11

1.8K 175 18
                                    

KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association💡

(Home of Experts and perfect Writer's)

*SANADIN K'AWA*

NA

*khaleesat Haiydar*

BABI NA GOMA SHA HUDU


11



Cikin dare bata jira shawarar kowa ba ta mike ta dau maganin da Elbasheer ya siya mata ta sha don wani mugun xaxxabi take ji, har kusan asuba bata yi bacci ba sai bayan da aka yi sllh taji dama dama sai a sannan bacci ya dauketa. Da safe ko kafin ta fito Ammi ta gama duk aikin gidanta, jiki ba kwari tayi wanka ta wanke baki ta tafi daki ta shirya sannan ta fito ta debi kunu kadan ta sha ta kuma shan magani ta kwanta. Yau ma kamar jiya haka aka dinga xuwa ana ma Amminta jajayen dawowarta duk kuma me son ganinta sai dai ya leko daki ta gaishesa ya wuce, ciki har da yan uwan mahaifinta duk sun xo, da rana Ummi ce ta kawo mata Danwake, yunwan da take ji yasa ta cin kadan a cikin danwaken, ko minti biyar bata yi da tura plate din ba amai ya taho mata, a nan tsakar gida ta dinga kwarara aman, ko kallon inda take Ammi bata yi ba, can kuma ta mike ta wuce daki, dai dai shigowar Nafisa gidan, da sauri Nafisa ta nufeta tace "Subhanallahi sannu Fatima" ita ta taimaka mata ta kawo mata ruwa sannan ta wanke gun aman, daga ta tayi suka nufi daki, ta durkusa kusa da ita tace "Sannu Fatima, jiya da rana da na xo kin fara bacci ban tashe ki ba na wuce ya jikin?" Fatima ta mike xaune tana kokarin maida hawayen idonta tace "Da sauki" Nafisa tayi tagumi tace "Wllh ban san abinda ya faru ba knn sai jiya Murja ke gaya min" shiru Fatima tayi, can ta kalli Nafisa dake kallonta da tausayi cikin sanyin murya tace "Nafisa na cuci kaina, had it been I didn't neglet any of ur advice all this wouldn't have happen to me" Nafisa ta kamo hannunta da damuwa tace "Don't worry besty, we do always learn from our mistake, Alhmdllh tunda kika dawo gida lafiya" Fatima ta fashe da kukan takaici tace "Not this type of mistake Nafisa, I was raped...." Ja baya Nafisa tayi da mugun mamaki tana kallonta, kuka ta sakar mata ita ma tana kallonta tace "Innalillahi, How?" Where?" Fatima ta hade kanta da gwiwanta tace "Husnah.... She ruined my life, had I known..." Hawaye na sakko ma Nafisa tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" bbu abinda Fatima ta boye mata tun daga farkon haduwarsu da Elbash har karshe, yanda take kuka haka Nafisa ke kukan, daga karshe ita ta daina kukan ta dinga lallashin Fatima har ta samu ta nutsu, Nafisa tace "Baki ce masa kada ya sake xuwa gidanku ba kuma?" A sanyaye Fatima tace "Tsoronsa nake ji, har ce min yake xai gaya ma Ammi abinda ya faru" Nafisa ta hade rai tace "Toh ya fadi mana, duk ya sake dawowa wllh kiyi masa koran da baxai kara tuna hanyar gidan nan ba, macuci da shi" Fatima dai tayi shiru bata ce komai ba amma har lkcn hawaye ya kasa daina sakko mata, cikin rawar murya tace "Toh don Allah ki gaya min yanda xan yi da baxai sake dawowa ba, wllh tsoronsa nake ni Nafisah" Nafisa tace "Tara masa jama'a xa ki yi idan har ya sake dawowa" Nafisa bata bar gidan ba sai kusan magrib bayan ta tabbatar ta kwantar ma kawar tata hankali, ta kuma bata duk shawarwarin da ya kamata. Washegari da safe ta fito tsakar gida, ganin Ammi bata gama aiki ba ta fara hada kwanuka xata wanke, Ammi dake shara tace "Ni ban sa ki ba, ki tafi ki shirya mu wuce asibiti yanxu" Har suka isa asibitin kusan karfe goma Ammi bata ce mata komai a napep ba, amma kana ganinta kasan tana tare da damuwa sosai, duk jikin Fatima yyi sanyi sanin ita duk ta sa mahaifiyarta a damuwar nan, duk iya kokarinta na ganin bata bar hawayen dake makale idonta ya sakko ba ya tashi a banxa don hawaye sosai ta dinga yi har aka xo kansu a ganin likita, series of tests aka yi mata bayan Ammi tayi ma likitan bayanin komai wanda sai da ta kashe ya fi dubu takwas a take, daga karshe magunguna aka hada mata da allurai bayan an tabbatar bbu wani matsala, aka kuma basu lokacin da xa su dawo a sake mata tests din sannan suka wuce gida. Bayan kwana biyu fatima na debo ruwa da yamma daga tap dake kusa da kofar gidansu kasancewar bbu ruwa gidan kuma Ummi na makaranta, Ammi dake girki a tsakar gida tace "Ki bar ruwan haka nan" Fatima tace "A'a ya kusa cika Ammi yanxu xan gama" daga haka ta fita, xuwa lkcn bbu laifi Ammi na kulata sosai kuma tana jan ta jiki, wanda hakan yasa ta fara mance komai, gashi kuma Elbash din bai sake xuwa gidansu ba, yanxu dai damuwarta Umar, tasan baxata taba aurensa ba kamar yanda Ammi ta gaya mata a baya, ko da Ammi bata fadi hakan ba ita dama ta kudira a ranta baxata iya aurensa ba kuma don bata san da idon da xata kallesa ba, tana kkrin daukar ruwanta da ya cika taga mota ya shigo layin, tun daga nesa ta dinga kallon motar har ya iso kofar gidansu yyi parking gaba da inda take, lkci daya kuma ya bude motar ya fito, sanye yake da Gezna sky blue dake ta faman kyalli, ya rungume hannayensa yana kallonta, gabanta yyi mugun faduwa tayi saurin dauke kanta tana kiran Allah a xuciyarta, nufota yyi ya tsaya dai dai inda take yace "Wannan katon bucket din kike dagawa superwoman?" Hade rai tayi ta juyo tana kallonsa tace "Malam ka fita rayuwata na hadaka da Allah, stay away from me, I hate seeing you, ka fita rayuwata ka kyaleni" a tsawace ta kare maganar cikin fushi, kallonta kawai yake kafin yace "Ohh really?" Tsaki ta ja ta juya xata dau ruwanta ta wuce ciki yace "Toh wai ma na ce maki gun ki na xo?" Wani kallo ta watsa masa yyi wani murmushi yace "Rashin kunyar dai?" Bata tanka sa ba ta dau ruwanta da sauri ta wuce ciki, tana juyewa ta shiga daki ta xauna ta dinga rusa kuka, ita kam ta shiga uku Husnah ta ja mata, har aka kira magrib tana daki, daga bisanni ta fito a sanyaye ta daura alwala ta koma ciki, tana idar da sllh ta shiga wanka. Bayan ta gama shiryawa ta sa hijab ta wuce dakin Ammi, Ammi da ke kan darduma ta bi ta da ido har ta xauna, Fatima tayi kasa da kanta a hankali tace "Ammi don Allah ina son xuwa gun Umma a Kaduna" Ammi dake ta kallonta tace "Saboda me?" Kasa dagowa tayi sbda hawayen da ya cika idonta, Ammi tace "Tell me ur problem Amira" hade kai tayi da gwiwa cikin rawar murya tace "Ammi bana son in xauna nan kuma, don Allah ki bar ni in tafi" Ammi da jikinta yyi sanyi tace "Fatima" sai a sannan Fatima ta dago tana kallonta, ta nuna mata kusa da ita ta dawo, Ammi tayi kasa da murya tace "Ki gaya min meye damuwar ki har yanxu? Ba nace kada ki sake sa ma kanki damuwa ba" A hankali tace "Ammi ni ma ban san me yasa nake haka ba" Ammi tace "Ki dinga azkar din ki kan lokaci ki kuma dage da karatun Qur'an kin ji" ta gyada ma Ammi kai sannan tace "Baxan je ba kuma Ammi?" Ammi tace "Bani da kudin mota yanxu, ki bari sai na samu kudin" a hankali tace "Toh Ammi nagode" sannan ta mike ta fita dakin ta koma nasu. Yau Friday Fatima na xaune tsakar gida tana yi ma Ammi tankade tayi nisa gun tunanin abinda xata gaya ma Umar ya rabu da ita ba tare da yasan komai akan abinda ya sameta ba, cikin kwanakin nan tausayinsa take ba kadan ba, kusan duk dare sai ya xo gashi ta rasa ta inda xata fara hakan yasa ta shiga damuwa sosai, yau kam ta dau kudurin dole ta sanar masa ya nemi wata kawai. Washegari ta yi iya kokarin ganin ta kauda duk damuwar ranta har yamma, Ammi dake wanke wanke tana lura da ita tace "Tunanin me kike?" Da sauri ta dago kan ta ce komai wani yaron makwabta ya shigo wai ana sallama a waje, Ammi ta sa Hijab tace "Toh a shigo" Fatima sai kallon kofar xauren take taga wanda xai shigo, da sallama ya shigo gidan hannunsa rike da makullin mota, sanye yake da shadda milk kala, kallonsa kawai take ko kiftawa bbu, ya karaso yana kallon Ammi da ta amsa masa sallamar sa ya xauna gefen tabarma da fatima ke xaune ya gaisheta ta amsa tana tambayarsa ya aiki, yace "Alhmdllh mama, ya mai jiki?" Tace "Alhmdllh mun gode Allah" Fatima ta kasa ci gaba da abinda take duk jikinta yyi sanyi, ajiye rariyar tayi ta mike da sauri xata wuce daki Ammi tace "Toh ki kawo masa ruwa koh" ta juya a hankali ta nufi gun da suke ajiye ruwa, ta dau cup ta debar masa ruwan, Ammi ta mike ta shiga ciki da cooler din da ta wanke, Fatima ta karaso fuskarta daure ta durkusa gabansa ta ajiye masa ruwan, xata mike ya rike tip din Hijab dinta, tsayawa tayi amma ta kasa kallonsa, jin bai ce komai ba ta dagota kallesa, kallonta yake, ya wara manyan idonsa yana nuna kofin ruwan yace "Is it clean?" A takaice tace "Ban sani ba" ya kai fararen hannunsa ya dauka ya kai baki, kadan ya sha ya ajiye cup din sannan yace "How you feeling?" Bata ce komai ba yace "Toh ci gaba da aikin ki" Tsaki tayi xata mike yace "Don't move, or I shock you" jigum tayi bata ce komai ba, can ta koma a sanyaye ta xauna ta ci gaba da tankaden da take yi, murmushi kawai yake yi shi kadai, can ya kai hannu cikin garin ya dangwala ya shafa mata a kumatun ta, kauda kai tayi ya kuma shafa mata a daya kumatun, hade kai tayi da gwiwa tana jin kamar ta rusa ihu, ya mike yana juya makullin hannunsa yace "Kice da mama na tafi" kofa ya nufa ya fita gidan, sai a sannan ta dago hawayen dake makale idonta ya sakko ita kam ya xata yi da ranta da mutumin nn dake bibbiyarta, bayan kusan minti biyar sai ga almajirai uku sun shigo gidan ko wannensu rike da foodstuff, xaro ido tayi ta mike tace "Daga ina?" Suka ce "A waje aka ce mu shigo da su" da sauri ta fita, buhun shinkafa ne da babban jarkan mangyada da na manja suka yi saura a waje, ta bi motarsa da har ya kusa barin layin da kallo, gabanta na faduwa ta juya ta koma ciki, tsaye taga Ammi tana kallon Kwalin taliya biyu da couscous da ke ajiye tsakar gidan tace "Wannan kuma daga ina" a d'an tsorace tace "Ammi nima gani nayi suna shigowa da su" Ammi tace "In ji wa?" Tace "Wannan mutumin da ya xo" Ammi ta mata wani kallo tace "Baki gaya masa kina da mijin aure bane?" Girgixa mata kai tayi kamar xata yi kuka, strictly Ammi tace "Toh maxa shiga ki kirasa ki sanar masa yanxun nan" da sauri tace "Ammi bai ce yana so na ba, kawai..." Ammi ta katse ta tace "Wuce maxa kiyi abinda na sa ki nace" juyawa tayi ta shiga ciki, ta dauko wayarta da ya kawo mata ranan ta kunna a karo na farko, bbu bata lkci ta nemo lambarsa ta yi dialing, katsewa yyi ya kirata, ta daga ta kai kunne, yace "Kin kunna wayar kenan?" Ta hade rai tace "Malam ka dawo ka tafi da sakon da ka aiko da shi yanxu" yace "Koh?" Tace "Eh" yace "Ohk, but nayi nisa yanxu, anjima da daddare xan dawo sai in tafi da su" tace "Better" daga haka ta katse wayar, ta xauna gefen katifa tayi tagumi, Lambar Umar tayi dialling jikinta a sanyaye, katsewa yyi shima ya kirata.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now