chapter two

17 1 0
                                    

So da buri
Free book
02
                      

Shiru Baba yayi yana tunanin ta hanyar da zai bi ya d'an kwantar ma da Umma hankali...chan ya yunk'ura yai gyaran murya kafin yace
"Sadiya ni bance harda yayunta maza ba,dokar iyaka kanki ne ke da Jalila shima kuma saboda Kaka yayi mini kashedi mai zafi shiyasa, ko kina so Allah ya isan shi ta hau kaina??
yayunta maza sunada ikon hukuntata indai ta yi laifi kuma ai...."

"Aikin banza ma kenan!!!"tsawar Umma ta katse shi
Kafin ta ci gaba da cewa"ai kaga wannan matar"
ta yi maganar tana nuna Mama wadda tunda aka fara maganar bata ce uffan ba. Cikin huci ta d'aura da cewa"tabbas in dai baka taka mata burki ba tunda ta samu Kaka yana goya mata baya zata sake komawa wajen shi ta kai k'arar su Junaidun suma..tunda naga kamar ma  tsoronta kafara ji."
Ta k'arashe maganar tana huci.

Shiru Baba yayi kafin ya d'ago kanshi ya kalli Mama
"MARYAM"
ya kira sunanta cikin kakkausar murya.D'agowa Mama ta yi ta kalleshi kafin a hankali tace "naam"
Nisawa yayi sannan ya ce
"kin kai k'arata wajen mahaifina,an yi miki abunda kike so ko? To nima ga nawa sharad'in,
Indai Huda ta yi laifi kika hana su Ja'afar hukuntata kema a bakin aurenki,don kamar yadda Sadiya ta fad'a ba zai yiu ace Yaro babu mai kwab'arshi a gida ba,
Ita dai da Jalila ga sunan sun bar miki y'ar ki."
Yana gama fad'in haka ya d'ora da cewa
"Shikenan kowa zai iya tafiya na riga na gama magana."

Ahaka aka tashi kowa yai d'akinsu .

Umma sam ba haka ta so ba,dan ta san daman auren Baba ba wani d'ad'a Mama yayi da k'asa ba,kawai dai saboda Hudan yasanya take hak'uri take zaman gidan.
Hakanan ranta babu dad'i suka k'arasa d'aki tanata k'ulla ta inda zata b'ullo wa alamarin a ranta.

Mama atunaninta sauk'i zai zowa y'artata sai dai sam  abun ba haka yakasance ba domin kusun kullum sai ansan sharrin da aka had'a mata an saka Ja'afar yai mata shegen duka,sannan sharar tsakar gidan da aka ce shine aikinta kullum,tofa a rana sai Umma ta sakata ta yishi sau uku ko fiye da haka duk kuwa da girman shi,da gangan Jalila za ta jefar da abunda bai taka kara ya karya ba ace sai ta share duka ai daman yayi datti. Sauk'i d'aya zuwa biyu ta samu shine na talla da wankin su,amman ko wankin band'aki ranar na Jalila kwara ruwa kawai takeyi kusan ita ce za'ace take wanke band'akin duk ranar yinta.......
...................
K'arar buga k'auren ne ya dawo da Mama daga duniyar tunanin da ta tafi
K'arar bata gama barin dodon kunnenta ba ta ji an shigo gidan ana wak'a,ko ba a
fad'a mata ba ta san Jalila ce.
Huda Mama ta juya ta kalla tace "kikace bata ce miki ki gyara d'akin yayanku ba ko?"
Kai Hudan ta d'aga mata alamar 'eh'
Mik'ewa Maman tayi ta juyo ta kalli Hudan tace mata
"zauna kar ki fito" daga haka ta yi waje.

wata budurwa ce take K'arasowa tsakar gidan...ba za'a  kirata da bak'a ba sannan kuma ba fara bace fat!!shekarunta ba za su wuce goma sha shidda ba,tanada manyan idanuwa da d'an matsakaicin hanci sannan bakinta ba k'arami bane ba kuma k'atoto bane ba yayi dai dai da yanayin fuskarta
kallo d'aya za ka yi mata ka kirata da kyakkyawa
sannan yanayin shigarta zai tabbatar maka da irin y'an matan nanne marasa kunya...tana tafe tana wak'a had'i da taunar cingum wanda hakan yabawa gefen kumatunta damar lotsawa. Uniform d'in jikinta koren wando ne da farar riga da farin hijabi wanda hakan ke nuni da makarantar da take zuwa ta gwamnati ce...da alama tanada wani muk'amin a makarantar tasu domin d'an kwalin kanta yellow ne ba Fari ba ba kuma kore ba,ta zaro shi daga cikin hijabin nata tayi daurin ture kaga tsiya ta saman hijabin....daga makaranta take  amman ta rambada uban jan jambaki,sannan ga idon nan yasha kwalli ya sake fitowa rambad'au!!!! tubarkalla,y'ar
k'aramar jakarta da ba za ta ci littafi biyu ba na sakale a gefen hannun damanta.

Ido suka had'a da Mama wadda ta gama fitowa daga d'akinta yanzun hakan yasa ta jan wani dogon tsaki had'i da tofar da cingum d'in bakinta kafin  tace"Ni fa na tsani kallo."
Sannan ta yi hanyar shiga d'akin Ummansu.

SO DA BURI Where stories live. Discover now