Babi na 5_Miss Zozo

2.8K 224 12
                                    

*KUNDIN HASKE*

*AL-K'ALUMAN MARUBUTA...*

*_NA KUNGIYAR:-_*
     _HASKE WRITERS ASSO...._

TAREDA AL-K'ALAMIN...
       *_Nana Hafsat_*(MISS XOXO)_

🙆🏻‍♀ *_NI NA JAWA KAINA!!...._*😭
    (SHAYE SHAYEN MAGANIN MATA)

*BABI NA BIYAR*

     *SHAFI NA 'DAYA...*

*Bismillahirrahmanirr rahim*

*S*allamar da aketa kwad'awa daga soro yasaka Nafisa fitowa daga falonta tana amsawa da,

“wa'alaikissalam,wacece ne?shigo mana”
     
Cikin washe jajayen hak’waranta tace,

“Nice maman Zara'u,ai nazatama bakya gidanne? Ko ko Baban Zara'u na nan?”
 
  “A'aaaaaa hajjaju mutan Makkah! Kece Ashe?.Wlhy ina nan,barcine yad'an figeni bayan nakammala 'yan ayyukan gida,Baban Zara'u yanzu agida?Aida anbani,yana kasuwa wlhy,  kinsan ance jiki da jini”

“Hakane kuma maman zara'u”
Cewar hajjaju tana jawo kujera 'Yar tsugunno ta zauna a gajeruwar inuwar da hantsi yafara tarawa.

Itama maman Zara'u saita d'akko wani tsumma dake kan igiyarta ta shimfid’a ta zauna, tareda jawo buhun ledan da hajjaju tazo dashi,

“To yaukuma me muka samu? Hajjaju mutan Makkah?”

Hajjaju ta washe baki,yo kayan harkane maman Zara'u, jiya-jiyannan aka turomin sabbin kaya daga Nijar, yaukam nad'au alk'awarin kece farkon ganinsu,dan nasan bakida wasa kokad'an”.

Dariya maman Zara'u tayi jin anyabeta, tace,

“kai hajjaju,dad'inafa dake akwai iya zance,musamman idan kinsan akwai maganar kud'i”.

“Hhhh maman Zara'u kenan,yo duniyarga wane shegene bayason kud'i? Kekanki harda maganarsu ke saka ki shan kayan harka. nikuwa ina labarin 'DAN MAZAK’WAI? Dana baki wancan zuwan, shin kingwadane?”
Tak'are maganar a hankali tamkar munafuka,

“Humm hajjaju kenan mutan Makkah da madina, kedai bari kawai, ainaso kizo gidannan washe gari”
Ahayyeeee casss...suka kwashe da dariya tareda tafawa.

Maman Zara'u tayi k'asa da murya, tamkar mai gudun kar wani yajisu, tace,

“kinsan wani abu kuwa?”

“a'a saikin fad'a”..Cewar hajjaju tana karkace kai.

“Hummm hajjaju aii dolene namiki k'yauta, ranarfa tamkar Oga zai karya gado, sambatu kuwa aii ba'a magana, harda alk'awarin jirgin sama,da hajji da umrah akamin”

Hhhhhhhh”A lallai gimbiyar mata, ta gaban goshi kenan, kice kinzama sarauniya ranar?, aidama nafad'a miki kisaya da ba so kikayi ki goceba, maganin yayi sosai wlhy,shiyyasa danaga kina neman gocewa nace kid'auka,kyabani kud'in idan nadawo, dama nasan za'a rina,

Kajimin bawan Allah,yajishi asama harda alk'awarin abinda yafi k'arfin arzik'insa? Hhhhhhh d'an mazakwai yayi aiki”


Hhhh
“kibari kawai hajjaju, aii koba'a sayamin jirgiba anmin k'yauta da safe, kuma sambatun da akaimin kawai yabiyani, kyautarki nanan tareda kud'inki”.

“Iyeeee banmusha mana”
Tareda cafke hannaye abinsu kuwa

Ni miss xoxo nace aiki..

“Aikuwa tunda hakane maman Zara'u dolene nakuma d'oraki a network, yo yanzu duk matar data zauna aii itace zataga zaunau, babu boka babu Malam, amma kiringa juya miji kamar sitiyarin mota, yo yana tsoron dare yayi ahanashi abubuwan shagali”

“Kinga wannan namatsine, idan kinyi sallar isha'i saiki dafa ruwanki dad'an gishiri kad'an, sannan kid'iba wannan maganin kiyi matsi dashi, saikije kiyi tsarki daruwan d'umminnan, shine zaisa maganin yakuma kamewa,wlhy ko bakin tsuntsu baya fad'a miki matsewaba,daganan kijuye wannan akofi kisa madara kishanye,wannan ma kisha,to wlhy yau Baban Zara'u har k'yautar babarsa zaimiki d'ungum”.

“kai amma ngd sosai hajjaju,nasan kina sona wlhy, shiyyasa bazan ta6a mantawa dakeba, Allah dai yaja kwana zamuce, aita had'a mana kayan harka.”

Cikin washe bak'i hajjaju tace,

“Amin maman Zara'u, aiini y’a na d'aukeki, yanda zanwa Zaituna tawajena haka zan miki, indai zaki rik'e kayannan aii mijinki ko neman aure bazaiyi tunanin yiba, barema zancen shegiya kishiya. kinga wannan turaren sunansa *MOTSA MASA*, indai kika shafa Oga yaji k'amshin, kobaiyi niyyar zuwa garekiba saiyazo babu shiri, saidai akula kar'ashafa gaban an jikallena Zara'u, Dan za'a iya fara komai agabanta”....

Dariya suka kuma shek'ewa dashi.Daganan Hajjaju tacigaba da nunama maman Zara'u kayan mata iri-iri, saida takwashi masu yawan tsiya, aka buga lissafi, kud'i suka kama kusan dubu goma sha shidda.

Babu tunanin komai maman Zara'u tashiga d'aki ta harhad'o tazo tabama dillaliyar maganin mata hajjaju, itakam ta lale kud'inta a lalitarta,tahad'a sauran kayanta tatafi tana wasa Nafisa maman Zara'u.

    Tana fita tashek'e da dariya,

“yo aii irin wad'annan mukeso, indai kana harka da irinsu maman Zara'u aii duk sati saika kawo kaya,kokad'an batajin asarar fiddawa tasiya,inagama yanda take sayen maganin mata ko zanin d'aurawa bata saye haka bare taimakon iyayenta, alhalin gasucan kuma cikin wahala”..

Hajjaju ta ta6e baki tareda kuma rik'e buhunta da k'yau,

“yoni inama ruwana, nidai bana kawo ansayaba, takula da iyayenta kokarta kula wannan matsalartace, nidai kaina nasani wlhy, gobema kawowa zanyi, mu aii bama sanya da Neman nakanmu” ita kad’ai ke wannan maganganu kamar sabuwar mahaukaciya tanayi tana jefa hannuwa sama...

Bayan Hajjaju ta fita Maman Zara'u ta had'e kayanta takai d'aki ta adana, zuciyarta nawani farinciki,Dan tasan yau Oga babu dama.

*_Dare_*

   Duk yanda hajjaju ta misalta mata hakan tayi. takuwa sami yanda takeso, washe gari Baban Zara'u harda kyauta yamata gagaruma kuwa.

Tsalle taitayi tana ihu itakad'ai agida, tama k'agara hajjaju tazo gidan takuma d'ibar kayan harka.

Nidai nace "uhumm".

 

✍🏾BY MISS XOXO

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now