Shafi na bakwai

1.6K 144 1
                                    

*KUNDIN HASKE*

  *AL-K'ALUMAN MARUBUTAN HASKE.*

*K'UNGIYAR:-*
   *HASKE WRITTERS ASSOCIATION.*
(Home of expert and perfect writters)

*TAREDA AL-KALAMIN*🖋
Zaynab bawa (zeeyybawa)
            
   *TALLACE-TALLACE*
(Sanya idanuwa akan tarbiyar yarnmu)

*BABI NA BAKWAI*

*SHAFI NA  BAKWAI*

Gidansu suwaiba

   Mama! mama! Shine abunda suwaiba take fad'i lokacinda tashigo cikin gidansu, daga d'aki mama taji kiranda suwaiba takeyi mata, tanajin kiran ta tabbatar ta siyarda tallantane, fitowa mama tayi cikin murna tana fad'in suwaiba! Badai harkin dawoba?"

Nadawo mama kuma na siyarma duka d'agowa tiren tayi tana fad'in kingani ko d'aya babu, kuma Kud'inki bai 6ataba suwaiba tafad'a tana washe baki, Mama itama dariyar  takeyi tace" Ahh lallai y'an matana anyi qoqari, ynzu nazuba miki wanine kokuma zaki huta?"

Suwaiba tana gyara d'aurin zaninta wanda yake qoqarin sincewa tace" Aa mama kibari ni yanzu hakama bacci zanyi zuwa rana saina d'auka na kayi,

Toh naji kishiga ki huta kiyi baccinki kafinnan nima zanyi qoqari nahad'a abincin rana, wucewa suwaiba tayi d'akinta, juyowa tayi tana fad'in laah ungo wannan mama kinga na mancema kuma ban baki kud'inba,

Sanya hannu mama tayi takar6i kud'in tana fad'in y'annan babu abunda zance dai dai Allah yayi miki albarka, maza shiga kiyi baccinki,

Suwaiba tana shiga mama tasoke kud'in jikin zaninta, cikin azama tafara kici kicin had'a abincin rana,

Ba suwaiba tatashiba sai qarfe 2na raba hakanma kashine ya tasheta tana tashi tanufi band'aki da saurinta,

Sanda tagama sannan takwala mamanta kira, mama! Mama! Na'am mama ta amsa tana qoqarin fitowa daga cikin d'aki,

Mama kawomin buta, toh mama tafad'i had'eda d'ura ruwa cikin butar takai mata,

Bayan tayi tsarki tafito tana fad'in mama ina abincina?"
Yana kitchen mama tafad'a tana komawa d'aki d'auko abincin tayi tafaraci, shinkaface da wake da mai dakuma yaji😋 tanaci abunta cikin kwanciyar hankali,

Fitowa mama tayi tad'auki kujera y'ar tsugunno tazauna tana duban suwaiba tace" suwaiba kiyi-kiyi mana,  ranafa tayi sosai yanzu zakiji yamma tayi ynzu idan kika d'auka kafin kidawo dare yayi bazakiyi wani ciniki ba,

Suwaiba tanacin abincin tace" mama aikoda yaushe nafita dashi zan siyar nikam ki rabu dani kada na kware,

Shiru maman tayi mata, ita kuma tacigaba da d'urawa cikinta abincin,

Saida tagama sannan taje randa tasha ruwa sannan tadubi mamanta tace" nagama d'aukomin natafi, da mamaki nake duban mama ina kallon ikon Allah tunani nakeyi shin zata dauko matane kokuma Aa, domin naga batayi sallan azaharba kuma sallah yakamata tayi ynzu ba fita talle ba, kuma koda ita batayi tunanin yin hakanba yakamata mahaifiyarta ta tunasarda ita (sallah itace aikinda za'a fara dubawa cikin ayyukanka aranar alqiyama, mugyara sallalolinmu domun akwai kura kuraida mukeyi cikin sallah ta fannoni da dama mutashi tsaye munemi addnin musan addini, muneni lahirarmu, mutane da dama suna yiwa y'ay'ayansu sake wajan sanyasu suyi sallah, zakiga mahaifiya tayi sallah amma kuma bata damu ya yaranta sunyiba kokuma akasin haka, inaso iyayesu sani cewa sune malamai na farko wajan y'ay'ansu domin duk wata d'abi'a da yaro zai taso dashi kaine zaka koya masa, sannan kuma sallah yaro tun yana qarami yakamata kina nusardasu, kaikuma mahaifi idan zaka tafi masallaci saika d'auki yaronka kutafi tare dashi, don icceh tun yana d'anye aka tanqwarashi idan yagirma  a kaso tankwarashi sai dai ya karye, kada kadubi shekarun yaranka/ki kace wai nawa suke idan ynzu basuyiba wata rana zasuyi, Allah tunda wuri zaki koyawa yaranki tarbiyya, a kullum ina tunatarda mu cewa yaranmu kiwone agaremu kuma Allah zai tambayemu akan kiwonda yabamu, Allah yasa mudace amin) back to labari jira nakeyi naji mai mama zatace  ga mugun mamaki sainaji mama tace" jira inazuwa barina d'auko miki dukda kasancewar tasan d'iyar tata batayi sallah ba,

Ta shiga ciki domin d'auko mata tallan, sallama baba yayi yashigo, suwaiba wacce take tsaye batareda ta amsa sallamarba take duban babanta wanda takan manta dashi acikin gidan domin kuwa sai suyi sati basu had'uba shi yayi ficewarsa itama tayi tata ficewar sai dare yake dawowa lokacin tana wajan talla kafin tadawo sunyu bacci da rana kuma idan kaga yadawo tocin abincine saiya gama abunda zaiyi yatafi tana bacci,

Kallonta yakeyi da dariya yana fad'in Aa suwaiba ba'a fita bane yau?"
Nafitama nadawone ynzu zan koma suwaiba tabashi amsa

Toh Sannu bbu wata y'ar naira hamsinne wajanki?" baba ya tambaya, sannan yad'aurada fad'in
Wallhy takaunina ya 6alle kin ganshi haka nakeda jansa,

Kallonsa suwaiba takeyi tawani had'erai tace" kai kullum baba saika kar6emin y'ar nera hamshin d'ita,

Tafa hannu yayi cikin washe hakora yace toh y'ar nan idan bankar6i takiba tawa zankar6a?"
Cirowa tayi ad'aurin zaninta tana fad'in gatanan shikenan kuma kada ka qara tambayata,

Mamace tafito tana duban baba da takaici tace" ynzukai mlm bakada aiki kullum sai dai abaka-abaka?"
Y'arka kullum ka kar6e mata d'an kud'inta,
Kaikam aikaji kunya, kaima kafara neman nakanka nama, ai itana y'artaka fita takeyi tana nema da kanta,

Qarasowa yayi yana fad'in uwar suwaiba kenan toh a'ina zanfitana nema d'n?"

A yanda maza suke nemowa mana, mama
Tabashi amsa tana wurga masa harara,

Zama yayi yana fad'in bani abincin naci,
Gafara kabani waje wani abinci kenan?" wanda ka nemo kakawo?"
mama tafad'a cikin 6acinrai,

Aaa Allah yahuci zuciyarki nidai zubamin naci,
Tsaki taja tamiqawa suwaiba tiren dake hannnunta tajuya tadubeshi tace" zaka iya zuwa kitchen kad'auka nikam nayi d'aki,
Tana fad'in haka tashige d'aki itakuma suwaiba tafice tallanta shima miqewa yayi yashiga kitchen yad'auko abincin,

Sanda yaci ya koshi yasha ruwa sannan yatashi domin fita wajan zaman banza, wajan gulmar y'ay'a da matan mutane wajan fad'i sonka wajanda su basa kallon irin ta6ararda suke aikatawa saidai zagin na mutane domin kowa ya wuce sai an zageshi, dama ance ynzu gulma takoma wajan maza lolx😂."

  Suwaita data fita bata wuce wajan talla kai tsayeba gidan qawarta tawuce domin tasan kusan tare suke fita kullum ay'an kwanakinnan,

Aikuwa tasamu bata fitaba don haka tajirata tagama tafito suka fita,

Har bayan la'asar suna zagayawa babu wani cinikin kirki,
Suwaiba tadubi furera tace furare tace" furera yaukam babu ciniki tund'azu muke yawo,

Yatsuna fuska furera tayi sannan tace ke nifa dama shiyasa bansaba yin yawon talla sosaiba,
Kingani da big boy yananan idan ynzu mukaje kud'in tallan zai bamu gabaki d'aya yace mu rabawa yara,

Da mamaki suwaiba ta kallesta tace yarafa kikace?"

Jijjigakai kawai suwaiba tayi tace nikam akwai wani mutum acan bayan layinnan dayake bani 200 kullum najeni saiya kar6i abun naira hamsin kawai,

 
  Furera tadubi suwaiba tace mujetoh tunda kinga lokaci yana tafiya wucewa sukayi dukansu,

Shida abokinsa suka sameshi suna zaune tsugunnawa suwaiba tayi ta gaishesu, d'an dariya yayi sannan yadubi abokinsa yace yagani dama nafad'a maka zatazo,

Abokinne yace" kada kabari dama tawuceka kullum sake kakeyi, aikam haka za'ayi yafad'a, batareda suwaiba da furera sun fahimci mai suke nufiba  yadubi suwaiba yace kinga shiga gidannan kicewa matar gidan takabaki ruwa kikawomin,

Tashi suwaiba tayi jiki yana 6ari tace" toh shigewa cikin gidan tayi shima abokin yadubi furera yace nima shiga ki d'aukomin kufito tare, tashi itama tayi tabi bayansa,

Suna shiga cikin gidan suma sukayi saurin miqewa suma suka shige had'eda kulle qofa."

To be continued

Ur's zaynab Alabura."

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now