tada motar ya fita harabar asibitin, wani babban pharmacy ya nufa, ya siya mata drugs sannan ya dau hanyar gidansu, suna isa kofar gida ya kalli Ummi dake bayan mota yace "Ya sunanki" tana wasa da yatsunta tace "Ummi" yyi murmushi yace "Wani class kike?" Tace "Primary 6" yace "Good" ledan maganin ya mika mata ya ciro dubu daya ya kara bata yace "Kai mata maganin gida, wnn kuma ki siya biscuit" maganin kadai ta karba yace "Take the money" still bata karba ba ya kamo hannunta ya sa mata sannan ya ce "To shiga gida" ba musu ta bude motar ta fita, Fatima xata fita ita ma ya rikota, juyowa tayi tana kallonsa, sosai gabanta ya fadi, tayi saurin sauke idonta ta warce hannunta daga nasa, dage glass din motar yayi, a tsorace ta xaro ido tace "A'a don Allah ka bude min in fita plss ka bude" har lkcn yana kallon kwayar idonta yace "Me yasa xan daina xuwa gidan ku?" Ta hadiye abu da kyar tace "Aa toh ka dinga xuwa" murmushin da ya bayyana beauty point dinsa yyi ya kamo hannunta a hankali yace "Ke kika nuna min hanyar gidan naku ai kuma xa ki ce in daina xuwa" ta ki daga kanta, ta kwace hannunta a hankali, shiru yyi na kusan minti daya yana kallonta, jin shirun yyi yawa ta dago tana kallonsa, shafa beard dinsa yyi yace "What exactly is making you still sad?" Bata fuska tayi sai kuma ta fashe masa da kuka, da mamaki yake kallonta, muryarta na rawa a hankali tace "You took away my pride, you raped me" kallonta Kawai yake kafin yace "You brought the pride to my door step, ke kika kawo min kanki har gida" hade kanta tayi da gwiwa tana kuka sosai, sai da tayi me isarta ta dago ta rike kofar motar cikin rawar murya tace "Ka bude min" bude lock din yyi ta bude motar ta fita, ya bi ta da ido har ta shiga gida.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now