3

1.6K 154 13
                                    

KUNDIN HASKE

ALKALUMAN MARUBUTA🤝

*💡 HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*

*Wattpad :-AyusherMohd*

TARE DA ALKALAMIN

*Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*MENENE MATSALAR?*

*Babi na Ashirin*


Domin neman Kundin Haske daga na 1 zuwa na 20 ziyarci https://my.w.tt/psg00vI7a5. Ko wani babi yana kushe da labarinsa ne, ba cigaba bane ba kuma a hade suke ba.


Part 3

Sosai Abdul ya nuna mata farincikinsa akan cikin data samu sai dai sam kulawar da takejin labari a littatafai da fina finai sam bata samu, ba ruwansa da me ta sawa cikinta, ta iya dafawa? ta iya ci? Yata wuni? Kawai shidai harkar gabansa ce ta dameshi.

Yau kafin ya fita bayan ya gama cin abinci takai maganar Jamb dan taji an kusa rufewa.

Tea ya kurba yace "jikinki kike fama dashi ko karatu?"

Tace "idan nai Jamb din kafin na nemi skul na samu kaga na haihu insha Allah, sai nai karatun hankali a kwance."

"Abinda kika haifa fa?"

Tace "Umma na gida zan dinga kai wa can, su Yaya Rabi ma a haka sukai karatu."

Gidanku za'a kai d'ana? Ko 'yata?

Yanda yai tambayar ne yasa tace "ban gane ba?"

Mikewa yai ba tare da ya shanye tea din ba ya fita.

Gaba daya jitai ta kasa ko mikewa, haka ta wuni kalmar na dawo mata.

Zahra tabi ta rame saboda sam bata iyacin abinci hanci a toshe take iya yin girki, ga kasala data addabeta.

Shiga kitchen yai shan ruwa ganin tana bandaki, sai dai me? Ganin kwanukan datai amfani dasu tun safe hade dawandai tai amfani dasu da rana a cikin sink yasa ransa yai matukar baci.

Daki ya nufa yana bude kofa tana fitowa daga toilet amai tai a galabaice ta fito.

Wani kallo ha mata yace "Zahra kazama kike neman komawa? Akan me za'a bar kitchen da uban kwanukan da ba'a wanke ba?"

Dan xama tai a bakin gado tace "zanyi anjima na gaji ne wlh."

Wani dan tsaki yai yace "sai yanzu na gane meyasa wasu mazan ke kara aure daga matarsu ta haihu ko ta fara laulayi, haka kawai kamar a kanki a ka fara ciki shikenan sai gida ya fara kaxanta saboda dan ciwon da bai kai ya kawo ba?"

Bata taba musu dashi ba sai dai da alama cikin datake dashi ne yasa taji zuciyarta kamar wacce aka tunzuru, cikin fada tace "bai kai ya kawo ba kace? Yaushe raban dakaga ko abinci naci? Ka taba damuwa da yadda nake cusa abincin da bana so? Haka ina gama ci nai amansa? Abdul anya ka damu dani kuwa? Meyasa duk abinda nai bana taba burgeka? Duk iya kokarin da nake na faranta maka baka gani?"

"Kokari? Kina san cewa zaman auran da kike dani ma kokari kikeyi kenan ko me?"

Mamaki ne ya kamafa ganin ya fassara abinda tace, wani kallo ya mata yace "mata nawa ne suke da ciki suke haihuwa lafiya? Kece kika fi kowa ko taki tsaftarce dama batai nisa ba?"

Jikinta sam ba karfi ga takaicin kalamansa dake mata yawo.

Ido kawai ta zubamai bakinciki ya hanata magana, mikewa kawai tai ta fita ta wuce kitchen.

Dakyar ta ita jingina take wanke wanken tana yi tana share kwallarta, sam itakam wata dayan farkon aurenta ne kawai taji dadi amma sam zama da Abdul baya mata dadi ta rasa daga ina matsalar ta soma.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now