Shafi na hudu

1.5K 132 4
                                    

*KUNDIN HASKE*

*Haske Writer's Association*💡

(Home of Experts and perfect Writer's)

   *RAYUWAR WASU MA'AURATA...*

  *NA*

*UMMU BASHEER*



*Babi na goma sha uku*


Page 5

....Da karfi ya rike Mata gashi yayin da wasu hawaye ke zubo Mata. 

"Uban ki ne ya siya min wayar? "

Ya kara daka Mata tsawa "nace ki fad'a min uban ki ne ya siya min wayar.  Daga nace dauko min waya sai ki yar ya fashe "

Cikin kuka tace"Jiri ne ya dauke ni  shine wayar ta fad'i.  Ba da gangar nayi ba"

Ture ta yayi ta fad'i a jikin gado har ta buge a goshin nan da nan sai gurin ya fara fitar da jini.

Ko a jikin shi sai ma zagi da ya bita dashi ya bar Dakin.

A rud'e ta shiga bayi ta wanke gurin da kyar jinin ya tsaya domin ta bugu sosai.

Zama tayi ta rusa kuka.  Ta dade tana kuka sannan ta tashi ta koma parlour.

Washegari da safe

Bayan ta gama duk aikin gidan ta tana hada lunch domin yau ta kasance Saturday . 

Jin knocking tayi nan ta Isa kofar ta bude.  Mommy ce mahaifiyar Safwan.  Nan tayi Mata barka da zuwa ta shigo ciki.

Zama tayi suka gaisa.  Mommy ta amsa Mata cikin sakin fuska.

Ganin ciwo a goshin ta . Sai ta tambaye ta Meye ya same ta?.

"Na zame ne a toilet "

"Allah ya kara kiyayewa.  Ina fatan lafiya kike zaune da mijin naki.  Naga duk kin rame ne.  Meke damun ki?"

Murmushi tayi cikin boye damuwar ta "Ba komai Mommy "

"Ki dauke ni a matsayin mahaifiyar ki.  Ki fad'a min ko akwai abinda Safwan ke miki.  Ki sani duk yanda muke son shi ba zamu so yayi abinda ba daidai bane "

"Mommy Allah babu komai "

"Tohm Shikenan Allah ya kara hada kan ku"

Nan taje ta Kira Safwan dake Ta faman barci.  Da farko zai balbale ta massifa ne ta tashe shi . Sai tace mai Mommy tazo sai yayi mukus.

Mommy bata dade ba ta tafi Bayan tayi musu Nasiha Wanda ya kashe ma Husnah jiki.  Yayin da Safwan ko a jikin shi.

********************

"Innalillahi wa'ina ilaihir raji'un " Abinda Layla Ke furtawa kenan a ranta domin ba karamin cikin tashin hankali take ba.

Lalai Mami ta dage sai da aka sa ma Rayyan ranar aure da wata Hameeda yarinyar kawar ta.

Kuka take yi sosai a gaban Rayyan Wanda ya rasa ya zaiyi shima kamar yayi kukan.  Yayi rarashin har ya gaji.  Domin kunsan mu Mata da kishi.

Biki saura sati daya

Mami sai farin ciki take.  Abubuwa dayawa tana yi ne dan Layla taji haushi.  Anan cikin gidan dama akwai wani flat Dan gidan babba ne.  Aka gyara nan Hameeda zata zauna.

Nasiha sosai yan uwan Layla sukayi Mata.  Sannan Rayyan ma ko yaushe Yana cikin kwantar Mata da hankali.  Set din akwati biyu yayi Mata.  Amma bai bari Mami taga daya ba. Dan dayan ma saida tayi fad'a wai na Layla yafi na Amaryan kyau   shi dai hakuri Ya bata kawai.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now