4

1.2K 112 9
                                    

*KUNDIN HASKE*

            _Al 'kaluman Marubata_

     KUNGIYAR:-

     *HASKE WRITERS ASSOCIATION* (home of expert and perfect writers)

   TARE DA AL 'KALAMIN✍🏼
           *SAFIYA GALADANCI*

*K'AIK'AYI*

BABI NA GOMA SHA TARA

Page 4

Wani gida taga sun shiga hankalin ta ya Dan tashi Dan bata san gidan waye ba amma sai taga yara sun rugo da gudu suna cewa oyoyo uncle kabir, murmushi tayi tasan gidan yan uwansa ya kawo ta, murnarta ta ragu tunowa da tayi anfa saka mata rana, amma sai ta share, shiga sukayi ciki matar gidan na zaune palo, kabir ya kalleta yace "to Anty yau dai ga khadija na kawo miki, na kusa zama ango ki daina yimin gori" dariya tayi tana kallon khadija suka gaisa sannan yace "to bari mu tafi anty zasu shiga jarabawa ne" mikewa anty tayi ta shiga daki Leda ta mikawa khadija amma sai taki amsa sai kabir ne ya karba yana godiya, me makon taga sun wuce makaranta sai taga sun nufi wata unguwar, tasan yau zata sha yawon dangi kadan tayi murmushi, har suka shiga gidan batayi magana ba, gidan abude sai sallama yake zabgawa amma ba a amsaba, ya kalleta yace "na manta batada lafiya matar gidan fa, shigo dakin pls" ya fada yana yi gaba, bin bayansa tayi da sallama a bakinta.

Murmushi yayi yana kallonta sannan ya rungumeta yana cewa "wai khadija bakya bukata ta ne? Sam yau ko hannuna baki rike ba" zaro ido waje tayi tana cewa "sakeni mana matar gidan fa zata iya ganin..." Rufe mata baki yayi da nashi yana kai hannunsa Inda yasan zai kunnata, a hankali ta zauna kujerar dake dakin ya bita ya zauna yana cewa "ai ko ta ganmu tasan soyayya ce tasa haka" bai kuma bari tayi magana ba yaci gaba da abinda ya fara, ta kasa hanashi Dan tana jin dadin abinda yake mata, kafin ta Ankara babu uniform ajikinta sai inner wears kawai, kallonsa tayi tana cewa "me kake shirin yimin? Dagani nasaka kayana ka maidani makaranta" ta fada tana kokarin tureshi, nauyinsa ya sake mata Dan kamar bayajinta ma, kara tureshi tayi yaja vest din jikinta saida ta yage kara tayi Dan taji zafi,daganan suka ci gaba da kokawa.

Gefe ta koma tana kuka tace "Wanda kake turamin duk banga sunji zafi ba, mugunta kayimin, Allah sai ya saka min" kallonta yayi sannan ya kalli agogo saura minti arba'in su shiga jarabawa, da sauri ya shiga toilet ya kunna ruwan zafi suka taru sannan yace ta shiga ta zauna, da sauri ya fita daga dakin yashiga na kusa dashi, wanka yayi koda ya dawo harta saka uniform tana masa mugun kallo tace "ka maidani makaranta" bai yi magana ba ya fita tabi bayan shi tana jin zafi ajikinta, nesa da makaranta ya ajiyeta ta taka da kafa ta karasa, koda ta shiga skul wani gumi take saboda yadda kasanta ke mata zafi, hankalinta duk baya kan abinda ya faru, tunanin yadda baza agane a gida take ba.

A hall din da suke exam sit dinta ne farko Zainab kuwa tana can baya bayan an fita bata nemi Zainab dinba kawai ta fito lokacin har abbunta yazo ta shiga mota suka wuce, juwairiya na zaune a Palo tana waya da jawahir tana cewa "sai ayita yin abubuwa a gida ban sani ba, yanzu ya kyautu ace halisa ta haihu ban sani ba har gobe suna? Aiko bazanzo ba inada hakkin a fadamin, gwaggo luba yanzu sai taga laifina Dan kinsan su basa gani su kyale, a hadu dakai cikin mutane a yarfa maka magana Mara dadi" tana maganar tana kallon khadija data shigo kamar Mara lafiya har ta shiga korido dinda dakinsu yake, jawahir tace "yaya ke matsalar bakya WhatsApp ne, da komai zaki ringa gani idan ya faru a group dinmu na gida, ki lallashi Abbun Nana khadija mana" tabe baki juwairiya tayi tace "rabani da kayan wahala karki jaza min indai zaki iya ki masa magana ke ko zai yadda amma ni idan nayi hayayyako min zaiyi" dariya tayi sannan tace "to zan masa magana dan har khadija ma yakamata ace tanada waya" juwairiya tace "to Allah ya cida ita, bari na lekata naga ta dawo daga makaranta kamar Mara lafiya" jawahir ta amsa da to sukayi sallama.

"Me yake damunki kika dawo haka" juwairiya ta tambayi khadija dake kwance, kallon umminsu tayi tana cewa "tunjiya naji kafata ta fara ciwo shine yau ciwon ya karu kuma kaina na ciwo sosai, cike da tausayi juwairiya tace " to tashi kiyi wanka da ruwan zafi kinji kizo inshafa miki rub" toilet din khadija ta shiga tayi wanka ta fito, juwairiya tana Shafa mata rub din tace "Aiko wannan wahalar jarabawar saita saka ki ciwon kafa, najima har jikin ki ya soma yin zafi" shuru khadija tayi har juwairiya ta fita anan Inda take baccin wahala ya dauketa.

Sai da ta kwana biyu tana jin jiki sannan ta warware, tun daga lokacin bata sake jin labarin kabir ba haka ma Zainab bata sake yi mata zancen shi ba, suna dai kawancensu amma zancen samari baya shiga tsakaninsu, tuni ta daina daukar wayar ummi ji tayi gaba daya ta tsani wayar.
Babu dadewa suka kammala exam din ta shiga zaman gida, lokacin kuma an fara Azumi, duk azumin da ta dauka a wahale take kaishi har aka kai ashirin da biyar, juwairiya idan ta kalleta sai tace "ke kullum bazaki taba cewa Alhmdllh ba, idan kin dauki azumi sai dai kiyita kwanciya"?  Shuru kawai khadija tayi mata, juwairiya taja dogon tsaki tana ci gaba da aikinta.

Ciwonta yayi tsanani sosai har sai da ta ajiye azumi biyar na karshe, se faman dura mata maganin typhoid ake na turawa Dana gargajiya, amma babu sauki, sallah da kwana biyu Abbansu yace Gara su tafi asibiti, shiryawa juwairiya tayi itama khadija ta shiryata, sai da suka sauke su Aisha gidan jawahir sannan suka wuce asibitin, babu bata lokaci aka kwantar da ita ana kara mata ruwa sannan aka rubuta musu test da hoto, tunda suka ga hoton gaban juwairiya yake faduwa, sharewa tayi har sukaje aka yi komai aka gama.

Zaune kawai suke suna sauraren bayanin likita har yakai karshen maganar shi saifullahi ya mishi godiya ya fita, anan yabar juwairiya ko motsin kirki ta kasa yi, Dr din ya shiga kwantar mata da hankali, ta daga kai kawai ta fito daga dakin.

Tana kwance ya shiga dakin, maida kofar yayi ya rufe sannan ya zauna kusa da ita yahada hannayenta duka ya rike yace " waye ya miki cikin dake jikin ki"? Ya tambayeta yana zaro mata idonsa da suka gama yin ja, a firgice ta kalleshi tace "Abbu banida ciki, banyi komai ba" mari ya sauke mata mai kyau yana cewa "akwai wani hali Nawa da baki san dashi ba? Wallahi idan baki fadamin ba sai na baki mamaki" ganin yadda yake Neman birkice mata yasa ta saurin fadin "Abbu idan ka dakeni mutuwa zanyi dan Allah kabari gobe zan fada maka" cikin tsawa yace "yanzu zaki fada" tana kuka tace "Abbu kabir ne dan gidan umar mai shinkafa" mikewa tsaye yayi yana kallonta, yadda zuciyarsa ke masa zafi bada ban kar ya kashe ta ba wallahi sai ya mata dan banzan duka, mikewa tayi tana ganin jiri zata gudu amma ta kasa, sai yanzu abinda ta aikata yake damunta duk da bada son ranta bane amma tasan ita ta bada kofar da hakan ya faru.

Ruwa aka kara mata har yamma sannan suka koma gida, suna zuwa gida ya kasa hakuri, ya hau dukanta, juwairiya na gefe tana kallon ikon Allah, har sai da taga yarinya ta fadi ta kasa tashi ma sai amai take daga kwance, da sauri ta matsa kusa dashi ta ture shi tana cewa "kashemin ita zakayi? Ko akanta aka soma yin cikin shege? Saifullahi na gaji, wannan karon zan dauki mata ki, kuma kasani ko kusa wallahi barewa bazatayi gudu danta yayi rarrafe ba".

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now